Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 6

Chapter 6

Gidan Gandu Book 1 Complete Hausa Novel 1,266 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

allah da annabi daya lullube sararin samaniyah,a wannan lokacin babu yanda za'ayi mace kamar kowacce ba irin sameemah ba tafito da irin wannan daren kuma a mashin ita kadai. Tana cikin tafiyane taji alamun wani abu yah rike mata tayar mashin,tsayawa tayi cak da mashin din amma shiru bataga kowa ba,Murmushin gefen baki tayi da tagane mai hakan yake nufi, "Tabbb gaskiya an rainani,yanzu harni wani zai rikemin tayar mashin,toh me akeso nayi ihu ko kuma zefar mashin din na barshi a wajen,kafin gobe wani yah lallab'o yasace koh?" Tura mashin din tayi sai kuma taji tayar ta tafi,wani yunkuri tayi tasake tayar da mashin din kafin tace, "Yadai fi muku,a saukake dan ni ba addu'a zanyiba dama tunda ba iya wa nayi ba,kuma ba ihu zanyiba tunda ba ganin ku nakeba,kunga bata lokacinku kueyi nima ku bata min nawa,saboda so nake naje nayi bacci kuma sai gobe,aga dame zatazo a tareta ana mika wuyah" Har taje bakin kofar gidannasu batabar surutunba kaman wanda wani ne a kusa da ita yana jin me take cewa. Alamun kamar mutum tagani a bakin gidannasu kamar mace tana firah,duba agogon hannunta tayi tana murza ido,karfe biyu ta kusa amma ga wata a kofar gidannasu tana hira, "K'undun ubancan mai yarinyar nan take a waje a wannan Daren,mu manya ma mungama mun dawo gida amma ita tana waje,hmmmmm bari nazo na sameku" (Toh fah kunji wai itace manya,su manya gatan wasa) ❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤ Kar ku manta da #comment #share #like #follow. ____** *GIDAN GANDU* **____ ❤❤By sadi-sakhana❤❤ Wattpad username:SAKHNA03 ❤05❤ A manne suke a jikin katangar sun lab'e itada dashi har baka gane me ake kullawa a wajen,sameemah ceh ta sharo mashin din da gudu,suna kallonta kuwa sukayi saurin bajewa da sauri,saida taje ta kafe mashin din kafin ta dawo wajenna su tana gyara zaman gyalen dayake wuyanta da kuma wandonta wanda rigar ta tattare saboda hawa mashin. Kad'a key din tayi a gabansu kafin ta karewa saurayin kallo, "Kai uban me kakeyi a kofar gidannan,har karfe biyun dare,duk wanda kasamu da ka lallatsa tun karfe goma bai isheka ba saika kai har karfe biyun dare dan zalama,kawuce ka bar wajennan ko saina saka karnuka sun sanja ma kamanni tukunna,da haka kam ai sai kajata ku shiga cikin gidan zuwa kan gadon baba umaru ku karisa tunda har yanzu bai isheka ba(wato ubannata ma bata barshiba kenan)" Cikin sauri da alamar rashin gaskiya yabar kofar gidan yana sosa keyah,harara ta bishi da shi tareda cewa, "Heeeege mai siffar mayu kawai" "Wai miye hakan zakina wani zagin min saurayi kaman wanda yayi miki sata?" Buge mata baki sameemah tayi cikin sauri kana ta dora da cewa, "Har kina da abin cewa keda na kamaki dumu dumu da laifi,a kofar gidanmu saboda ki jawo mana abin magana koh?,nasake jin bakinki ,kin shige gida ko saina yi kwallo dake tukunna" Cikin kunkuni khadija tafara cewa, "Kuma wallahi saina gayawa ummah abinda kikamin,naga kema daga yawon ta zubar din kika dawo kuma daga gani shaye shaye kika iyo tunda ga nan warin wiwi a jikinki.....," "Mekikaceh wai?" "Babu komai ba abinda nace" Tana fadin hakan ta shige gidan da gudu dan ba karamin aikinta bane ta biyota ta kara mata wani dukan. Sassafe masifar a gidan su labiru ta kare dan yanda salame taga rana haka taga dare ita da labiru da kuma mai maganin tofi ,wanda ta daukoshi saboda yayi ma labirun magani,dan batada arzikin kaishi ko chemist ne bare kuma asibiti. Da safe har ya samu ya yi d'an bacci saboda maganin da aka saka masa,saidai fah su labiru babu saka wando zaman daki yakamashi kenan. Saida safenne saleh maye yah shigo dakin uwar tasa duba labirun,salame ce takalleshi da takaici kafin tace, "Yau ganshi bawan mace kawai,tun jiya ake ta maganar abinda akayiwa dan uwanka sai yanzu uwartaka ta biyu ta barka kazo ka dubashi kenan,wanda yarako maza duniya kawai" "Haba Babar labiru yah kike yawa ne,ni ina can bansan ma me ake yi ba,dan sai yanzu na tashi a bacci,shine nace bari nayi hankali nazo na duba shi da jikinnasa,kuma ma dazakice LUBABATU ceh tahanani zuwa,ai kaunace idan ta hanani ma" Kuka salame takawo ta kece tana fyace majina ga ciwon labirun ga kuma takaicin babban dannata wanda yanzu shida wanda suke turu babu wata maraba mai yawa, "Dallah ni tashi kaban waje,yanzunnan ba sai anjima kaje ka dau matakin abinda akayiwa labiru dan bazan yadda ba wallahi" Mikewa yayi da d'an guntun karfinsa yah ciro wata wuka a wandonsa wanda yafita acikin kalarsa saboda daud'a, "Wannan dolene yanzunnan zanje na koma waye fad'a minshi saina fard'e masa wuya a yau ba sai gobeba,mu daman ai ta irin wannan harkar muka kware" "Eh naji ana cewa wani a anguwar yaga yaran sameemah wannan shegiyar yarinyar mai kama da y'ay'an aljanu,wai sun ajiye buhun da aka samu labiru a ciki,ina da itace tayi wannan aika aikar ,dan kowa yasan zata aikata" Suleh ne yajuyo ya kalli uwar tasa tareda cewa, "Iyee inna banji mai kika ceba,ai seemah dai tawa kike nufi?,kai ba mai taba wannan cikar na kyaleshi ,yanda nakejinta a kashin raina ai koke banajinki,babar labiru itah ceh fah surukarki wanda za'a daura auran kwanannan,so kike idan naje na yanketa akawomiki suruka mai tabo" "Inalillahi jama'a kuzo ku tayani bakin ciki,wannan d'a haihuwar banza nayi,yanzu nikake fadawa bawanda kakeso sama da ita a duniya,kuma wai harda ni,bayan irin aika aikar datayiwa dan uwanka?" Turewa sulen tayi cikin bacin rai yah wancakala gefen labiru wanda yake zaune an saka zani an lullube masa gun da ya kone din,sai zazzare ido yake maganar ma wuyah take masa kaman wanda aka kone masa bakin. "Dan banza ji yanda ka wani baje a kasa dan kawai na bugeka,dama uwar me zaka iyah idan kajedin duk kwaya ta gama hudaka tun daga baki har hanji,wannan masifah da mai tai kama" "Inna gaskiya karkije gidanannan kiyi musu wannan masifar taki ,gidan surukanki ne fah " "Innnnnnaaaa ba ita bace tayimin haka ba,karkije kice itace tayimin haka na rokeki innannnnaaaa" "Yawwa inna kinji abinda labirun ma yace koh?,in ma itace cikin soyayya zan lallameta ta fad'amin" Dawowa tayi tana karewa y'ay'an nata kallo,daga wanda yake kwance babu abinda zai iyah an nakasa shi sai wanda shida tab'ab'b'u basuda maraba dashi da su. Cije baki kawai tayi dan takaici ta rasa ma mai zata ce, "Shashashu kawai in ma asiri tayi muku yau zai karye dan ubansa,zuwa gidan gandu kuwa ba fashi inyaso idan naje ku hadiyi zuciya ku mutu,yau koni koh su a garinnan wallahi,dan bazan tab'a yarda ba,in ta kamama kotu zan maka su,muje ayi ta shari'ah daga nan har kotun k'oleee. KO safiyah bata gama waye ba,dan wasu ma ko karyawa basu gama yiba salame ta doko sallama cikin gidan gandun, "Salamu alaikum gafaranku dai,ko bakowa a gidanne" Wani yarone ya fito daga kofar su larai din yace, "Suna nan amma kowa yah kofarsu" "Inane kofar su sameemah wannan shegiyar yarinyar" Tun kafin yayi magana larai ta leko domin ganin wace bakuwar da safiyanannan,dan tun a jiya da daddare suka baro asibitin saboda yanayin sha'ani na kudi, "Kutt dama kece,kin hutasar dani dama ina shirin zuwa gidannanki muyi duk wacce zamuyi dake amma tunda kinzo shikenan sai a fara" "Mekike

Table of Contents

Chapters

55 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});