Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 37

Chapter 37

Gidan Gandu Book 1 Complete Hausa Novel 1,281 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

alhaji bala gwanda da kafadi abinda yake bakinka,toh bari kaji in fadamaka,ba abinda zai shafeni dan ka taba wayannan mutanen,koh zai dameni ma ba sosai,saboda wadda naso a duniyah sama da komai ta tafi ta barni kuma na rayu,dan haka uban kowa ma yah mutu,idan aka jajanta na sati daya kowa ya koma harkarsa. Bar ganin na fadi hakan kuma,allah yasa naji ko mura wani yayi a cikin gidannan ace da hannunka...........hmmmm danka zan dauke mubar kasar dashi muyi rayuwa,sai yagama makancewa akaina na nuna masa video ka sanda kake kokarin yin lalata dani,idan ciwon zuciyah ya kamashi sai na dawo na barshi a can😎" Tun daga jin bayanin irin ta'asar da sameemah zatayiwa dansa yasa yasha jinin jikinsa,saidai bai kai ga komawa hankalinsa ba yaji ta cigaba da cewa, "Kai maganar da kayi ma,ka karawa kanka yanzu bayan na siye zuciyar hajiyah mairo da kuma danka,saina saka yarka taji batada wata kawa mai shirin zama kuma yar uwa a zuciyarta sama dani,saina ga yanda zakayi dani idan sukaji ka illatar dani,kuma kana kokarin keta min haddi a video" Saurin toshe kunnensa yayi tareda cewa, "Yah isa haka mai kikeso ne kika zo gidannan iye?" "Abu kadanne,naji labarin shirin da kakeyi a kaina,Toh ka daina banaso sannan batun bani kujerar vigilantee tana nan babu inda zaraje,dan har na karbi takardar ixini a wajen shugaban yan sanda,dan haka ka shiryah zuwa wani sati,in kuma kak ji baza ka ki ganiba. Ina nan a kan bakana babu inda zanje" Saida yasauke ajiyar zuciya na babu yanda zayyi kafin yace, "Shikenan naji,amma batun d'ana please karkiyi wasa da zuciyarsa kinga baisan komai akanki ba" "Zai sani a hankali karka damu,ai yanada hankali ba mahaukaci bane shi,dan haka in yayi kuskuren hanya zan saita muku shi,sai kuyimin godiyah na cigaba da aikin da iyayene ya kamata su dinga yi,kun sakaltashi da yawa yana bukatar gyara daga irinmu" Zaro glass dinta tayi daga cikin jaka ta toshe fuskarta dashi,har ta isa bakin kofah ta dawo tana cewa, "Ahh alhaji zan tafi amma bakazo kun gaisa da motarka ba,ko ka daina santa ne bansaniba" Ganin dan bakin ciki bai kulata bane yasa ta fita tana Murmushin mugunta. A can Gidan su surayyah kuwa yau sati daya kenan kullum tana cikin aiki,ko an saka ta ko ba a sakata na zata tashi tayi,tunda ta dawo daga hannun sameemah kaman an sanjata haka ta zama,ummanta sai murna takeyi. Yauma zaune hajiyah Sa'aden take bayan sun gama aiki dan d'anta dayake aiki da sojoji yau zai dawo garin,Kwallah mata kira takeyi amma babu itah babu labarinta sam,abu tun safe har wajen yamma,lokacin yayannata har ya iso yah huta,shima daya tambaya cewa akayi bata nan. Shigowa tayi tana sanda hanyah,bata ankaraba saijin maganar mutum tayi a bayanta, Juyawa tayi taga ashe yayantane da zaizo yau, "Daga ina kike haka tun safe,kuma ke ba makaranta kike zuwaba,yansu surayyah kina nan da halinki na yawo da rashin kamun kai koh?" "Iyah Gidan kawata fah naje,ni ba wajen wasu najeba yau din" Jijjiga kai yayi kawai ya wuce shima cikin gidan,itama binsa tayi a baya har ta wuce dakinta,tanajin kowa yana fadar abinda takeyi ita kuwa tura dan kwali tayi tana bubble din chewing gum. Sallamar yah Mahmoud ce ta fito da itah daga cikin dakin tana lekawa ta window, "Miye kike lekoni kizo ki karba abinda kikace na baki" Fitowa tayi kanta a sunkuye kamar wata wanda kwai yah fashe mata a ciki. Mahmoud ne ya mikawa kaninnasa takardar tareda cewa gashi kaima kayi sign tunda kazo, Har zai tambayi ta mecece amma Mahmoud ya hanshi,hakan yasa yah karba shima yayi sign din. Mikawa surayyah takardar yayi kafin yace, "Abinda kika tambayeni sati daya daya wuce ne,wanda nace miki saikinyi hankali shine kika dauki yin aiki na karyah ga ummah,ganin ban baki ba kika tafi wayo inda zan ganki koh?wato koma menene nayi din,shikenan na cika miki sharadinki,gashinan mun amince kiyi aiki da sameemah jar wuyah komai yah faru da amincewarmu" Ba iyah surayyah ba har su ummah su da suke wajen saida sukayi Mamakin abinda yake faruwa,itah kuwa karbar takrdar tayi tareda komawa dakinta tana Murmushin jin dadi,kaman anyi mata albishir da kujerar makkah. Uwar ce takasa hakuri tace, "Amma mahmuda wannan wane irin danyen hujunci kayi,yarinyar da ake nema ta shiryu" Saida yayi murmushi da alamun shi ya hango mai yah faru tukunna yace, "Ummah karki damu babu abinda zai faru sai shiriyah,dan ina mai tabbatar miki kwananna surayyah zata shiryu a wajen seemah,dan nayi bincike nagano cewa duk yaranta yanzu ta hanasu shaye shaye da kuma aikin banza,dalilim da yasa tayi kidnap din surayyah dan na yi mata sign din takrdar neman izinine na zama shugabar yan vigilantee,kuma duk yaranta tace zata sakasu aiki,wanda zasuyimata iyah itah kadai,kaman yamda kuke ganinta ba haka takeba,tana kula da duk wanda yake karkashinta sannan yanda kikasan uwa akan yayanta haka take akan duk wanda ya yadda yah zama acikin kungiyarta,zata iyah bada ranta akansu. Yamzu haka idan wani abu yasamu surayyah,ko bamuyi komaiba zatasan yadda zatayi ta tabbatar ta kubutar da itah,kuma ina mai tabbatar miki zata hanata yawon dare da kuma shaye shayen da take ganin tanayi,kuma dole ta daina dan dole,saboda zataji maganarta fiye da yanda takejin taku. Kudai kuzuba idon ku gani,itah bata san yah sameemah takeba shiyasa take rawar kafar shiga kungiyarta ai,kudai ku zama yan kallo,sannan ku kwantar da hankalinku kaman kun kaitah gidan horo................mai zakuje zai faru tsakanin surayyah da seemah😂😂😂😂😂😂. *Please wanda basayin comment sai dai thank koh liking,ku dunga yin comment mai kyau,musamman Facebook da telegram,naga yan wattpad sun dan fara dagewa. Amma WhatsApp kune akan gama ina ji daku sosai* *+______________________+* *ABIN YABO BOOKSHOP* Kasuwar Rimi Kano Tel:📞 *07038339244* ❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤ Kar ku manta da #comment #share #like #follow. ____** *GIDAN GANDU* **____ ❤❤By sadi-sakhana❤❤ Wattpad username:SAKHNA03 ❤26❤ Kwanaki sunja sameemah ana ta shiryen zama yar damara,duk wani abinda take bukata ta gama hadawa,dan yanzu koh lokacin yan gidannasu bata da shi bare kuma akai ga tsayawa ana saida dan hali. Suma yan gidan nasu bidirin sukeyi an kawo goron tambayar auren Zainab,wannan jarabbabbeb saurayinnata da suke kaiwa dare a wake,sukuwa manyan gidan wato sameerah salma da su sameemah kaman anyimusu asiri babu wacce tayi aure har yanzu,dan gwara ma sameerah ta tabayi ta fito. Su inna ramatu sai kafafa akeyi y'a zatayi aure,su guzuma ana zaune wato su salma. Babu laifi yayi mata kaya masu kyau dadai karfin sa,inda aka saka bikin nan da wata biyu. Duk abinda akeyi sameemah batasan anayi ba dan idan ta fita bata dawowa sai dare,sai shirye shiye sukeyI. Yau ma da sassafe tah tashi kaman abin arziki akayi su wanka da shigar mutunci tafito,babu kowa a tsakar gidan dayake safiyah ce amma rana ta fito,manjo ta samu yana alwala a bakin kofarsa ko kuma nace wanke ido,hada ido sukayi koh eh bata cemasa ba haka shima bai kulata ba,yan miskilancin suna kusa. Gidan su burgu ta fara zuwa tah daukeshi suka tafi ainihin babban office din dayake birini,dauke da takaddar da Mahmoud yayi mata sign da kuma ta Alhaji bala. Saida ta dauki lawyer tah saboda tsaro kafin suka dauki hanyar tafiyar. Zainab ce a zaune tana shafa kurkur a fuskarta tana wakar habaici saboda taga yayan

Table of Contents

Chapters

55 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});