Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 53

Chapter 53

Gidan Gandu Book 1 Complete Hausa Novel 1,260 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

gidan,aikuwa ba itah ta dawo gidanba sai shabiyun dare. Tayi mamaki ganin har sannan su sameerah basuyi bacciba sai tadi sukeyi kaman ba darene yayiba,haushine ya isheta ganin dukkansu babu wamda yayi bacci gashi tana bujatar hutu. Sameerah ce takallesu cikin ji da kai,harda fada da karfi saboda sameemah da batasan mai yah faruba itama da ji me ake cewa, "Ai ko yanzu na cire tuta a tarihin gidan gandu,dan tunda ake auren yan mata a gidannan ba'a taba kawo irin kayama ba,har akwati guda shida kuma masu tsada" Haushine yakama zainab dan duk da uwar su daya amma ba karamin kishine da haushi yah turnuketa ba ganin yamda kayan yar uwar tata ya kere nata. "Toh nidai anga kayana saikuma muka wane kaya gobe tsoho zai kawo ,shin zai taka rawa ko kuma karyar ce kawai" Salma tanajinta amma bata ce komaiba saima murmushi kawai da tayi da alamun zan baku mamaki ni kadai na san abinda na tanada. Duk zancen da suke babu wanda yayi gigin saka sameemah acikin zancen dam tunda kowa yaga yanda sameerah duk da rashin mutuncinta take kaffah kaffah da itah kowa ma fita harakar ta bare yimata abinda ba daidai ba. Washagari da yamma dadai lokacin da aka kawo kayan su sameerah itama salma aka kawo nata,saidai nata yaci uban nasu sameerah,dan akwati shidan itama aka kawo amma kuma hadda wata jaka ta takalma dackuma jakakkuna,banda kuma uban kudin da aka hado dashi a cikin takrda,kofar kawu shehu babu abinda kakeji sai tashin guda da kuma hayaniya. Tunda ganin kayan bakin sameerah ya mutu tah daina cewa nata yafi yawa,wanda hakan yabawa salma damar cewa, "Toh yamzu mai farin jini kayan waye yafi na wani kenan?" "Eh naji idan kayanki yafi yawa ma amma aikin banzane tunda tsoho zaki aura kuma bai kai dai saurayi ba koh?" "Eh naji tsoho zan aurah,amma ki sani babu boka babu malam da kissata na kamashi a hannu,ke kuma fah saida aka hada dana gindin tsamiyah tukunna,saboda baza'a iyah ba. Fada sukayi tayi har saida aka rikesu tukunna suka daina. Kwanaki sun matso na auren su sameerah,dan dama abinda aka sakawa rana toh fah lallai sai yazo,ko ina na gidan shirye shiye akeyi dan an kula auren na manyam mutanene,babu yadda yan uwan su inna hajara basuyi da sameemah ba amma fur tace koh tsefe kai ma bazatayi a watan ba bare ace na Niki tayi,haka dole suka kyaleta,kowa yana shirin bikii ita kuwa tana tafiyah wajen aikinta. Ana sauran kwana uku daurin aure ta dawo daga aiki cikim kayanta na damara,dan ranar koh dan karamin hijab dimma bata saba,daga itah sai hular aikim kawai. A bakin kofar gidan suka hadu da sameer wanda shigowarsa kenan garin,wani aiki aka turoshi yankin toh yah gama shiyasa yah zo idan aka daura aure sai yah wuce,dan dama yah fadawa shugabansa. Kallon kallo sukayi da itah ta dauke kan ta tana shirin wucewa cikin gidan, "Ke sameemah zonan" Tsayawa tayi kaman bazata zoba sai kuma ta taho ta tsaya a gabansa tareda cewa, "Gani" "Kina Ganina amma kika saka kai kika wuce koh,wai yaushe zakiyi hankaline kam iye,su inna Rabi(kanwar inna hajara),sunce sunyimiki magana akan kiyi dan shiga irin ta mata saboda yanayin biki amma kika cemusu bazakiyi ba,sannan baba yace dukkanku kowa tah fitar da miji,amma ke kikace bazakiyi aureba,so kike a jikaki a sha,yanzu fadamin wanne Kika fitar a cikin samarinki" "Ni yah sameer banda saurayi,kuma batun kwalliya indai kainane toh nace banaso dolene,kuma aure ai ba wajibi bane mutum yana iyah cewa bazayyi ba,dan haka karabu dani karka saka daga zuwanka mufara fada da kai akan abinda bai kai ya kawoba" Tsayawa yayi sororo yana kallonta da mamakin abinda ta fada duk da ba yau yafara jin tijararta ta ba. "Ke yamzu sameemah abinda kike kinga yana dacewa,kinsan dai bazan ji dadi ganin ki haka ba koh,kalli aikin da kikeyi fah,babu wanda yasani sai gainki sukayi a ciki,kuma dam tsabar ke kin iyah tarar aradu da ka wai kece mai hukunta kawu shehu dan yayi laifi,kina tunanin sunji dadin abinda kikayi ne duk da basu fadamikiba" "Toh suzo su rama masa mana,ko kuma su turoshi ya rama idan zai iyah koh .......,......." Tun kafin ta gama surutun sameer yayi buge mata baki da hannunsa yana cewa, "Rashin kunyarki shiyake hadaki da mutane,kawunna ki da iyayenki kike cewa suzo su rama?" Saurin rufe bakin tayi tana hade rai itah a dole taji haushi,shikuwa bai kulada yanayin dake ba sai wucewa da yayi yah tafi masallaci jin ana kiran sallah. Sauke hannunta tayi a wajen tana kallom dan jinin dayake hannunta yana konewa kaman ruwa akan karfe mai zafi,wanda dama dalilin dayasa tah rufe wajen kennan. Shigewa tayi cikin gidan kan ta tsaye ko kallon wanda suka tsura mata ido bata yiba. *** *** *** Fatiha allah yabawa SAMEERAH UMAR &UMAR BALA ZAINAB UMAR&YUNUSA SHEHU, SALMA SHEHU& ALH BALA....................SAMEEMAH&.................πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚,kujirani zuwa gobe inshaallah,wannan wajen daga kasan ster duk shortcut ne..πŸ˜€πŸ˜€πŸ˜€πŸ˜€πŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌ. *+______________________+* *ABIN YABO BOOKSHOP* Kasuwar Rimi Kano Tel:πŸ“ž *07038339244* ❀❀SADY-SAKHNACEH❀❀ Kar ku manta da #comment #share #like #follow. ____** *GIDAN GANDU* **____ ❀❀By sadi-sakhana❀❀ Wattpad username:SAKHNA03 ❀37❀ Tun wayewar gari na ranar da za'a daura aure kowa yana ta shiri,su sameerah sai rankwada kai akeyi za'a yi aure. Karfe takwas na rana bakin kofar gida yah fara cika da mutane masu daurin aure. Yau sameemah bata tashi da safeba saboda rashin bacci jiyah da batayiba saboda yanayin surutu na gidan,dan duk matan da'akayi aurensu nagari da ba na gari ba dukkansu sunzo,wanka tayi kafin tah dauko kayan aikinta zata saka,inna rabi ce tah ganta aikuwa ta hada mata kwaredede, "Yanzu diyar nan mai kike shirin yi haka?,za'a yi aure a gidanku amma ke kina kokarin fita wannan shegen aikinnaki,toh ko namijima yau kam bazaije ko ina ba". Hakadai tah rinka yimata fada har saida aka hada da sameer tukunna kafin ta ajiye kayan. Amma kayan anko kam na daurin aure kin sakaawa tayi,bare kuma lalle da kitso. Baba umaru yah sha farar shadda sai sheki takeyi ga kuma hula ya kafa,duk inda yazaga murmushi kawai yakeyi kaman gonar auduga. Motocin su umaruje ne suka fara shigowa kofar gidan da abokannansu,can kuma saiga na alhaji bala ma shida abokansa su alhaji Sama'ila,ummaruje bai tashi mamaki ba sai da yaji abinda mai shela yake fada na daurin auren,baki yasake jin wanda yah auri salma,sai a sannan ya tabbatar ba iya wajen daurin aurensa na ubannasa yazo,shima nasa aurenne yakawoshi ashe......... Fatiha allah yabawa SAMEERAH UMAR &UMAR BALA ZAINAB UMAR&YUNUSA SHEHU, SALMA SHEHU& ALH BALA.................allah basu zaman lafiyha. Har bayan an gama daurin auren mutane har sun fara tafiyah saiga kira daga wajen uban amare biyu wato wato baba umaru kan cewar yana kara gayyaar wani sabon daurin auren na y'ay'an sa. Dawowa aka farayi angwaye harda ma abokan angon da kuma yan uwansu,su alhaji bala sai washe baki sukeyi kaman bai san tashin hankalin dayake jiransa a gidaba. Mamakine yakama mutanen gidan kan cewar wane aure za'a daurah bayan kuma angama,sannan nawa kuma wanda ba'asan dashiba sai yanzu?. Surutun da'ake a cikin gidanne yatsayah cak,yayinda kwanon dayake hannun sameemah yah fadi a kasa ta koma kaman gunki wanda bashida digo rai a cikinsa sakamakon abinda kunnuwanta suka jiyo mata a waje daga

Table of Contents

Chapters

55 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});