Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 31

Chapter 31

Gidan Gandu Book 1 Complete Hausa Novel 1,275 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

gidan yah tafi da kayansa.yah ajiye jakarsa kenan yana kallon dakin saiga manjo yah shigo yana kirga kudi a hannunsa,sai wuriwuri yake da ido da alama baya son wani yah ganshi,sameer ne ya katseshi daga diridirin dayake ta hanyar cewa, "Ah MUSA dama kana nan ,na shigo ban ganka ba tun dazu" "Lah wa nake gani kaman sameer,shege kace kaine dai nake gani,wallahi daka ganni nan wani abun arzikine yasameni,da banso na fadamaka ba amma tunda kaima babban yayantane,toh bari a yi zancen dakai" "Menene yah faru Musa(manjo)?" "Ai in fadamaka abokina ne sule maye yake son seemah jar wuyah kaman ya maida ta cikinsa,toh shine nace yah kawo nairah dubu talatin casss ba ragi ba kari na bashi itah,ni zan shige masa a daura aure,kagansu nan ya bani su cifff,ai ni kam yau kakata ta yanke saka,irin wannan kudi haka inba sata nayi ba har saina kai ga filo da kasa ban sami kamarsu ba" Mamakine yakama sameer jin abinda manjo yake fada, "Amma Musa Kaman naji kace na neman aurenta ne,kuma yanda naga fuskarka kaman so kake ka rike kudin,kuma kana tunanin yanda nima iyah yau na hadu da itah zata bari ka aurarta a haka kuwa?" "Kaga tsaya sameer shiyasa fah dama nake tah buyah kar a ganni,toh gashi kaima kana cikin yan bakin cikin ashe,kudi babu mai hanani cinsu ,batun kuma karta yarda ai dolenta ma ,ina yayanta ta kawomin iyah shege" Daga haka sameer bai sake cewa komai ba sai jijjiga kai kawai da yayi. A dakin su sameemah kuwa,iyah sameerah ce sai zainab a zaune suna ta zubawa saleemah labari,wani ta amsa wani ta gwalesu ko kuma ta tayi shiru,amma da yake basuda zuciyah kkh a jikinsu,suna cikin hirar ne salma ta shigo itama tana wani yatsina fuska dan kana ganinta kasan haushin saleemah takeji ,koh miye dalilinta oho. Sameerah ce ta washe baki bayan saleemah tah yabawa zainaba wata magana ta rashin mutumci, "Amma anty saleemah gaskiya kina burgeni dazan samu dama ai da nabiku porthacourt koba komai zan tayaki ayyuka acan,tunda a nan din na rasa miji kinga acan din watakil saina samu mai dan romo nima,nasan yah sameer din ma bazai hanaba" Saida saleemah tayi mata kallon mamaki kafin tace, "Lallai kam ki bimu,waya ce miki ina bujatar yar aiki,nida nake sanja yan aiki sau kusan goma ma a sati daya,sannan sashe guda aka warewa masu yimin hidima,kinga kuwa bana bukatar yar aiki,sannan dakike cewa yaynki bazai hanaba,dama bashi keda ikon wannan ba nice nan,sai wanda na yadda kafin yah zauna a cikin gida" Dariyah sameerah tayi cikin jin kunyar maganar ta da kuma irin amsar da aka bata,saidai bata da ikon nuna cewa taji haushi. Duk maganar dasuke sameemah tana jinsu dan shigowarta kenan daga waje. Tsayawa tayi akan katifarta ganin jaka da kuma gyalen saleemah akan gadonnata,daukarsu tayi ta wurgawa saleemah akan fuskarta kafin ta zauna a bakin katifar. Binta sukayi da kallo ganin abinda tayiwa saleeman,sameerah ce tayi karfin halin cewa, "Kefah sameemah bakida mutunci,yanzu a gaban bakon ma saikin nuna halinki,toh akan gadonnaki zata kwanta in yaso saiki kwana a shimfidin wata,haka inna ramatu tace" "Saboda ubanta ne yasiyamin katifar kome,ko kuma itah inna ramatun ce ta saya mun iye?" Cikin bacin rai saleemah ta fara yiwa sameemah magana, "Ke na kula tun sanda na shigo garinnan bakida mutunci kina ji da tashen rashin mutunci,toh bari kiji na fadamiki ke baki kai ki ganni ba ina dan dalilin nazo gidanku ba,bare har kiyi misayar miyau dani,ke kinsa inda nake rayuwa kuwa da har kike takama da wata katifa" "Hmm lallai kina bukatar na koya miki hankali,da farko uban me yakawoki gidan namu da har naganki,koh nice na take Naje inda kike,sannan idan harkin isa yanda kikace da sai kice bazaki zo garin ba mana,kodai kina tsoron mijinnaki ne kar ya sakeki?,toh ki bude kunnenki kiji,daga ke har shi a tafin hannuna kuke,ke inkinyi wasa saina shiga har Gidan ubannaki na saka masa wuka a wuyah ,kuma idan kina musu ki bani lokaci da kuma address ki gani" Tsayawa tayi da maganar ta furzar da iska idonta yayi ja,dan daga gani dama a cikin fushi take,wiwi ta,dakko a cikin kwarkwaro ta banka mata wuta ta fara zuga tana fesarwa ta hanci da baki. Karkade tokar tayi kafin ta zawo wata leda da ta shigo da itah,kaza ce a ciki taji jar suyah da dakuma lemo mai sanyi. Saida taci tayi nak kafin tah koma kan katifar ta zauna tana daddanna waya. Duk abinda take suna kallonta amma babu wanda yayi tunanin magana saboda abin yafi karfinsu sosai. Kirane ya shigo wayar tata inda ta daga tana cewa, "Eh yah kawomin information din dazu sannan nagani sosai,kah saurari abinda zan fadamaka,inaso ku satomin kanwarsa a gida ku kaimin itah gidan horo ,amma ban yadda kuyi mata komai ba ,har abinci ku bata kafin naje wajenta,ba lallai naje da wuri ba saboda zanje karbar kudina a wajen alhaji Sama'ila gobe" Gyara shimfidin tayi taja bargo sai bacci,abinda ta iyah kenan. Sameerah ceh ta kalli su Salma lokacin da sameemah taja numfashi bacci na farko tace, "Tabbbb yanzu ku gani,toh ni ko a tarihi ban taba ganin mai irin halin Sameemah wlh ba karamin tsoro take baniba" Basuja hirar da yawa ba suma suka kwanta dan kar tsautsayi yasa ta jisu su shiga uku. Fitowa tayi daga dakinnasu cikin shiri zata je wani waje,babu kowa a kofar tasu saboda yanayin lokaci daya tafi sosai. Baba umarune ya tsayar da itah har takai bakin kofa ,juyowa tayi kafin kuma yam hankalin suka ce ta dawo da baya, "Ina kwana "shine kawai abinda tace daga nan kuma tayi shiru, "Lafiyah kalau saidai ba dan gaisuwa na tsayar dake ba,wani waje zakuje dake da yayanki da kuma iyalansa,saiki shiryah tunda ba yau zaku dawoba" "Wani waje kuma ina kenan" "Dangin mahaifiyar ki ko shima bazaki jeba ne" "Ahah zanje amma ba yanzu ba,akwai abinda nake idan na gama saina je daga baya ai nasan garin sosai,kuma nafison tafiyah ni kadai" "Hungo naki(yafada yana bata yatsu biyar),dasu zaku tafi kuma a mota daya saura kuma naji kince bazaki jeba kumadu,kije maza ki dauko kayanki koh guda biyu kizo ku tafi" Daga ido tayi tana kallon sameer wanda yake ta zabga mata harara shikadai,itama ramawa tayi tareda mutstsika baki kafin kuma tah cije lebe alamar zasu kwala. Komawa dakin tayi da dauko wani dan karamin trolly,na irin tafiyah kwana biyu,ficewa tayi zuwa wajen ko sake kallon baba umaru batayi ba,tun a hanya take hango saleemah a gaban motar sameer din,itama itah take kallo ido cikin ido. *+______________________+* *ABIN YABO BOOKSHOP* Kasuwar Rimi Kano Tel:📞 *07038339244* ❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤ Kar ku manta da #comment #share #like #follow. ____** *GIDAN GANDU* **____ ❤❤By sadi-sakhana❤❤ Wattpad username:SAKHNA03 ❤22❤ Budewa motar tayi ta shiga tareda maida kofar da karfi kaman zata cireta,itah dai saleemah bata kuta ba,dan abinda ya isheta yah isheta na zuwa kauyen da za'ayi na su inna hajara,tana ganin an kawota lungunan cikin zariyah a she ga kauye can za'aje. Shigowa yayi cikin motar suka fara tafiyha a cikin motah,sunyi tafiyah mai nisa amma babu wanda yace wani abu,saleemah ce ma ta kalli sameer da alamun shagwaba tace, "Honey fushi kake da ni?" "Haka nace miki,abinda kike yi ne

Table of Contents

Chapters

55 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});