Chapter 30
Chapter 30
shashanci ku kiyaye,ku kuma (tafada tana nuna yaran da suka ganta lokacin da sukayi fada da yaron bubu jini da kuma dukkan yarannasa),tunda kun ji labarina toh kun dawo yan kungiyar nan,daku za'a fara aikin vigilantee,musamman matan kune masu kamomin wani idan yah shiga Gidan su,daga wani satin za'a fara koyar da horo wanda zan dauki nauyi a gidan horona dayake cikin jeji" Dukkansu amsawa sukayi da cewar, "Mun ji shugaba kuma mun mika wuyah" "Yadai fi muku,sauran naji wani yayi abinda ban saka shiba kuma" "Babu wanda zayyi ma ranki ya dade" Motarta ta nufa tana kakkada key,saida ta zauna na dan wani lokaci kafin ta ja motar tabar wajen,sai kurar tashinta me kawai yah saura. Wata bakar motace tah faka a gaban gidan gandun,baka mai sheki amma ba wacce sameemah ta iyo kwacenta a wajen alhaji bala bace. Saleemah ceh takalli major sameer ganin ya faka a wani waje kaman gwalalo,shima kallonta yayi amma baice komai ba, "Honey naga ka tsaya koh motar ce ta baci kai?" "Ahah ba motace tah baci ba anzo gidanne" "Gida kuma honey wannan fah kaman ba gida bane,baka ganin yanda yaje ne" "Saleemah ya fah isheki haka,tun kafin mu taho kike wani bata rai,miye nufinki,bazaki zo gidanmu ba kenan,saidai ni nayi ta zuwa gidanku,toh bazai yiyu ba wannan shine gidan mu kuma sai munyi sati guda kafin mu tafi,dan haka kima shirya zaman cikin gidannan" Hawayene yafara zubowa a cikin idonta tana wani cuna baki, "Nikam bazan iyah zama a cikin gidannan ba,mai laifin ka kaimu hotel sai mu dunga zuwa,gaskiya d'ana zayyi gudawa a cikin gidannan" "Eh Kat d'anki yayi gudawa ko?,toh ni na mutu mana kafin ki ganni,kuma sai yanzu kike son dan" "Eh KO ma menene ni bazan zauna ba" Ganin abinnata bazai kareba ne yasa yah fito daga cikin motar yah barta itah kadai tana ta mita da shagwabarta,tsayawa tayi da mitar da take ganin wata mota mai irin tasu bak'a ta shawo hanyar layin da suke,saleemah ceh ta fito daga cikin motar tareda tsayawa a kusa da sameer din,tambayar sa take saboda tsabar gulma tana cinta, "Honey dama akwai irin wannan motar acikin garinnan ne,tunda muka shigo ko karamar mota ban ganiba amma ji wannan motar kuma a hanyar gidanannan?" "Kin isheni da surutu ki tsaya ki gani mana" A bangaren sameemah kuwa tunda ta shawo hanyar gidannasu tah kulada motar kofar gidan ,kuma ta gane sarai suwaye a cikin motar,tana zuwa fakawa tayi a gefensu tareda fitowa daga cikin motar tana feduwa. Dukkansu kallon ta sukayi da Mamaki harda saleemah wanda bata santa ba,ina kuma ga uwar gayyah yayannata. Tahowa tayi tah gabansu zata wuce sameer din yayi saurin shan gabanta tareda cewa, "Ke ubanwa ya baki wannan motar haka" "Uban wani ne yabani itah mana" "Akan wane dalilin,wane irin aiki kike masa haka" "Akan dalilin na bashi budurcina ne,batun aikin danake masa kuma,irin aikin da matarka take maka duk dare shi nake yi masa nima,har yah bani itah" ............,.😲😲😲😲 *+______________________+* *ABIN YABO BOOKSHOP* Kasuwar Rimi Kano Tel:📞 *07038339244* ❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤ Kar ku manta da #comment #share #like #follow. ____** *GIDAN GANDU* **____ ❤❤By sadi-sakhana❤❤ Wattpad username:SAKHNA03 ❤21❤ Baki yasake yana bin sameemah da kallon mamaki,wanda ta shige gidan tana feduwa da karfi. Sun fi minti goma a,tsaye kafin yayi karfin halin jan hannun saleema suka shiga gidan. Tun daga bakin kofa ake tah muranar isowarsu,yayinda saleemah take tah makewa a jikin sameer kaman taga kashi,lura da hakan da yayi ne yasa shi tureta daga jikinsa yana aika mata kallon tah shiga hankalinta,itama wayancewa tayi tana aika musu murmushin. Cikin kankanin lokaci aka shimfida musu tabarma a tsakar gidan suna gaisawa,shima baba umaru yana gida saboda yasan da zuwan dannasa bare kuma su baba shehu kodan gulmama ai,kowa shiru yayi da zancen sa ganin shirga shirgan karnuka sun shigo gidan suna d'aga jela,saleemah ceh tayi tsalle ta haye kan sameer tana kikkifta ido,dan dama kaman akan kaya haka take ji,wucewa sukayi tareda nufar dakin da sameemah take ciki,sameer ne yayi karfin halin cewa, "Karnukan fah,kuma a cikin gida haka" "Uhmmmm" Shinen abinda kowa yace tareda kawar da zancen.Sameemah ceh tah fito daga dakinsu daga itah sai wata vest da dogon wando,ledar nama ce a hannun ta karnukan sai binta sukeyi har suka je wajen kejinsu. Ganin koh kallon inda suke sameemah batayi bane bare kuma gaisuwa tah hada su,yasa Baaba umaru cewa, "Keh sameemah baki ga dan uwanki da matarsa bane,kika tsaya baki zo kun gaisaba" "Mun gaisa mana dashi a waje,wace gaisuwar kuma yakeson kara ji daga wannan" Sameer ne ya mike tsaye cikin zuciyah irinta sojoji yace, "Ke anya kuwa hankalinki daya dazu kin yimin rashin kunyah yanzu kuma kina yiwa harda yan gida,ana miki magana hankalinki yana kan karnuka,wai tukunnama menene na ajiye karnuka a cikin gida,in kinyi wasa yanzu zansa a fita dasu kuma bazaki kara ganinsu ba" Inna larai ce tah tashi cikin jin dadi tace, "Yawwa gwanda da kazo ko zakayi maganin ta,wlh ta addabemu matuka" Kowa fara fadan albarkacin bakinsa yayi. Duk abinda suke sameemah bata koh motsaba ,saida kowa yagama fadan abinda yake bakinsa kafin ta tafa hannunta raffffff,tsitt kakeji kaman anyi ruwa an dauke,takawa take a hankali har ta kai gaban sameer numfashin su yana bugar na juna, "Wace rashin kinyar na maka,fadamin itah naji,amsar dana baka dazu bayan ka tambayenine rashin kunya ko kuma dan naki zuwa na gaisheku kaida matarka,wanne ne daga ciki?,sannan kuma da kake cewa zaka batar da karnukana bazan sake ganinsu ba koh?,dan allah bismillah kada ka fasa,kaima kuwa kai kadai zaka koma inda ka fito batareda danka da matarka ba,dan nima saina batar dasu" Kowa zaro ido yayi tareda shan jinin jikinsa jin abinda sameemah tace,musamman ma saleemah da taji ana cewa za'a batar da itah,cikin kankanin lokaci tah tsure. Kallon kallo aka fara tsakanin sameemah da sameer,shi yana mata kallon Mamakin yanda ta zama ita kuma tana masa kallon zaka san koni wacece. Katse kallon da suke ita da yannata tayi sanadiyyar karar da wayar ta tayi a cikin aljihun wandonta,saida ta danyi yar karamar tsuka kafin tah daga kiran tana hade girar kasa da sama, "Kai miyene wai kuka dameni,naga yanzunnan na dawo gida ko hutawa banyiba" Dayake wayar tana handsfree kanajin abinda ake fada a daya bangaren, "Ogah Ranki ya Dade wallahi duk bayanin da mukayi masa akan kece kika turomu yaki bada hadin kai,yanzu haka muna wajensa ma" "Okay inason information gameda komai nasa nan da dare,sannan ina sabin yan kungiya suke,dafatan kun fara nuna musu aiki kaman yanda nace" "Eh shugaba,matan sun bi su uban dawa wajen campaign din alhaji Sama'ila,sauran kuma har yanzu jikinsu a mace yake tunda sukaga abinda kikayiwa ogahnsu wanda yake asibiti" "Karka dam u dasu zasu ware ,ka kawo min information kafin dare ina jiranka" "Shikenan ogah allah yaja da ranki" Sauke wayar tayi tareda yah mutsa fuska ganin yanayin reaction din fuskar su ya nuna duk sunji abinda aka fada a cikin wayar. Barin wajen tayi ,ko a jikinta maganar da tayi. Su sameerah ne suka dauki kayan saleemah wanda suke kira da anty saleemah zuwa dakinsu,binsu takeyi a baya kaman anyi mata dole,su kuwa sai shige mata sukeyi ganin yanda tasha kaya na girma da alfarma. Shikuwa sameer dakin mazan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55