Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 44

Chapter 44

Gidan Gandu Book 1 Complete Hausa Novel 1,265 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ranta zai fice,sameerah mai karfin gwiwar tambayar ta menene,amma sauran mutanen dakin koh kallo bata ishe su ba, "Ba........ba shine ba wai an zanye yin auren sai ya dawo daga service din aikin dan sanda ,yace wai sai bashida kudi toh sunansa ya fito a cikin masu tafiyah service,kuma dama wai bai gama giniba yana so dama a daga auren" "Koh so yake yah gudu dama ba" Salma ta fada tana dariyar mugunta,wani ashar zainab ta nana mata kafin suka rukume da fada kaman karnuka. Itah kuwa sameerah da dakin mahaifiyar su ta nufah da sauri domin jin tushen bayanin. Da wuri ta tashi yau babu baccin safe,wanka tayi ta ruwan sanyi amma ba ta sanyin take na burinta kawai taje inda yake ranta. Kayan uniform ta dauko na vigilant ta saka,dan karamin hijab din kayan ta saka tareda dora hular a kansa,hoda ta shafa kawai sai mai kafin ta feshe jikinta da turare,glass ta saka baki wanda yayi match da wandon jikin ta ga kuma kalar fatarta ta fito a cikin coffee rigar tasu,jakar ta dauka da kuma key din motarta kafin tah fita daga dakin. Duk abinda takeyi su salma suna kallonta,dukkansu mamaki suka dungayi da ganinta cikin kayan,dan babu wanda tah fadawa zata fara aikin. A tsakar gida kuwa bata hadu da kowa ba har ta isa wajen motarta ta shiga. Su surayyah kuwa an fi kowa d'oki dan rana ma acan ta fito ta ganta,dukkan su kame wa sukayi tareda sarawa lokacin da sameemah tah iso wajen,dan labarin sauyin shugaba dama yazo musu,kuma sunyi farincikin da hakan dan dama babu wanda yake somsa,shiyasa da tace wanda yake bukata zai iyah tafiya babu wanda yah tafi,suna fatan dai kar ayi gudun gara a tadda zago. Fitowa tayi a motar tana gyara zaman glass dinta fuskarta babu alamar fara'a bakinnan a d'ane. Hanyar office dinta ta nufa koh kallonsu batayi ba,wata bazawara ce wanda anan suka zo suka samesu tah kalli surayyah tareda sauke murya kasa kasa tace, "Hmm kika ce shugabarku tanada mutunci?,amma yanzu ji yanda tazo ta wucemu koj kallonmu bata yiba bayan wannan shine zuwanta na farko" "Ke me kike ci na baka na zuba yanzu fah aka fara wasan,ki tsaya ki gani mana" Itah kuwa sameemah batayiwa kanta a ko ina waijiba sai kan kujerar ta office din,saida ta zuyah ta sake juyahwa kafin ta saki wani dan iskan Murmushi. Wasu takardu aka kawomata da alama sauran aikine da tsohon shugaban bai gamaba. Zare glass din idonta tayi ta ajiye a gefe kafin ta daga takarda tah farko,case ne akan yanda karuwai da yan daudu sukayi yawa a gidan kara,yan hisba sun kawo case din akan za'a hadu dasu ayi amma babu wanda yayi magana. Sai kuma na gaba yanda sane yayi yawa a kasuwa sannan idan an kama su yan sanda basayin komai akai,da kuma wani saurayi dayah kama wani tsoho a unguwarsu yayi masa duka,dan kawai yakaishi kara yah sace masa akuyah. Dariyah sameemah tah fashe da itah saida mai kawo takardun yah ja da baya,daga ganin dariyahr kasan ta mugunta ce zallah, "Irin wannan kujerar dama nake nema,inda zan baje tawa baiwar,kai inaso ka kiramin duk wani maikaci yasameni a waje yanzunnan" "Angama Ranki yah dade" Da gudu yah fitah kaman zai kifah. Bayan mintu kadan yadawo tareda shida mata kowa ya hallara. Fitowa tayi ta tsayah a gabansu,kowa yah kame kaman an daskarar shi,yaranta ta kallah acikin tsofin maikatan dukkan su sun sha kaya kaman ba suba,koba komai taji dadi da ta sama musu sana'a. "Inaso kijini da kyau,wanda suke wajennan dayawa dama yarana ne nasan halinsu,su kuma sauran na duba bayanansu wanda ina fata muyi aikin daya kawomu banason shashanci. Abinda yasa na kiraku shine,akwai casr kuda uku wanda sune suka fi girma kuma ina so yau dinnan basai gobe ba a gama dasu" File din ta Bude tareda kiran suna,saida ta tabbatar ta raba wani rukuni gida uku tukunnan tace sauran su koma aiki. Su burgu tah nuna da wssu suma biyar tace su je kasuwa,duk wanda yayi sata su kamo mata shi kafin ma yan sanda du sani,sannan wsu ma guda uku tareda surayyah da kuka shamsiyyah(bazawar nan),su kamo mata yaton da yayi duka ga tsohon anguwarsu. Sai kuma wanda tasaka akan aje gidan kara kamen karuwai,amma kar a tabasu har sai taje tukunnan,kawai suyi kaman ba wajen suka jeba su yi shiru har zuwa yamma. Nuna lubna tayi da kubra kafin tace su biyota zuwa wani waje. Direct office din hisba ta nufah,tana isa ta nemi iso zuwa office din shugaban,shiga sukayi ta zauna su kuma su kubra suna tsaye a bayanta sun kame,dan dama matan sun ji karfi da kuka kira,bare suka samu training daga wajen sameemah na salon fada daban daban,shiyasa itama take ji dasu ta wannan fannin. Dagowa yayi daga rubutun dayakeyi yana kallonsu,ganin sun shigo amma babu wanda tayi magana, "Eh ina jinku mai ke tafe daku" "Da baka tambayi mai ke tafe damu ba shiyasa nayi shiru domin baka daMa ka gama,amma yunda yanzu ka taambaya sunana sameemah sabuwar shugabar kungiyar vigilantee. Gameda abinda yakawomu kuma ba kkmai ba ne illah akan zancen case daka rubutah na gidan karuwai ne yakawoni saboda na ganshi a office" "Eh anyi haka amma wannan case din yace bazasu damar yiba,ku kuma muma muna wani aikin har yanzu gashi bamuda wasu ma'aikata masu yawa,idan muka ce zamuje irin wannan aikin mu kadai,mukan samun barazana,toh shi kuma yace mana wai ogansa ya hanashi irin wannan aikin" Numfasawa sameemah tayi dan tasan wa yake nufi da ogan, "Shikenan karma damu dama akan case din nazo,Inaso kasaka hannu akan takardar Ta yajejeniyar ni zan ajiyesu a wajena ba ma kune zakuyi ba, nikuma a yau basai gobeba zan kamasu" Hankalinsa ne kaman bai dan kwanta da zancneta ba dan da alama bai wani yarda ba,ganin hakanne yasa tace, "Idan wata matsala ta faru ka dora laifin a kaina sannnan karka sake bani wani hadin kai anan gaba" Karbar takardar yayi yai mata sign din kaman yanda ta bukata kafin yabata. Tana fitowa direct gidan karuwan suka shige,acan nesa da wajen suka hadu da sauran yarannata inda itama ta fito daga motar ta suka shige. Gidane mai fili sai dakuna dayawa,kaman dai gidan haya,da wasu yam daudu suka fara cin karo a tsakar gidan suna wasan karta,aikuwa suna ganinsu suka rufah da gudu kowanne yana zefar da zanin daya rufe kirjinsa dashi. Dakuna dakuna suke bi suna fito da mutanen ciki,mutane kala wasu da attach wasu saikace fatalwa dan fari. Duk tarasu akayi a tsakar gidan masu ihu suna yi masu roko sunayi. Wata kujera sameemah taja ta zauna tanan kare musu kallo,wai yau itah ake roko kartayi rashin mutunci,gashi kuma gangar rashin mutuncin nata ta riga ta kada sauti. Wani dan daudu ne yakalle ta tareda cewa, "Haba ke kuwa sister ai andaina zamanin kame tun wancan karnin,ki fadi kawai nawa kike so a baki a wuce wajen" "Ahah mai kake ci na baka na zuba dama ai za'ayi ciniki,har saikayi cinnki ka kaji,yanzudai bari muje a gyaraka ka koma ainihin siffarka tukunna koh?" Shiru yayi jikinsa yafara tsima jin abinda tace,wata ce a cikinsu tace, "In gaskiya ne naga ba'a je chamber su yar sheelah ba idan

Table of Contents

Chapters

55 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});