Chapter 38
Chapter 38
kawu shehu mata a wajen da kuma sauran yan matan gidan, "Lokacinki ne yayi amarya yar amana sai kize ki zauna da miji aure ibada ne............" "Hee amaryah manya,amaryah da yin kurkur,kir ayi mai na kanti mana,kuma a wane shegen saurayin kowa yasan halinsa da bin yaran mutane" Wata ce itama ta sake cafkewa bayan salma ta yi shiru, "Ke ma kya fada,dan dai an rasa wani ne sai shi,in ba hakaba mai za'ayi da Uzairu a rayuwa" "Eh haushin rashine makaho yace ido da wari,inma mai danne iyayene wata ta fito da nata mana,aurene nima zanyi na bar gidan gandu nafara girka nawa abinci wanda nakeso na barku da tuwon masara miyar lami" "Dan ma tuwon masara kikaci kika girma ,kuma shi uwarki zata shigaba da ci har kasa ta binne idonta" Salmace cikin yatsina fuska tace, "Ke zainab ya isheki haka kuma,bamuson raini,a wane shegen saurayinaki naga saida nace bana sonsa kafin yah dawo wajenki,kuma shi banzan bazarane a cikin masoyana wallahi" "Eh naji banzan bazarane shiyasa naga baki auri wannan tula tulan alhazan nakiba ai kika makale da soyayyar yah sameer har kike zagin matarsa,kuma duk jarabarki ma zaki barshi ki auri daya daga cikin tsofinnaki,dan anty saleemah ba sa'arki bace ehhe" Cikin rashin daurewa da zancen salma tah kaiwa zainab wani uban naushi a bakinta,abinka da brush bai ishi bakinba sai jini yace yah samu wajen fita shikuwa. Kururuwa ta hada itama ta kamata suka fara fada sai ga sameerah ta shigo da leda a hannunta da alama daga wani waje take,wajen su tayi tana rabasu tareda cewa, "Ku hakan menene mai kuma yah faru kuke wannan kokuwar,ke salma bakiga aure zatayiba kike dukan ta a fuska?" "Ke sameerah kema banason iskanci,auren yaci kundun ubansa,haukane auren dan zatayi ta dunga yadawa mutane magana,toh gobema ta kara saina zubar mata dukkan hakoranta,saidai inna ramatu ta akaita a saka mata na roba" Tana gama fadan hakan ta bar dakin tana huci,sukuwa binta sukayi kawai da kallo. Ita kuwa sameemah tun safe suke bakin kofar shugaban amma basu samu shiga ba schedule dinsu bai zoba har dare yafarayi,tun suna saka rai har suka hakura suka dawo,gashi sai wani satin su koma kuma. In ran sameemah yayi dubu toh yah baci a wajen dan ko magana batayi sosai,haka ga gajiyah ga komai tah tuko motar suka taho. Saida ta fara sauke barr.Kamal kafin ta sauke burgu shima a gidansu,yana mata godiyah da huta gajiyah ko kulashi batayi ba saima kara hade fuska da tayi. Tun da ta shigo layin gidansu takejin muryar yan gidannasu gashi darene dan 9:30pm ta kusa,takaicine ya isheta tasan ba lallai ta shige Kalau na. Ai kuwa hakance tah faru dan inna karimane da inna larai suke fada akan marar tuwo guda biyu. Babu wanda yah kulada da itah a wajen dan manya da yara an tsatstsaya kowa wasuma hadda torchlight a hannunsu saboda su gani da kayau dayake an dauke nepa. Baba umarune ya dawo ana tsaramasa yanda akayi,tun kafin su gama tsarawa sameemah tah fisge kwanon tuwon ta wullawa su bingo wanda suke biye da itah sunga ta shigo. Kowa mamaki yayi tareda yin shiru amma banda inna larai dan masifah ta farayi kaman makogaranta zai fashe, "Kinsan allah inna larai ko kiyiwa mutane shiru da darennan ko kuma na tura karennan yah ciromin mamanki na hagun idan kina bacci,kinsan sarai zan aikata yanda kofar dakinki kuwa ta baci babu sakata,dan haka saiki zaba yanzunan" Kowa inna larai yake kallo da jin wanne zata zaba maganar sameemah,aikuwa cikin sauri tayi kofarsu tsitt kakeji kaman ruwa ya cinyeta. Kowama dayaga hakan kofarsu ya nufa yana dariyah da tsoron inna larai,ga tsokana ga fada dakuma rashin gaskiya, aka bar filin wajen,sai gobe kuma.😂 Yanzu dakinnasu iyahsu kadaine babu zainab saboda tah koma dakin iyah mai kalwa(kakarsu da ta rasu )ana mata al'ada na aure,kaman su tsimi na tsugunne da sauransu,hakanma sai yafi musu,domin indai zasu zauna da itah da salma toh fadane zai biyo baya tsakninsu da itah,ita kuwa dama sameemah babu wanda take shiga shirginsa saidai idan ka shiga nata shirgin ku kwashi yan kallo. Misalin karfe 12;00pm rana tayi ga kuma zafin rana saboda yanayin lokaci na rani,surayyah ce ta shigo gida da sauri sai hada gumi takeyi,babu ko sallama bare ta kula mutanen gidan ta dau buta tayi bandaki da gudu,saida ta fito ta sha ruwa kafin ta zube a tabarma a tsakar gidan nasu wanda take karkashin bishiyah. Saida ta gama hakin da fifita kafin ummansu ta tambayeta, "Mai Sunan uwata ya na ganki haka kaman wanda aka zefoki daga sama" "Hmm ai bari kawai ummah,muna kan tsallaka siradi ne,da yawanmu shugaba ta saka a training kuma duk wanda bai fito da matakin nasara ba sallamarsa zatayi,gashi bata afuwa,idan tana yimana training dinannan kaman fah soja haka takeyi,gwanda ma ogah burgu yana mana da sauki. "Ahh kikce aiki kukeyi babu kama hannun yaro" "Hmm ni ummah kuwa anya kungiyar yan daba ce kuwa?" "Me kika gani?" "Naga an Hana shaye shaye,an hana yawon dare sannan ba'a yin shagali,kullum ana cikin training da kuma fita aiki,ni gaskiya gani nakeyi kaman ba kungiyar dana ke jin labari bace" Dariyah ce ta kama ummah amma haka ta kunsheta kar surayyah ta gane,kwata kwata satinta daya tana zuwa wajen sameemah amma har ta fara sanjawa,babu shegen wayon club,babu shigar rashin mutumnci sannan babu wannan baccin safen har zuwa azahar. "Uhm ummah bani abinci naci,nayi wanka dan in anjima shugaba tana neman mu akwai abinda za'ayi,naji tace wai zata sakamu a wajen koyon computer wasu kuma a turasu wajen training na police da yan sojoji,nikam kungiyar tamu har ta fara bani tsoro,yanzu ko samarina nagani tsoton kulani sukeyi wai tunda na shiga kungiyar seemah" Narai narai tayi da ido kaman zatayi kuka,amma tunanin abinda zai faru idan bata koma ba yasa ta mike tana wani lankwashewa kaman wanda ta fito daga labor room,itadai ummah bata kara cewa komaiba sai dariyah da takeyi ciki ciki tareda fadin madallah. Aikuwa la'asar nayi tun kafin tagama cin abinci saiga kiran burgu,da sauri ta tura sauran lomar da cokali ta mike zuwatt,badan tsoron burgu ba saidan tsoron wanda tasa burgu ya kirasu. Da gudu gudu tayiwa ummah bye bey ta fita,sai a wajema ta karisa saka gyalen a wuyanta. Tun da sameemah ta dawo gida sanda su inna larai suke fada da daddarenan take ta bacci har bayan azahar,su kansu yan gidan su zata ta mike ta can zuwa makwancinta na gaskiya,wanda da hakan yah faru da sunfi kowa farin ciki,saidai kash!!! Daidai wani lokaci ta bude idonta tareda yin wata mika irin ta wanda babu abinda yah dameshi. Fitowa tayi tsakar gidan tana rarraba idon neman yaro dan ya debo mata ruwa,ita wannan rashin ruwa da suke fama dashi yana ci mata tuwo a kwaryah ba kadan ba. Dan Gidan manjo ne yah yazo wucewa zai fita waje,sai sameemah ta kirashi,da sauri yah taho wanda koh uwarsa ce albarka,saboda yasan bata wasa dasu ko kadan. Bayan ya tafi debo ruwanne tah koma dakin jin wayarta tana ta ringing,gashi dama bata saka volume kadan,kuma da saninta takeyin hakan. Ganin number ummaruje saida tayi jimm kafin ta dauka, "Allah ya taimaki gimbiya sameemah,yah gida da kuma jin dadi" "Lafiyah kalau yah hajiya"
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55