Chapter 24
Chapter 24
nufi nayi ba,kawai dai naji ta ne,ni dai ina rayuwa kawai naci na koshi kuma nayi abinda nakeso idan masu kuladamu basu ganiba,dan yanzu har wajen bangaren maza nake jan shaheedah muje hira dayake itama jar wuyah ce tasan takan rayuwar air,saimunsha hirarmu da su munajin mai sukayi aka kawosu suna fadamana,harda labarin yanda area su take. Haka kawai idan ba zancen rashin arzikba bana jin raina yanaso don duk lokacin da'aka zo karatu tun daga na turanci har na larabci yi kawai nake badan raina yanaso ba,duk da ina kokari sosai na iyah kowanne amma raina bayaso,kawai dannasan horon dazai biyo baya bazaimin kyau bane,gashi tsoron malamin addinin nan nake kaman raina zai fita,dan koda da kuskure ya zangamin carbinsa ji nakeyi kaman yana kona jinin jikina,shiyasa ni nake fara bada hadda idan yazo karba,sai yaga kaman nafi kowa san karatun ,nan kuwa ba haka abin yake ba sam. Wata ranar juma'ane aka daukemu zuwa makabarta,munsha abaya bakake dukkanmu matan,su kuma mazan sunsha fararen kayah,bayan mun shiga motane kuma naga wasu matan suma sunsha bakaken kaya amma su da nikaf a idonsu suna shiga wata motar,tabo shaheedah nayi wanda take gefena a zaune,dagowa tayi tareda tambayar menene,nuna mata nayi tunda har sannan ban iya larabcin sosai ba sai kalmomi kadan kadan,ganin ta kallesu ne nace mata suwaye? Murmushi tayi kafin tace, "Masu laifine amma sun haura shekara goma sha takwas shiyasa aka kaisu wancan kurkukun,muma da mun yi shekara sha takwas da can za'a kaimu,kuma su suna aiki sosai ga kuma horo ga wanda yah aikata laifi mai yawa" Jijjiga kaina kawai nayi har muka ja muka tafi idona bai dauke daga kan motar tasu ba. Mun dade muna tafiyah kafin muka isa zuwa cikin makabartar,ba mu muka dawoba har sai wajen magriba ,naji dadin fitar sosai koba komai nayi kallon waje dayawa. Bayan munyi sallar isha ne nazo na kwanta ba bacci nayi ba tunani kawai nakeyi na gida ,tareda yiwa kaina tambayoyi yanzu suna can sun manta Dani babu wanda zayyi tunanin an saceni kowa zai dauka na tafi babban birni neman kudi kaman yanda na fadamusu,hawsyene ya fito a idona dansn tuna da ummah na,lallai mutuwa mai yanke kauna ce,nasan da tana.nan da yanzu ina gefenta a kwance tana yimin tatsuniya,saidai wani bangare na zuciyah ta yana cewa,gwanda da bata nan,domin da tana nan da hankalinta sai ya tashi matuka da haka na gama tunanina har bacci ya dauke ni. Kwanci tashi shakuwa ta shiga tsakanin mu ba iyah yan dakinmu ba hatta bangaren maza babu wanda bai sanniba musamman ma shaheedah wadda kullum tare muke da itah,dan ni da itah har wiwi mike sha wanda mazan suke bamu suna siyah a wajen amintattun mutanensu masu gadi,saidai duk abinda mukeyi babu wanda yasani hatta yan dakinmu ma basu saniba,gashi babu inda na fita naje amma zallar rashin mutunci koh shaheedah bazata gayaminba duk da ita ta dade a cikin yan iska amma saida na nuna mata iyakarta wajen rashin tsoro da kuma aikata abinda nayi niyyah,saboda ni bayan rashin mutuncin danakeyi har jinake ana,zugani a cikin kaina idan kuma nakiyi sainaji kaman ana son azabtar dani,gashi duk sanda mukayi fada da wani sainaji babu abinda nakeso sai shan jininsa,tun kafin aje ko ina na kula cewa wannan abinda zuciyata takeso yana da matukar hatsari,shiyasa idan hakan ta faru saina shiga bandaki na rufe,saina huce kafin na dawo,yanzu kuma in ba wiwi na zukaba banajin dadai kwata kwata. Muna cikin tsaka da shuka tsiyamu nida shaheedah kwatsam saiga iyayenta sunzo tafiyah da itah,a da lokacin baya kafin zuwana babu abinda takeso sai tabar wajen amma yanzu bata kaunar abinda zai rabata da wajen,dan yanzu ta gane tsiyar danake jan ragama anayi a cikin wajen koh inda take ba'a irinta. Tun safe take kuka nake rarrashinta akan wata rana zamu hadu,sai can wajen rana kafin motar kawunta yazo,wata takarda ta mikomin da number a jiki,kafin tace. "Ni zan tafi amma ki tabbatar kin kirani duk lokacin da kika dawo,zanyi kokarin na gyara number kuma ina jiran kiranki duk ranar da kika fito,bazan taba mantawa dakeba,yimata alama nayi da karta damu,dan ni a yamzu tunda na rabu da mahaifiyata to kowa ma zan iyah rabuwa dashi ko waye shi kuwa. Bayan naga kulewar motarsu ne na kade rigata tareda shigewa dakinmu ko a jikina ,wasan ma yanzu aka fara bugawa. Toh fahh. *+______________________+* *ABIN YABO BOOKSHOP* Kasuwar Rimi Kano Tel:📞 *07038339244* ❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤ Kar ku manta da #comment #share #like #follow. ____** *GIDAN GANDU* **____ ❤❤By sadi-sakhana❤❤ Wattpad username:SAKHNA03 ❤17❤ Ina Shiga naji su nairah sunyi tsit da alama gulmata ma sukeyi,dan kwanannan naga wuyahnsu nema yake ya isa yanka,kallon kowaccensu nakeyi cikin kankanin lokaci suka shiga taitayinsu,shigewa nayi bandaki nayi wanka kafin na fito na kwanta sannan ana ta kiran sallah,gyara filona nayi na kwanta,khairah na kalla wadda take saitina a zaune itama daga idon tayi tana kallona tareda cewa , "Menene anty sameemah?" Murmushin jin dadi nayi yanda ta kiranin kafin nace, "Idan muallim yace ina nake a wajen sallah kuce bana sallah ne" "Ahh amma fah yau kwananki uku da yin tsarki,kuma muce masa bakya sallah a cikin mutane" "To Karku fada ku hadu dani,ina ruwanan dan kowa yaji bana sallah iye,dolene said nayi sallah ni ya takuramin dan yaci sa'a babu wanda nake tsoro duk duniyah sama dashi da wallahi saina koya masa hankali,kuma saura karku fada ku gani,hmmm" Komawa nayi na kwanta,dan wannan shine period dina na farko a duniyah,tinda yanzu naji a kwai excuse din rashin sallah ai kuma shikenan ta zo gidan sauki kuma,na samu abin cewa har sai yaganoni da Kansa. Komawa nayi na kwanta su kuma suka fita suna tura baki jin irin aikan danayi musu,gashi dole said dun fada ,dan yanzu ba karamin tsorona suke jiba,tun lokacin dana danna kan khairah a cikin ruwan toilet na ploshing dan ta zageni suka mungun tsorona kaman mala'ika,gashi kuma shaheedah bata nan dama itace take taremusu hukuncina idan suka shoga gonata. Ban ta shi a bacci ba sai wajen magriba,ina tashi na dauki abincina na ci,nasake wani wankan kafin kuma nafara shirye shiryen bin barauniyar hanya zuwa cell din maza,ban samu su hairah a dakinba sun tafi sallah dan haka har na bar dakin basu dawoba, Wajen babu nisa da inda muke dan haka dama sun san da zuwana kawai kofah suka budemin na shige,zama nayi a tsakar dakin ina kallon kareem wanda zaikai shekara sha biyar a duniyah,yarone amma shegen kansa ne,murdaddiyar wiwi yah mikomin na karba ina busawa,take wani sanyi yah ziyarci zuciyata naji duk duniyah babu wanda yafi burgeni sama dashi,hira aka shiga yi ta labarin duniyah da kuma yanayin yanda kasar take. Bani na dawo dakinmu ba said sha biyun dare,aikuwa ina dab da shiga dakin na hadu da nannyn mu mai kulada wajen,saurin juyar da fuskata nayi ina kallon kasa, "Ke seemah me kike a wajen" Shine abinda tace da Mamakin ganina a wannan lokacin,dayake nidin shigaba ce Cikin sauri nace mata cikina ne yah baci shine na fito domin nayi tusa a waje kar na damu su hairah,alamar kin kyauta tamin tareda yimin addu'a allah yah kara shiryamu,ni kuwa a raina nace,aida zanyi tusa dari wallahi duk sai sun sheka dan banga shegiyar dazan fito waje dan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55