Chapter 32
Chapter 32
banaso bawai fushi dakeba,bai kamata ki dunga kushe gidanmu a gabana ba" "Toh na DA in a" Takaicine ya isheta tana bayan mota,ga an katse mata aikinta na rana guda an hada ta da wayannan shashsashun waje daya a cikin motah,ganin abin yayi waya ne yasata daka wata uwar tsuka kafin ta fuske ta kalli window,dukkansu juyiwa sukayi suna kallonta amma babu dama sanin mai ya sameta tunda ba magana zata musu ba. Tin daga bakin kofar shiga garin yara suke ta shafa motar saboda yanayin kauyene sosai. Wani gida suka shiga wanda aka zagayeshi da dangar kara,tun daga cikin gidan suke jiyo murnar yara suna fadan isowarsu. Irin tabarmar karauno aka shimfida ga kuma kindirmo(nonon shanu)da kuma kaji da aka dafa saboda taryarsu,dan kowa yasan mutunci irin na inna hajara shiyasa komai idan daga wajenta ne toh yan uwanta basa kyashin nuna tasu bajintar,saidai marar nuna godiyah ya kushe musu,irin su saleemah dan fafur kin saka wani abu a cikinta tayi,itah a dole wai jagwalgwalone,sukuwa su sameer zama sukayi suka ci abincin sosai. Dan duk duniya sameemah babu wanda take ganin mutuncinsa badan yah tursasata ba ya mahaifin ummah ta wato Malam Mansur,saboda ya nuna mata soyayya matuka,musamman idan suka zo da inna hajara a wajensa take zama har su tafi yana mata labarai da kuma jan kunne,duk da bata so amma tana kokarin ce masa zata gyara. Mahaifiyar su inna hajarance ta zauna ana gaisawa Sannan wani lokacin idan ana tadi sai a dunga sako irin abubuwan da inna hajaran tayi a baya,sameemah ce tayi kuncin da fuska can kuma da taga abin bazai yiyu ba said tace, "Nikam iyah in san samu ne kidaina sako ummah in kina yin zanjenki kiyi zancenki kawai,bai kamata zance marar amfani a dunga saka ta ba gaskiya" Baki ta sake tana kallon sameemah wanda ta hade fuska tana wani bada umarnin a daina zancen ummahn tah, "Iyeee lallaima yarinyar nan toh kinci gidanku,bazan daina zancennata ba idan yar kice ke kika haifeta" "Toh ina ummah tace koh,to nace a daina haka kawai sai a dunga zancenta a kan abu marar amfani,ko kuma a dunga bada labarinta ga mutum marar amfani,hakan bai daceba" Sameer ne ya kalli sameemah wanda ta wani hade rai tana zuba tijara,sai a sannan ya gano meyasa take fadan,dan kawai an fadawa saleemah labarinta ne yasa take wannan tsiyar,jijjiga kai yayi yana Mamakin yanda yarinyar ta zama bayan tafiyarsa,kwata kwata ta koma kaman an sanja ta. Malam mansur ne ya shigo daga gona da fartanya a rataye a kafadarsa, "Lahh baki mukayi a garin,wa nake gani kaman sameer,ko dai gizone yake min kai?" Iyah ce ta amshe da cewar, "Ba gizo bane shine yazo da matarsa gashi nan,wata sabon gani a garin zariyah" "Toh madallah sannunku da zuwa yah iyalai tunda naga an fara tarawa koh?" Sunkuyar dakai sameer yayi yana sosa keyah kafin yace, "Iyalai alhamdulillah,mun sameku lafiya dai ko" "Lafiyah alhamdulillah,yah iyalinnan ka bata magana ne" Kunya ce ta kama sameer da halin saleemah na rashi girmama mutane,dan duk abinda ake idonta akan malam din amma gaisuwa ta kasa hadata dashi,shikuwa irin mutannene masu nuna wa mutum kuskurensa sannan bayason raini ko kadan shiyasa ko wasan kaka baya yi. Jungurarta yayi yana mata alama da ido,saida taga ransa ya baci kafin ta gaisheshi tana wani yah tsina fuska. Shima dayake baya daukar raini amsawa yayi ciki ciki kafin yayi hanyar dakinsa. Iyah ce takallesu tareda cewa, "Zaku kwana mana ne koh kuma akan hanya kuke kaga saimuji mai za'ayi" Saleemah ce ta washe bakinta dan dama tun dazu take so taji anyi zancen tafiyah,tun kafin ta bude baki sameemah tayi saurin cewa, "Eh iyah kwana zamuyi mana ba yau zamu tafi ba" Takaicine da mamaki ya cika saleemah lokacin da taji abinda sameemah tace,shikuwa sameer a bangaren sa bai damuba duk yanda akayi dayane,saidai shima yayi Mamakin sameemah amma yasan da biyu tayi hakan,dan saleemah taji haushine. Dakin dayake gefen iyah aka gyara musu domin su kwana shikuma sameer ya shiga dakin malam din. Katifa dayace a dakin ta bunu saikuma tabrmar karauno,a tare suka shiga dakin su biyu kowa yana karewa dakin kallo,saleemah ce ta bude baki tana kallon itacen da akayi rufin dakin dashi ga kuma yayi kasa kaman zai kifo a kanta,hannu ta kai tana taba plastar kasar da akayiwa daki da kuma wanda akayi a kasan dakin. Bata ga komai ba saida aka zo kwanciya ta dora hannunta akan katifah taji wani tauri kaman buhun siminti,ja tayi da baya tana zare ido tareda cewa, "Nikam gaskiya bazan kwanta akam wannan abunba ,wannan ai saina tashi da ciwon jiki gobe" Jin abinda ta fadane yasa sameemah kara matsawa ta baje akan katifar sosai yanda babu wamda zai iyah sake kwanciyah akai idan ba jinjiri bane,wata uwar hamma taja tareda juyawa da alamar bacci zatayi. Saleemah tafi kusan awa daya a tsaye itah bata kwanta ba itah bata zauna ba,ganin yanda kafafunta suka fara gajiyah ne yasa ta zaunawa dabas akan tabarmar tana karewa sameemah kallo da take kwance a akan gadon cikin takaici. Kwanciyah tayi akan tabarmar saidai koh minti uku batayi ba ta tashi ta zauna,saboda yanda taji kaman a saka ta a kabari,bubbuga katifar take akan sameemah ta tashi amma tayi shiru kaman dutsi. Har ta juya zata kwanta kuma sai taji motsin wani abu a dakin,bata kawo komai a ranta ba ta gyara kwanciyarta da niyyar yin baccin kawai. Wani katon abu taji akanta amma bai kai kuliya ba saidai katone,ihu tasaka tana kakkade jikinta,shikuwa beran tuni ya fice a dakin. Jijjiga sameemah take tana hawaye amma shiru babu alamar ma zata motsa,da haka tana kukan bata san lokacin da bacci ya dauketa ba. Da safe da ta bude idonta a kasa ta ganta kayanta sunyi futu futu da kura saboda artabun da sukayi da berayen dakin,sameemah tah kallah wanda ita ma tashinta kenan tana mike hannu babu ko salati,saleemah ce ta kalleta tareda cewa, "Jiya kika tare katifar ina tashinki amma baki jiba ga kuma wasu abubuwa a dakin koh" "Ina jinki rass ba bacci nayi ba,dariyah ma nakeyi har kika gama kukan kikayi bacci" Da sauri Saleemah ta zabura daga inda take zaune kafin tace, "Dan tsabar iskanci dama kina jina ina tashinki kikayi shiru?" "Toh uban me zan miki,goyonki kikeso nayi ko me?" "Amma dai ................." "Kinga karki dameni da surutu da sassafe nan,ajiyarki aka bani mtsewwww". Tun daga haka babu wanda yasake magana acikinsu har suka fito karyawa wajen iyah. Anan ne suka hadu da sameer wanda shima ya fito daga dakin malam. Gaisuwa aka farayi itah kuwa saleemah sai shagwaba take yiwa sameer ko kunya bata ji. Kaman mai zargin wani abu sai sameer yace,naga dakinku shiru kunyi bacci mai dadi koh?",iyah ce itama tace, "Lallai kam dan naji da asuba ma shiru basu fitoba" Kunyah ce ta kama saleemah amma sameemah koh a jikinta saima kokon da takai bakinta a karo na biyu,fada sameer ya fatayiwa saleemah ta inda yake shiga ba ta nan yake fitaba,wanda yana cikin fadan ya kalli sameemah da niyyar bata itama nata kason,sauke kofin tayi kafin tayi saurin cewa, "Karka tambayeni komai ,saboda ba'a tambayar mace tayi sallah,yanzu zaakji kunya da jin amsata kuma ba abinda ya dameni ehe,(kiji
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55