Chapter 36
Chapter 36
zasuyi,ko sallama surayyah batayiba haka ta shigo tana wani cika,dukkansu tashi sukayi suna kallonta da mamkin ko kwarzana babu a jikinta,bayan hoton da aka turomusu duk jikinta ciwone. Mahmoud ne yafara cewa, "Ke ya na ganki kaman babu abinda yasameki baayan jiya video da suka turomin nishi kike yi kaman zaki mutu" "Ba abinda suka min,duk nice nayi saboda su saka ka bada kudi,dan cewa nayi zan taimakesu,amma wannan shugabar tasu ta ce wai bazata karbi kudiba saka hanunuka kawai take bukata a wannan paper" Da bakin ciki sir Mahmoud bai san lokacin daya zabga mata mariba da kuma yin boll da itah,kuka ta rusa tana kallon ummahn ta,itama kawar da kai tayi da a wannan fadan babu dama tayi magana dan surayyah ce bata da gaskiya. Haka ya dak at a saida tayi lis tukunna ya barta. Cikin sheshshekar kuka tace, "Kuma an taimakesu din,naga inna ce ka bani kudin hanani kakeyi,ka bawa su yaya Najeeb,kuma koh kasheni zakuyi saidai kuyi,ni yanzuma idan nasamu dama wajenta zan koma aiki. Dan takaici shigewa daki yayi kaman zai tashi sama,itakuwa mahaifiyar su ce tazata daga kwancen da take tace, "Gaskiya bakyaji surayyah,duk wuyar dayasha ganin kin fito ashe da hannunki a ciki,saiki tashi mutafi gida ai kafin ya karisa ki" Da haka uwar ta jata suka tafi nasu gidan,shikuwa uban dama dayajj abinda yafaru tun da farko yabar gidan. A cikin mota kuwa sameemah ce ta kalli C.I.D,tace, "Kafadamin inda zan ajiyeka dam akwai wajen da zanje daga nan" "Ahh KO Ina ma kika ajiyeni duk dayane" Fakawa tayi gefen hanya ta saukeshi kafin tayi hanyar gidan alhaji bala direct,tun kafin ta kai ga shiga cikin gidan tayi wani murmushin migunta. Da shirinta tazo dan jiyah C.i.d ya fadamata duk wani shiri da alhaji balan yakeyi akanta,kuma dama tayi tunannin hakan,dan a rashin muyumci irin nasa,da kuma itama irin tsiyar da tayi masa tasan bazasu kare iyah hakaba. Shi bazai fasa daukar fansaba itama kuma bazata daina yaki ba har sai ta hau kan kijerar shugabar vigilantee tukunna,saboda tarihin da takeso ta kafa bazai tafiba saida wannan kujerar tukunna. Danna kai tayi cikin ainihin gidansa kuma tasan yanannan. Mai gadine ya bude mata kofa ta shige kafin yamayar da get din yah rude. ...........hmm mm D'an sa ma yadawo yana nan.😂🤣😂 *+______________________+* *ABIN YABO BOOKSHOP* Kasuwar Rimi Kano Tel:📞 *07038339244* ❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤ Kar ku manta da #comment #share #like #follow. ____** *GIDAN GANDU* **____ ❤❤By sadi-sakhana❤❤ Wattpad username:SAKHNA03 ❤25❤ Saida ta gama saitawa kafin ta fito daga cikin motar,hanyar dazata kaita cikin gidan ta nufa tana wani shekar iska. A bakin kofar tayi sallama wata mata da alama mai aikice ta amsa mata, "Matar Gidan tana cikine?" "Eh hajiya tana nan bari nayimiki iso da itah " A kujera ta zauna kafa daya kan daya,wasu samarine suka shigo guda biyu suna ta magana,har saida sukayi wata hanya kafin daya daga cikinsu ya kula da itah. "Lah umar wallahi wannan zazzafar yarinyar danake fadamaka na hadu da itah a club toh wannan ce" Yafada yana nuna sameemah,itama kallonsa tayi sau daya dan taganeshi sarai,shine yace mata sunansa tukur. Cigaba yayi da magana tareda tsayar da ummaruje a waje daya. "Kai ban gane ba fah ko yar uwarkuce,naga ta sake a falon daga gani ba zuwanta na farko ba kenan" Da yayi niyyar share abin amma daga kallonta dayake shima dan duniyar ne,cikin sakanni yaji ya fola mata shima. Komawa falon sukayi suka zauna,ummaruje ne ya daga girar barin dama yana lashe baki kafin yace, "Yan mata me ne sunanki,abokina yace kun hadu a club daga gani kema yar hannunce wato ta hannun damanmu" "Like father like son" Sameemah ta fada a ranta,dayake ta sha kansu iyah rashin mutunci,kara daga kafarta tayi tana wani jijjiga ta irin ta shegun matannan,saida tah ciji lebenta ta gefe da hakoranta kadan kafin tah kashe murya tana cewa, "Uhm Wai ni sunana sameemah saidai banji sunan gwarazan mazanba kuma?" Ummaruje ne yah washe baki har kunne kamar gonar auduga kafin yace, "Sunana umar,ina karatu a abroad sannan nan gidanmune kuma nikadaine a namiji a wajen babana sai kanwata da tayi aure" Yah karisa magana yana kafafa,shikuwa a bangaren Tk mamaki abin yabashi domin yasan haduwarsu ta baya da itah batayi kama da wannan da take zaune ba,shikansa badan yagane fuskar ba zaice sanja ta akayi,waccer fuskarta banu annuri ga kuma uban shaye shayen da tayi,amma wannan idan ka ganta saika ce ai batasan menene fushi ba,dan fuskarta sai murmushi takeyi da annuri. Hada ido sukayi da Tk da kuma sameemah,wani kallo tayi masa na alamar gargadi,cikin sauri kuwa yah sauke idon tareda wayancewa yana dariya. Suna ta tadi dukkansu babu wanda yah kulada zuwan alhaji falon shiga hajiya Mairo,jerowa sukayi ko wannensu kaman zai fashe dan kiba,musamman ma hajiyah mairo sai huci takeyi. Tsayawa su sameemah sukayi da tadi ita da ummaruje wanda ya zare sai surutu yakeyi kawai dan yaga wannan kyakykyawan Murmushin a fuskar sameemah. Hajiyah mairoce ta tambayi ummaruje tareda cewa, "Kai daddy wannan kuma fah a ina kuka samota?" Sameemah ce ta hada ido da alhaji bala wanda yake feso gumi a akan fuskatarsa ta kyasta masa ido batareda kowa yah kula ba, "Ahh mommy nima anan na ganta ,nayi zaton fah kin santa,tana jiranki ne ki fito" "Ahah ni bansantaba kwata kwata" Tun kafin sameemah ta bude baki zatayi magana alhaji bala yayi sauri ya rigata saboda yaga niyyar ta kenan ta tona masa asiri, "Ahh hajiyah sai yanzu nagane ta ,ai yar gidan aminina ce,yayi min zancen tana neman kudin makaranta toh shine nace ta zo ta karba" "Ayyah to ai bazata tsaya anan ba sai tayi magana kuma" Wani Murmushin sameemah tasake yi masa mai nuna alamun ka ceci kanka,shikuwa ummaruje jin abinda akace gameda sameemah cikin sauri yace, "Lah Ashe kema student ce,allah ya taimaka,amma da kin bani number ki ko zamu sake gaisawa dan yanzu fita zanyi foot ball ba lallai na dawo na sameki ba " Yana gama fadan haka yabawa sameemah wayarsa,itakuwa kodan taga yah alhaji bala zayyi cikin innocent smile ta karbi wayar ta saka masa number tah. Tun wajen yayi tsallen samun nasara kafin yah fita aka bari daga alhaji sai hajiyah,itama hajiyah mairon Murmushin takeyi ganin abinda dannata yayi, "Yarinya ki saki jikinki kinji,idan da wani abunma kizo kanki tsaye,babu wata matsala" Sunne kai tayi kaman yar arziki tace, "Nagode hajiyah allah ya jikan mahaifa,yasaka muku da alkhairi" "Ameen ameen diyar albarka,menene sunanki" "Sunana sameemah hajiyah" "Kai suna kuwa mai dadi,yah dace dake sosai" Da haka hajiyah ta koma sashenta tabar Alhaji bala a tsaye wanda yayi simmm kamar gunki. Sameemah ce ta tafa hannunta kafin yadawo hankalinsa, "Amma seemah menene wannan kikeyi da iyalina,musamman umaruje wanda ba hanunsa a komai kike son ki cutar dashi" "Ka ga dakata cutarwa kuma bashi numbar ta shine cutarwa,cinyeshi kaga nayi komai,sannan abinda nakeyi sunansa wasa" Ta gama maganar tana kyalkyalewa da dariyaar mugunta, Takaicine yakama alhaji bala yarasa ma mai zaice,ganin tsayuwar ta gagareshine yasa ya samu kujera ya zauna wanda take facing din sameemah. Yanzu dai mudawo zancen gaskiya,duk abinda zakiyi kar ki taba iyalina,kowa yah ajiye iyalai a gefe,idan kuma ba haka ba kinsan kin fi kowa iyalai sama dani,zan iyah daukar mataki" "Lahhh
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55