Chapter 45
Chapter 45
iskanci ne ma ai sun fimu,kawai dan dai suna lungune" Tashi sameemah tayi tareda iza ketarta tana cewa, "Ina ne muje ki nuna min wajen,wayaki k'aari kuma" Wani lungu suka bi sai gasu a wani gidan irin wanda sukayi kame a cikinsa,dakin dayake farko sameemah ta bankada tah shige,zare ido tayi dan ganin da wanda suka hada ido. Shima zare idon yayi da yai kulu kulu a duhu,gashi yah hada gumi shirkiff. Da kyar bakinta ya samu damar tattaro harafin kafin ta furta.... "Kawu sheeeeehu!!!" Toh lokacinku yah kare sai wani jirgin yazo zai dibeku yanzu dai ku sauka a nan wajen.............. *+______________________+* *ABIN YABO BOOKSHOP* Kasuwar Rimi Kano Tel:📞 *07038339244* ❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤ Kar ku manta da #comment #share #like #follow. ____** *GIDAN GANDU* **____ ❤❤By sadi-sakhana❤❤ Wattpad username:SAKHNA03 ❤31❤ Tunda suka hada ido da sameemah duk wani motsinsa yah dauke saura kawai rawa da jikinsa yakeyi,musamman daya ganta da kayan da duk masu hali irinnasa suke tsoron su rutsasu. "Miye katsaya ka tsaya kana kallonna koh so kake nazo na saka maka wandonnaka harda wani rawar jiki,ai na karya kakkeyi zakayi bayani ne yau" Har sannan bakinta dauke da murmushi dan taan son irin haka dama,Kallon matar tayi wanda ta ja bargo tah rufe jikinta tana sunkuyar da kai. "Hmm ji munafuka dallah ku tashi ku fito inason ganinku a waje yanzunnan" Tana gama fadar hakan tah fice daga dakin tareda nufar sauran dakunan. Babu kowama a cikin su saboda tuni sauran ma'aikatan suka rarrako su zuwa wajen sauran. Dukkan su maza da mata yara da tsofi kkwa yah Zauna yayi shiru domin yaji abinda zai faru,mai gidan hayar ne ya shigo da sauri wani yaronsa yana biye da shi,da waya hannunsa koh takalmi bai saka ba,daga ido sameemah tayi tana kallonsa domin jin shikuma da me yake tafe, "Ina gida naji ance gidan hayata ba lafiya,wai masu kamen karuwai sunzo,toh ke kuma wayah aikoki saboda yanzu ma muka gama waya dashi bayuimin cikyakykyen bayani ba,dan idan kudinharaji ne nariga na bayar hada karin danakeyi a shekara,amma waka a bakin mai ita tafi dadi bari kiyi magana dashi. Yana gama fadar hakan ya mikawa sameemah wayar dake hannunsa,dauka tayi kafin ta saka hands free, "Hello........hello.sameemah bai kamata daga hawa aikinki har kin fara saba dokaba,kamata yayi idan zakiyi abu toh ki nemi shawara mana,yanzudai komai yah wuce ki baro Gidan zamuyi magana kawai sannan..........." "Alhaji bala KO nace Bala,kadaiji yanda na kira sunanka koh,toh billahillazi idan na sake jin hannunka a cikin aikina koda dan kadanne,kai ko wani nakama yafada maka kabashi koyon baya,toh wallahi idan muka dunga buga chakwakiyay dakai saina yi maka kaca kaca,hatta zaman garinnan ma kai har cikin yan uwanka ma sai yayi maka wuyah a rayuwarka,idan kuma kana tunanin ban kai nayi hakan ba toh bismillah mu zuba ni dakai" Daga wayar tayi ta kwankwatsata da kasa tun kafin ma taji mai zaice daga daya bangaren,jiki na rawa mai gidan hayar yaja da baya yana kallonta. "Kai kuma idan baka bace a wajennan ba ,toh idan na tashi dakai zan hada harda mataimakinnaka" Tun kafin ta rufe bakinta yah yayi waje da sauri yana baza rigarsa.kallonta ne yah koma kan wanda aka kama din wanda idonsu zuwa yanzu yah raina fata, "Ku kiramin wanda na aikesu kuma na ce su tsaya a waje yanzunan" "An gama ranki yah dade" "Wani dan gajere daga cikin yan vigilantee dinne yah fita da gudu zuwa waje,basu dade ba sai gasu sun dawo da wasu garada guda biyar,kowannensu dauke da dorina mai kai biyu, "Kubisu KO wanne kuyi masa bulala goma goma,sannan ku saka su a mota zuwa office" Ihu suka fara da kururuwa saidai babu yanda zasuyi tunda tafada toh fah lallai sai anyi musu. Bayan angama round Donne kowa sai nishi yake yi wasu kuma suna tah soshe soshe,masu ragwanta kam harda kukansu. Har an tashi za'a tafi sai sameemah tah dakatar dasu tareda cewa, "Tun daga ina akeson shugaba yayi adalci idan ya hau kan mulki?"." Had'a baki sukayi tareda cewa,"daga gidansu" "Toh Indian hakane a matsayina na shugaba mai adalci sannan mai nuna yakamata,zanyi adalci ta hanyar karawa kawuna dayake wajennan bulala ashirin kacal,kunga tah kama talatin kenan anyi masa ninkin nasu sau uku" Dama tun lokacin da sameemah tafara wannan maganar muguntar kawu shehu ya fara tara kwallah a idonsa saboda yasan bazata barshi ya tafi haka banza ba. Tana nuna yatsanta akan sa garsawannan suka tattagoshi dama basu gaji ba,taleshi sukayi aka fara tsula masa sabon wani lissafin. Saboda tsabar wuyah kasa ihu yayi sai nishi kawai kaman balamar tunkiya tazo haihuwa,kusan za'a kai karshe kawai gani sukayi wandonsa ya rine da fitsari yana zuba. Duk da zafin dukan da'aka yimusu saida wasu sukayi dariyah ganin yanda kawu shehu yake fitsari. Kowa tashi yayi yana dingisawa har wajen motar tasu,shikuwa kawu shehu saida aka tattageshi saboda lagabewa da jikinsa yayi. Suna zuwa office suka samu su surayyah sun dawo,kuma sunyi nasarar kamoshi kaman yanda aka fadamusu,saidai masu sata a kasuwane ba'a kama ko daya ba. Wajen da'aka kaishi sameemah ta nufah tareda tsugunnawa a gabanta. Dayake dan duniyah ne kallon cikin idonta yake yana cewa, "Dama barin zancen nan kikayi yah wuce yan mata,dan babu abinda zaki iyah a kai,dukane na riga na dake shi" Tashi tayi daga kusa dashi dan bai isheta ma kallo ba a yanda yake,wani na gefe ta bawa umarni akan yayi masa hukunci kafin a kai shi wajen yan sanda yah bada tara. Marinsa ma'aikacin yayi amma yah zuyah fuskarsa yah tofar da yawu yana Murmushin taurin kai. "Ashe Baki cika sunan ki ba na jar wuyha sannan baki cancanci gwagwarmaya da irin mu ba,nayi mamaki da aka cemin yanzu macece shugabar yan kato da gora,amma yanzu na gane kawai daurin kafa kika samu har kika hau kan kujerar,kuma kina daga gefe kina saka mutane aiki suna yimiki,kir idan kin isa ki kiyi dealing da mu mana da kanki" Har sameemah tah taka kafarta zata bar cikin wajen amma ta tsaya cak saboda jin maganar dayake fesa mata,jijiyoyin wuyanta ne suka tashi lokaci daya,damke hannunta tayi da cije baki,ba wanda bayyi mamaki ba ganin yanda takoma gabansa tah tsugunna. "Bazan ce komaiba akan abinda kace,saidai daga ni har kai zamu buga wani wasa sai aka ya zai in ma dorani akayi akan mulki saboda inada daurin gindi koh kuma matsayina yakai nasamu. Wasan mai sauki ne idan ka fahimata,zamu bada filin daga tsakaninmu,kowa zai fita babu wanda zai saka hannu,sannan idan har kayi nasarar yimin dukan da bazan iyah tashiba toh zan baka duk abinda ka bukata kuma za'a sallameka anan wajen,kuma babu ruwan shari'a a ciki." Murmushin jin dadi yayi dayaji abinda tace,shikuwa wanda aka Bashi ajiyarsa kallon sameemah yayi da alamar gargadi na batasan yan iskan zamani ba fah. Nuna masa tayi ba matsala tareda cewa, "Karka damu babu abinda zai faru ,kawai ka bamu waje sannan kace ban yadda koh wani abune yah faru wani yah shigo ba" "Shikenan tunda kince haka amma duk da haka zamu tsaya a kusa saboda tsaro" Jawo musu kofar yayi tareda nufar su burgu dan yasanar musu abinda yake faruwa saboda yasan su zasu iyha yi mata magana,amma yana gama bayanin yaga kowa yah cigaba da abinda yakeyi. Kallo
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55