Chapter 17
Chapter 17
suna tsorone basu fitoba,yanzu kam ai munfita a cikin haske,kafar mutane ta d'auke a wajen ,duk abinda zasumin ma babu wanda zaiji su" Zaro ido matan sukayi da Mamakin yah akayi tasan abinda suke niyyar aikatawa,kallon kanannan yara tsyimusu kafin tak'ara da cewa, "Lallai Ku yarane,a tunanin ku bansan me kuke nufi ba,toh tun a hanya nakulada ku kuna bibiyata,har na shiga club din kuma kuka kama table,bayan kunyi waya da wanda yasakaku kafin kuka nufo inda nake". Fezar da iska tayi daga bakinta irin na takaicinnan sannan ta d'ora da cewa, "Lallai wanda yah aikoku bai sanni ba har yanzu,ku kuma ba laifinku bane,amma idan muka gama da wannan cakwakiyar ku tabbatar kunnemi inda nake kunzo ,domin inason yin magana daku" Bata gama maganar ba tajiyo karar fed'uwa a bayanta anabin kid'an wakar *naira maley*,koh kuyawa batayiba har me wakar yah zo ta gaban ta,da wata wuk'a a hannunsa ya sak'alata a wuyansa. "Yau wata tazo hannu babu yaranta,ina dasu kike takama har kika aikatawa shugaba haka(buba jini).Toh yau saidai uwarki ta haifi wata,dan saimun farke cikinki mun cikashi da kasa,mun jefar a hanyar dabbobi" Duk maganar cikin larabci yakeyi irin na sudan,dan shikansa mutumin baiyi kama da mutanen nijeria ba. Farine sol yahsha rawani ,amma koh a duhu mutum yah ganshi yasan ba karamin tantiri bane. Wani ne daga cikin mutanensa yah matso kusa da itah tareda fassara mata abinda ogannasa yace,saidai har yah gama fassarar babu alamar tsoro a fuskar sameemah,dan ko motsawa batayiba daga inda take. Mutumin ne yah kalli yaronnasa tareda tambayar, "Ka fassara mata duk abinda nace kuwa?(yah kara fa'da cikin harshen larabcin)" "Eh shugaba dukka na fassara mata" Fusata yayi da yanda tah wani tsaya babu alamar tsoronsa,bayan duk kasar dayaje kowa tsoronsa yake,cikin zafin nama yah d'aga wukar hannunsa yah shaftawa sameemah a hannunta na hagun inda rigarta bai rufeba,wanda kuma yayi dadai da isowar su burgu wajen da gudu. Ihuu suka fasa dukkansu ganin abinda akayiwa shigabar tasu,burgune yah isa wajenta da sauri,saidai tsayawa yayi cakk a gabanta yana karewa wajen da'aka yanketa ido,jijjiga kansa yayi tareda murza idonsa,anya kuwa yah gani dadai,saidai lokacin daya d'ago idonsa yah kalli Mamakin dayake kan fuskar kowa har shikansa wanda yayi aika aikar sai hakan ya tabbatar masa da abinda yah gani gaskiyah ne ba gizo idonsa yayi masa ba. Wajen da aka yanki sameemah ne yake komawa yana had'ewa dakansa,kaman yankan wuk'a bai tab'a wanzuwa a wajen ba,shikansa jinin daya fito a wajen k'onewa yayi ya b'ace b'atttt.😲😲😲. *+______________________+* *ABIN YABO BOOKSHOP* Kasuwar Rimi Kano Tel:📞 *07038339244* ❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤ Kar ku manta da #comment #share #like #follow. ____** *GIDAN GANDU* **____ ❤❤By sadi-sakhana❤❤ Wattpad username:SAKHNA03 ❤13❤ Ganin kallon da burgu yake mata yah isheta ne yasa ta tureshi daga kusa da itah kafin tace, "Kai miye kazo kusadani har haka kaman zan maida ka cikina,wato dana ce karkuzo saida kuka biyoni koh,banzaye taron matsorata,ji idonku kaman kunga aljani da tsakar dare" Har tagama masifarta bayan ta tureshi bai ko motsaba,saima kallonta yakeyi kaman yah samu hoto. Wuceshi tayi taje har gaban shugaban,wiwi din da take hannunsa tah karb'a saida tayi masa zuk'a mai kyau kafin ta fesar tah hanci da baki,jefarta tayi take a kasa kafin ta mayar masa da martanin maganar da yayi mata cikin harshen larabcin da babu inda akeyinsa sai ainihin cikin kasashen larabawa. "Oh da kana tunanin banajinka d'azu koh,hmmm lallai kana cikin duhu a gameda sanin koh ni wacece,saidai yanzu zan nuna maka wani misali" Tana gama fad'ar hakan tayi masa ruk'o tareda kafa hakoranta a akan wuyansa,babu wanda yasan mai yah faru sai ganin sa sukayi dukka yah fad'i a kasa kaman wanda yah mutu. Kare masa kallo tayi tana goge jinin dayake bakinta,tana kuma tofar da yawu, "Ka tursasani yin abinda banida niyyah,ku kaishi asibiti aka ra masa jini yah mori lokacin sa kafin su biyo nemansa kwanan sa yak'are" Juyawa tayi ta bar wajen,har ta yi nisa amma su burgu basu biyota ba kamar wanda suke jin tsoron ta a yanzu,kallonsu tayi harda matan da aka aikosu gurinta,kafin tace, "Duk wanda yake wajennan yaga abinda yah faru inason gobe da safe yah sameni a office din kungiyata ,wanda bai san wajenba yah samu yarana su rakashi,kunji ina?" "Eh munji muka zamu dole" Kowa a wajen yah amsa jikinsa har rawa yakeyi tun daga kan yarannasa har yarannata. Tana komawa gida ta shige dakinsu kan gadonta tareda rike kanta wanda yake barazanar fashewa dan azabar ciwo,da haka har bacci barawo yah saceta. Da safe gidan da shirye shirye aka tashi na zuwan major sameer wanda zasuzo shida matarsa da kuma d'ansa,zuwan gobene amma tun yau ake shiryawa saboda cewar matar tasa yar shugabansu ce. A bangaren sameemah kuwa da ta tashi ma batasan wace wainar ake toyawa ba saboda wankan ta tayi ta fice babu wanda tayi wa magana. Motarta ta nufa wanda ta ajiye a kofar gidan,abin mamaki babu yaro ko d'aya a kusa da motar,saboda da wanine koh mashin ya ajiye sai an jefar dashi barekuma sabuwar motah Direct gidan kungiyar tasu ta nufa inda take kiransa da office dinta,saboda a makare ta zo ,gidan a cike yake kowa yah hallara ana jiran isowarta. Tana shigowa kowa yayi tsitt kaman ruwa yah cinyeshi saboda ganin fuskarta a murtuke kaman ta boss din y'an indiyah. Zama tayi akan kujerarta yayin da kowa yah zube akasan wajen yah zauna kaman wanda akayi musu wahayin su zauna a lokaci d'aya,kallonsu tayi da mamaki ganin harda su burgu ake mata kallon dodanniya ko mayyah,wanda ko kadan bata ga laifinsu ba saboda ita kanta tasan ta dace a kirata da dodanniyar,domin tun tashinta lokacin data fara maida martanin abinda ake mata ,yazamana kowane halitta yah rabeta sai yaji tsoronta,"lallai akwai aiki"ta fad'a a ranta. Gyaran muryah tayi kafin daga baya tace, "Kowa yah ga abinda yah faru jiya daddare ko?" "Eh kwarai kuwa mun gani sosai" "Toh inaso daga nan wajen kar kowa yah tuna cewa yah ga abinda ya faru barekuma yabawa wani labari,idan kuma ba haka ba,............" "Baza akai ga hakaba babu wanda yah tuna abinda yah faru ,koba haka ba yan uwa" Burgu yah fad'a yana kallon kowa a wajen,cikin sauri kuwa suma suka amsa da cewa, "Hakane babu wanda zai tuna da abinda yah faru" "Shikenan naji abinda kukace,saidai nasan a yanzu kunsan koni wacece,kowa a cikinku zai dunga kallona a matsayin dodanniya,kaman sauran mutanen dana yi rsyuwa dasu a baya,saidai bazan ga lafinkuba saboda nasan dagaske hakan nake" Sukunyar dakai tayi alamun hakan yah tabata,saidai cikin sauri tamayar da fuskarta wanda babu wanda yasan mai yake cikin zuciyarta. Burgune yah d'ago kaman zayyi magana sai kuma yayi shiru,kallonsa tayi ganin yanda magana ma yanzu yakasa yi mata,ganin yanda a lokacin baya har kyaleshi take idan yah isheta da surutu, "Karamin shigaba wace magana kake da itah? "Eh dama shugaba,mun ji kinyi yaren larabci kaman wata balarabiyah,ga kuma abinda yah faru wanda gaskiya yah shige mana duhu,toh kafin kizo kowa yah ce na taimaka na tambayeki ,idan bazaki damuba munason jin tarihinki" "Shine bukatarku jin labarina" "Eh Ranki yah dade" "Toh shikenan bari naga koh bazai d'auki lokaciba,saidai inaso kusani bawai zan fad'amuku saboda ku kai wa wasu labariba,saidan inason yin aiki daku,kuma naga yakamata kusan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55