Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 51

Chapter 51

Gidan Gandu Book 1 Complete Hausa Novel 1,264 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

naga sa'annina a gida zasuyi aure gaskiya nima auren zanyi,idan kuma kaga bazaka aureni ba toh gaskiyah karka sake zuwa kofar gidannan" "Haba salma baby meyasa kike haka,yanshe zan bari ki subucemin yanda na sameki dinnan,dudu watam mu biyu amma kin sace zuciyata,ai irinku mutum yasaka a cikin gida yah boye hankalinsa kwance yana sakawa a gaban motah" Murmushin jin dadi salma tayi jin yadda alhajinnata yana gwadata da kuma yaba kyanta, "Toh shikenan alhaji,nima kaine a raina ai idan har kaga kana ciki toh ka turo gidanmu,idan kuma ba haak ba na bawa wasu dama" "Ahah baza'ayi hakaba indai aurene ai abune mai sauki" Da haka kuma bayan zancen auren suka fara tabe taben su har wajen karfe dayan dare kafin tah fito ta shige gidannasu . Kulu ce tah kalli manjo wanda zamansa a gida baya zuwa wajen shaye shayen har yayi dan hankali saboda bata gara masa badaidai ba din, "Yanzu manjo kai baka ga hakan yafi maka ba,ji na lokaci daya har ka dan sanja abinka" Kara gyagygyara kayan yakeyi yana jijjiga kai shi a dole yayi abinda aka yabeshi, "Ai nake fadamiki yanzu haka idan na fita neman aiki zanje saboda nima a dunga ganina da kamala,ko yah kikace" "Eh hakan yayi,toh ni ai gwanda da akyi maka dukan gashi ai ka nutsu kana shirin bin hanya" Harararta yayi yana cewa, "Kefah dadina dake kenan ba'a abin arziki dake,toh in fadamiki makasudin kara shiriyahta saboda taron da za'a yi a gidannan ne,dan naji labarin duk yan matan gidan aurensu za'a yi lokaci daya,kinga idan mazajen suka ganni a haka,kuma aka nuna ni akace nine yayansu na karamin kyauta zasuyimin ba koh?" Dariyha kulu ta kece da itah tareda cewa, "Lallai manjo har yanzu da saura,kaidin yanzu jira kake ajo auren kannenka mazajensu su tara maka dukiyah ?" Kai mata duka yayi tah shige daki,sai kimbura fuska yakeyi ganin yanda take masa dariyah dan yayi mata tadi zasu samu abin alkhairi. Dukka yan matan kowa hidimar aurenta takeyi banda sameemah wanda hankalinta gabadaya akan aikimta yake,tah wani wajen ma dadi takeji zasu tafi subar gidan ta maida dakin iyah itah kadai kawai. Yanzu sameerah duk wani abu da zai shiga tsakaninta da sameemah gudunsa takeyi tumda ta gano sameemah tafi karfinta,saidai mai hali baya fasawa ,bayan mutuwar tsohon bokanta yamzu ta samu wani,wanda yafi na da yimata aiki,saidai koda wasa bata yarda wani tayi maganar sameemah a wajensa balle kuma yimata asiri. Ummaruje zaune a falon mahaifiyar tasa bayan isha,shiru yayi baiyyi magana ba ita ma kuma hankalinta bai kai Kansba dan ko dauke kanta batayi daga kan shirin da akeyi a gidan television na bolly wood,ganin bazata kula da sunkuyar da kan dayake yi bane yasashi cewa, "Ummah! Ummah ummah!" Saida yakirata wajen sau uku kafin tah juyo ta kalleshi, Na'am son me ake ciki?" "Dama Idan abba yana nan inaso zamuyi magana ne daku" "Ahh wannan ba matsala bace bari na kirashi sai yah shigo". Suna zaune kuwa sai gashi ya shigo, shima zama yayi akan kujerar tareda daukar wani apple akan pilate yana ci. "U hmm mahaifiyar ka tace kanason magana damu,ina jinka" "Eh ......eh damaaaa abbba akwai wacce nakesone a gidan gandu shine nakeson aje nema min ,dan tah cema na turo,gashi babansu yace zuwa nan da karshen shekarar nan kowa a cikinsu tah fito da miji" "Toh naji dadi da ka fadi haka kuma munyi farin ciki,dan dama shi namiji cikar mutuncinsa shine aure,toh amma yar ina ce waye babanta" "Eh a Gidan Gandu take sunan babanta umaru,yayar sameemah ce ma" Hajiyah mairo ce tayi saurin cewa, "Ayyah Kaga nifi na allah,ni da da farko ma nayi zaton da sameemah za'ayi ashe kuma da yayrta ne ashe,toh allah yasanya alkhairi inshaallah za'a bincika sai ajen tambayowa" Duk maganar da akeyi alhaji bala bai ce komai ba sai wani shiru da yayi kaman wanda ya tafi wani nazari,maganar da ummaruje yasake yi ne ya dawo dashi daga tunanin daya tafi. "Amma ummah bazawara ce dan ta taba aure,amma koh shekara batayiba ta fito,dan ko da bata dashi" "Toh gaskiya my son bazaka auri bazawara ba ban aminceba sai ka nemo budurwa,ga mata nan birjik a gari......" "Meyasa kake haka alhaji,wannan wane irin zamcene haka,bawani dan zancen bazawara tunda aka fadi yar wacece ka wani hade rai baka ce komaiba,kuma naga annabi ma yana saurayin yah auri bazawarar,ai abin farin cikine dan ka zai dabbaka sunna,ni dai bazan hanashiba duk da banso ba amma tunda yana son shikenan bazan haanshi ba,saidai kuma idan akwai abinda kake boyewa?" "Ahh ha m.............ahahha babu abinda nake boyewa mai zan boye,shikenan za'a san yamda za'a yi kaje allah yabada sa'a" Shidai mamakin ubannasa yayi ganin yanda yake wata rawar muryah ta rashin gaskiya. Manjone a zaune a unguwar su kulu dayake nanne inda yah samu sana'ar had'a bulo,sumyi dan hutune dan kowa yaci abinci yah koma aiki. Wata kanwar kulu ce take ta fad'a da wata sai zage zage sukeyi an rabasu sunki su daina. Budar bakin wani a wajen sai cewa yayi, "Hmm ai wanna yarinyar bata da mutunci,dukkansu yaran gidan haka suke,naga kana ganin itah kanta yayarta wacce tayi aure a gidan gandu,duk da aurenta amma duk sanda tazo gidansu raba dare zasuyi suna hira da tsohon saurayinta har sai sukai dayan dare a wajennan,gashi babu dama a fada sai uwarta tace karya ne" Wanine shima yah cafke tareda cewa, "Toh laifinta zaka gani,naga shima mijin shashashane,inba marar hankaliba ka tafi rani har kayi kusan shekara biyu babu labarinka,idan ma ba irin su kulun ba wace matarce zata yadda,ni banga laifinta ba sai nasa laifin gaskiya,ai aure ba hauka bane koh" Duk maganar da akeyi a kunnen manjo wanda yayi mutuwar tsaye,banda juyawa babu abinda kansa yakeyi,dan jinsa yakeyi kaman a wata duniya yake. Tun kafim wani yah ganshi ya dauki rigarsa daya cire yah bar wajen siyarda abincin tun kafin wani ma ya ganshi. Shirye shiye ake tayi dan yau masu kawowa kayan auren su sameerah zasu zo itah da zainab,sai wani rankwada kai sukeyi,za'ayi aure watan gobe. Dare yafayi dan wasu kanma sun kwanta,alhaji balane ya shigo dakin hajiyah mairo wanda har tasaka kayan bacci, "Alhaji lafiyah na ganka da darennan babu alamar kwanciyah allah yasa dai lafiyah" "Eh lafiyar ce tah kawo haka,dama inaso muyi magana da kene saboda in fitah hakkinki" "Toh wace maganace haka inajinka" "Dama inasone na kara aure,kuma badan kin gazamin ba kawai ra'ayin hakkanne ya taso" "Aure! Aure!! Fah kace alhaji?,wacce shigiyar ce zaka auromin ka kawomim cikin gida yau shekarar mu talatin da takwas da aure?" "Haba hajiyah ki kwantar da hankalin mana,yarinyace ba lallai tah baki matsala ba dan koh kanwar ummaruje bata kaiba" "Kutumar ubancan,alhaji mai kake nufi,dan kaga kwaanannan nayi sanyi shine har ka samu kwarin gwiwar fadamin wannan maganar?,kuma ma dankayi mungun rainamin hankali hadda wani cemin yar yarinyace,wato ni na gama zama dakai da haifamaka yara,ka gama ragwargwajeni bari ka auro sabuwa dall ku more nikuma na zauna na zuba muku ido koh?" Hmm .....alhaji dani kake zancen kawai,kuma banson sake jin wata magana daga bakinka ka fice kabarmin dakina tun kafin raina yafi haka baci,hawan jinina ya hau ka kasheni da dalili kayi auren ka hankalin ka kwance" "Aurene kuma

Table of Contents

Chapters

55 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});