Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 48

Chapter 48

Gidan Gandu Book 1 Complete Hausa Novel 1,261 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

yah wuce kowa yah cigaba da abinda yake gabansa. Harkar aikinta kuwa sai abinda ya cigaba,dan koh wata bata cikaba amma suanan ta ya zagaya inda mutum baya tsammani a fadin garin. Da dare suna kwance dakin shiru kowa yana harkarsa sameemah kamma aiki takeyi a cikin system na wajen aikinta,sameerah ce tah shigo dauke da leda a hannunta sai wani daga kai takeyi,dagargajewa tayu a tsakar dakin tana fito da duk abinda yake cikin ledar. Da biyu takeyin abinda take dan kawai su salma su gani, "Kai koh a tarihi ban taba ganin yanda masoyi yake kulada masoyiyar sa kaman umaruje ba,gaskiyah na yarsa ba kyau ne da kwallaiyah yake sa mace tayi farin jini ba,idan itah mai sa'a ce shikenan,saboda bakin jini har ana binsa gida amma ba'a sameshi ba har yah tako har wajena yah zabi sarauniyarsa" Haka tah cigaba da surutunta da zarar bunu, amma babu wanda yah tanka mata,dan gwara ma salma taja tsuka amma sameemah kam koh daga idonta daga kan system din batayi ba, "Salma bisimillah ga kayan dadi,wanda ba'a ci a gida fah" "Ke sameerah iskancin ya isheki haka kodan kinga mu zuba miki idone iye,ta bamaci a gidan kedin ci kikeyi,banza sabun shiga kawai a cikin hakrkar" Dari yah sameerah ta sheke da itah dan dama so take wani yah tanka mata a cikinsu, "Sabun shigar shiyasa naga daga shigata da kamo babban kifi dan gidan manya saboda na cika mace" "Wacce macen kika cika,koh kinace babu wanda yasan asirin da kukayi masa ne keda uwarki,kuka karkatar da hankalinsa daga kan sameemah zuwa naki,ai kowa ma yaga kallon dayake miki yasan ba a hankalinsa yake ba,idan har kina ji da ke macece ai saiki kallameshi tah kissa ba ta asiri ba" Bakin cikine yah kama sameerah jin abinda salma take fada mata,bata san lokacin da ta kaimata raruma suka fara fada ba,cikin kankanin lokaci duk suka tumurmjshe naman kajin a da lemon a kasa. Feduwar da sameemah tayi ne yasa su tsaywa sai a sannan suka ga irin ta'adin da sukayi da abincin. Karnukan ne suka shigo da gudu,dan yanzu harda wani karami ma a cikinsu wanda sameemah tah samoshi a hanya yana halin jinyah,yanzu watansa daya kenan har koma kaman ba shi ba. Dan dama itah haka halinta yake,yawancin abubuwan da suke karkashinta taimakone yake hadata dasu,shiyasa koda kudi babu wanda yah isa ya sayi yardarta a wake abinda yake nata. Hannu tah mika tareda nuna musu naman dakaye kasa a babbaje. Sukuwa dama jira sukeyi kare da nama,ai babu batun jira. Sororo sameerah ta tsayah tana kallon sameemah wanda tah bawa karnukanta naman da saida tah hada da bada jikinta kafin ta samu duk dan tazo tayi burga a gabansu,dan kallon yamda yake mata mutane suke gani,amma har yanzu bata wani mallkaki zuciyarsa yanda take so Ba,kawai idan tayi magana ne yaka aiwatarwa amma dan shi a karan kansa baya yi mata abu dan racayinsa kawai, "Me kika aikata haka sameemah, nama nawa dana shigo dashi kika bawa karnukanki suke cinyewa" "Yanzu yah tashi daga naki ai,tunda kin gama dashi ta hanyar zubar dashi a kasa,kinga yah zama na karnuka tunda dama abincin kasa su ake bawa,dan karna wahalar dake ne kawai na basu,menene lafina a ciki Toh?" Har ta bude baki zatayi magana sameemah tasaka hannunta a baki shshshs da alamar tayu mata shiru . "Banason dog on surutu aiki nakeyi,kuma nariga na fadamiki dalili,idan har kika sake cewa takk kuma a kan maganar toh umarni zan basu suna gamawa da naman su koma kan naki naman,in kuma kin musa ki gwada" Ga kwadayi yana cin sameerah ga kuma haushin yanda ta samu naman amma bata ciba,ga kuma takaicin bata da ikon yin komai akan abinda sameemah tayi mata,,dan haka hadiye wani yawu kawai tayi tah fice a dakin,duk da tana ganin salma tana mata dariyar mugunta amma bata,kulata ba. Dakin inna ramatu ta shiga ta sameta tana ta nade kayan wanki akan gado,daga ido tayi ta kalli sameerah din wanda sai kumbura takeyi dan bakin ciki, "Ke kuma miye kika tsaya min a kai kaman kububuwa" "Ummah da na fasa amma yamzu ina so a zartar da aikin kawai,sona ke yanzu duk wani aiki da zai rikitah kwalwalwar sameemah tah haukace to ayi mata,umma idan da dama ma tah daina yin komai a rayuwarta tazama tamkar mutun mutumi" "Hmm kindawo hankalinki kenan,lokacin danake nuna miki gabar ai yamma kike dosa,dama na fada muku matukar tana numfashi sannan babu wani abu na dauri da akayi mata toh babu wanda zai yi rayuwar farin ciki kaff a cikin gidannan" "Ummah harda salma ma inaso ayi mata wani abu" "Keee rabani da taba salma uwarta maba a zaune takeba,sannan itah ba itah ce mataalarki ba a halin yanzu,su kansu mutanen gidan indai akan sameemah ne toh suna cikin tashin hankali idam asirin kanta yah karye,ke kina tunanin iyah ni kadaice kawai mai hannu a cikin aikin? Hmm akwai abinda yafaru wanda iyah mu muka sani kawai,yamzudai a bar wannan zancen tunda kince kin amince shikenan dama tun farko kece kika yimin gardama. Boka yace baya bukatar kudinmu shidai burinsa kawai ki kwana a wajen sa toh duk wani abu da muke bukata zai tabbata,kinga koma menene sai ki tambayeshi kawai,saidai daga yanzu ki daina tuntubarta da fada,saboda kar ta gano mai yake faruwa" "Toh shikenan ai gobe ma zan tafi,sai kicewa baba umaru na tafi kauyen kawunki saboda kinsan bayason fitarmu kwana a wani wajen,ai yamzu na tsani sameemah dinnan,dan idan muna zaune da umaruje har kirana yake da sunan fah" "Yanzudai mungama magana ,kuma sannan ki fada masa yah turo a da maga ba tansa idan kuna hira,saboda da wurwuri ake dukan karfe kafin yayi sanyi" Yau da safe kasancewar weekend ne babu zuwa wajen aiki,kowa yana gidansu,sallama akayiwa sameemah ana nemanta a waje,sai kace na miji babu alamar wani tambayar wani kafin ta fitah haka ta yafa gyalen abayar da take jikinta ta fita zuwa ganin mai sallamar. Mamaki tayi da taga burgune da surayyah a bayan mashin dinsa suna kallnta fuskarsu dauke da murmushi,itama karisawa tayi kusansu saidai sabaninsu itah fuskarta babu alamar nuna wani reaction a ciki, "Menene yah faru na ganku da ranar nana haka?" "Shugaba alkhairi ne amma ga surayyah nan zaku shiga ciki tayi miki bayani,nizan je wani wajene idan na dawo zan maida ta gidan" Kallon surayyah tayi tareda cewa, "Ke Har yanzu kina yawon banzar koh baki dainaba,ba na gargadeki da bawa kowa lokacinki a araha ba,koh baki karanta takardar agreement din mu ba" "Ahah shugaba wallahi na karanta,kuma ba na bin kowa yawo yanzu,kawai wannan din wanj abune daban kuma zanyi miki bayani" Daga kai tayi kawai alamar taji kafin ta maida hankalinta kan burgu, "Kai kumaa dama dazu nake shirin kiranka akN batun taron daza'ayi na senatoci ran Monday,ku tabbatar kun shiryah wajen kulada zirga zirgar mutane da cike hanya saboda kae a samu matsala" "Shikenan zan samesu muyi maganar" Sauka surayyah tayi daga kan mashin din tana kallon sameemah da idanuwanta so innocent kaman ba itah bace mai filllah rashin mutunci,itama sameemah kallonta tayi sau daya tareda zuyawa cikin gidan. Ganin ta tafine yasa surayyah sake kallon burgu da alamar tambayar tabi ta kuma ta tsayah, "Ki bi

Table of Contents

Chapters

55 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});