Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 16

Chapter 16

Gidan Gandu Book 1 Complete Hausa Novel 1,280 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Murmushin tayi masa irin na muguntar nan kafin tace, "Karka damu mucigaba daga inda muka tsaya a maganarmu,wannan hukuncin tab'a jikina dakayine na maka" "Yanzu menene sunan abinda kikamin ina nemanki da arziki kina nemana da tsiya?" "Yawwa gwanda da kace kana nemana da arziki ai haka nakeso Alhaji,kai ne shugaban kungiyar vigilantee na garinnan koh?" "Eh nine amma bazan had'aki dasuba ai" "Oh kana nufin cewa zanyi karka saka su su kamani?,lallai baka sanniba ina ga so kake na k'ara maka wani marin" "Ahah kiyi hakuri na tuba ki yafeni" "Kai Dallah ni kadaina wani rokona haka,sai kace wani sarki da bafade,so na ke shugaban kungiyar ka d'orani akai,zan baka nan da wata d'ayah daga nan bazan k'ara koh kwana d'aya ba,sannan yarana ma zan nad'aasu mufara aiki tare,dan garinnan yana bukatar gyara sosai,kuma na duba naga babu mai gyarashi sai ni nan jar wuyah" Watstsakewa yayi daga marin da tayi masa yah yah gyara zama kafin yace, "Lallai na yarda ke yarinya ce,yanzu marin dakika yimin ne kike tunanin zai sa na sauke yarona dayake kan shugaban kungiya na baki,kinsan irin wuyar dana sha kafin na kafa wannan kungiyar zuwa yanzu,lallai da sauran ki" "Babu saurana alhaji kungiya kuma dole saika bani idan kuma ba hakaba zaka ga aikin yarinta kaman yanda kafad'a" Tana gama fadar hakan ta matsa wajen television dinsa tah ciro wata y'ar karamar camera wanda duk nacin mutum bazai san da ita ba inba yasan sanda aka saka ba. Zuwa tayi gaban alhaji bala tah tsugunna, "Nasan kasan menene wannan ba sai nayi maka karin bayani ba ,kuma kasan wacece hajiyah kulu,(matarsa) dakuma wannan saurayin umaruje(babban d'ansa wanda yake karatu a UK),toh cikin minti talatin sakon dayake cikin nan zaije ga kunnensu ,sannan bayan sun gama ji sun more,saikuma mutanene garinnan suma su shaida wanene alhaji bala,ko ban tuna maka ba ,kasan wane irin fad'e fad'e kayi a dakinnan koh?,toh maza saka hannu a cikin takardar nan" Tafad'a tana mika masa wata takarda,tsilli tsilli yayi da ido,ganin irin ruwan daya d'ebowa Kansas babu damar kuma fita daga ciki. Mika hannu yayi yah karb'i takardar hannunta amma daga nan ko motsi bai sake yi ba kaman wanda aka sankare shi. "Oh Ashe ban baka biro ba,bari nabaka" Tafad'a tana mika masa biro,ya dad'e kafin yah karbi biron yah fara rubutawa kaman mai koyon rubutun, Yana gamawa yah mika mata takarda fuskarsa d'auke da dana sani,fisgewa tayi tareda sake dubawa, "Yawwa yaron kirki ashe kana jin warning,yanzu kuma saikayi shirye-shiryen d'orani saboda jama'ar gari su shaida,ko baka jiba?" "Eh naji" "Yawwa mutumina,ashe kasan abinda kakeyi,kuma yawwa bari na fadamaka,motar da aka kawoni d'azu gaskiya akwai dadi,kuma ta birgeni,dan haka da itah zan tafi ina sonta" Alhaji bala bai san sanda hawayen takaici yah zubo masa a fuska,saboda tsabar irin fashin da sameemah tayi masa tunda yake a duniyah ba'a taba yimasa ba,ga kuma babu damar yayi magana. Itah kuwa gogar key d'in motar ta d'auka akan kujera a palour,tah fita tana kakkad'ashi tana fed'uwa har ta bawa motar wuta tayi gaba abinda kaman babu abinda ta aikata. Bayan fitar sameemah Alhaji bala ya dade a zaune bai motsaba ,can kuma yah kokarta yah tashi yana tafe yana had'a hanya gakuma rashin arzikin da sameemah tayi masa. Itah kuwa gogar daga wajen gidan shakatawa ta wuce(club)inda kowane d'an iska yake baje nasa bidirin. Tun a hanyah tah fad'awa su burgu akan su sameta acan,da murnar su suka isa wajen kuwa dan sunsan baza'a tashi banzaba. A tare suka iso wajen su da itah,saidai sai waigawa suke koh zasu ganta amma babu wanda yah hangota,ita kuwa a nata bangaren tana kallon su daga cikin motar da take zaune,saida taga alamar bazasu gantaba kafin tah bud'e motar tah fito,da mamaki suke kallonta bakinsu a bud'e,burgu ne yayi karfin halin cewa, "Shugaba jar wuyah wannan motarfah daga ina kika samotah,ta wayeh haka?" "Tawa ce" Daga nan bata sake cewa komaiba sai wucewa da tayi cikin club d'in suma suka bita a baya. Shirya musu table akayi ita da yaranta kafin aka tambayi order,kowa shiru yayi yana jiran shugabar ta fad'i abinda takeso,d'aga yatsunta tayi sama tai kyass dasu kafin tace, "Ki kawomin ruwa mai sanyi kawai,su kuma kowa ki kawo masa abinda ransa yake so" "Sai ogahhhh suka fad'a cikin jin dad'i" Kafin kowa yah fadi wane irin kayan maye yakeso. Bayan an kawone kowa yah fara hawa caji,kafin sameemah ta kallesu d'aya bayna d'aya tana wani linshe ido kaman wanda akewa tausa,ajiye kofin ruwan sanyin tayi kafin tace, "Kusha iyah shanku,daga yau duk kun daina shaye shaye" Kallonta sukayi a zabure cike da Mamakin abinda ta ce, "Eh Ai nasan kunjini,shaye shaye is enough from now,do you hear me" "Kowa kallonta yayi kamar ba itah ba,jin yanda take turanci kaman wata yar gidan mongopark, "Daga yau duk gyaraku zanyi na d'ora ku a hanyar gaskiya,saboda iyayenku basa son abinda kukeyi,kuma nayi tunanin dan inaso nayi iskancina bai kamata nasaka ku acikiba,bayan wannan shaye shayen dakuke zai iyah tab'a hankalinku dan na kula ni kuke biyewa bayan nidaku ba d'ayah bane. Saboda haka wani watan zan zama shugabar kungiyar vigilantee na garinan,dukkan ku zan d'aukeku aiki,saidai bazan hana kowa yin muguntar daya ga dama na,amma shaye shaye na hanaku daga yau,ni kadai zan dungayi banda ku,saboda zai iyah yimuku illah. Dan haka kowa yaje yah shirya kafin zuwa nan da wani watan,zaku tayani fara aikin rashin mutunci a garinnan,dan nakula kowa yah rainani,tun daga kan yan gidanmu har kan yan gari saina saita su na gyarawa kowa zamansa. Da fari sun ji babu dad'i data hanasu shaye shaye,amma daga baya da sukaji zasu sami aikin vigilantee kuma kowa zai yi tsiyarsa yanda yaga dama ba mai hanashi,ai suka fara ihu,kowa yana tunanin wace irin mugunta zai shuka a garin saboda ya kafa tarihi.(Allah dai yah kaimu lokacin) Suna cikin ihunsu ne,itakuma sameemah tana zaune kaman wata mai hankali tana jinsu,wasu y'an matane suka zo wajen table dinnasu guda biyu,sunyi shiga irin ta bariki amma daga ganinsu kasan bakaraman gogaggu bane a harka tsiyah,wani rausaya sukayi tareda sauke muryah kafin sukace, "Uhm idan bazaki damuba seemah jar wuyah muna san muyi magana dake" "Ku fad'i miye ina jinku" "Am da mundan fita waje saboda yanayin hayaniyar wajennan da kuma gamu a gaban maza,sannan maganar mai muhimmanci ce" Har su burgu sun hayyak'o zasu fara masifa ,sameemah tah dakatar dasu tareda cewa, "Ahah ban as on hayaniyah,ku kuma ina kukeson muje muyi maganar?" "Akwai wani lungu ta bayan gurinnan inaga muje can,saboda nan babu kowa" Burgune ya hararesu kafin yace, "Gaskiya shugaba bai kamata ki bisu ba ,ni kawai daga ganinsi naji ban yadda dasuba gaskiya" "Kai ne gaba dani koh nice shugaba?" "Kece shugaba" "Toh bance kasake shiga maganar nan ba,sannan kar kowa yah biyoni ku gama abinda kuke ku tafi gidanku" Tana gama fadin hakan ta tashi ta bi bayan matan suka bar wajen. Saida sukayi tafiya mai nisa amma babu wanda yah ce komai daga itah harsu,dan a yanzu sun bar wajen hasken club d'in sun fara shiga cikin duhu,tsayawa tayi tana karemusu kallo,yayinda suma itah suke kallon ganin ta tsayah,murmushi tayi tareda kama kunkumi ta gyara tsayuwarta, "Wai har yanzu bamu iso gun wanda suka aiko kun ba,koh

Table of Contents

Chapters

55 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});