Chapter 52
Chapter 52
kayi mugani,amma daga kai har amarayar zaku san kun tabo hajiyha mairo hmmmmmm". Alhaji bala yana ficewa ta daga wayah ta fara dannawa babu ruwanta da yanayin daren da gari yah fara. "Hello hajiyah Lailah kina jina" "Eh ina jinki hajiyah mairo,amma lafiyah kika kirani da tsohon darennan ?dan ma nayi sa'a mai gidan baya nan yana dakin shegiyar" "Hmm kedai bari kawai,dama kina fadamin halin maza nake cemiki alhaji bala dabanne,toh yanzu kam na gano halimsu duk dayane tamkar an cakudasu an raba su" "Wai meyah farune hajiyah mairo ki kaini ganuwa mana" "Alhaji ne fah wai zai kara aure nan da wata daya,ke inda irin nakine ma da sauki a auro maka wanda bata wuce sa'arka ba ta yanda babu abinda zata nuna maka,amma bakin cikin shine budurwa zai auromin mai jini a jika koh yusrah bata kai na a haife,ina so ki fadamin abinda za'ayi dan bazan zauna haka ba kam" Ashar hajiyha lailah ta durah kafin tace, "Ai bazai yiyuba kam dolene ayi wani abun,kinga irinta koh dama ina fadamiki ai kike wani yabashi gashinana ya zefar miki zani a kasuwa" D'urum manjo yah buga kofar dakinsu shida kulu yah shiga ,kallonsa takeyi tareda tambayar lafiyah,bai cemata komai ba sai maida kofar dayayi yah rude idonsa yayi jawur da shi dan bakin ciki. Zare wani tsohon belt a kungunsa yafarayi,yana wani kakkadashi tareda nufar gunda kulu take tsaye a dakin. *+______________________+* *ABIN YABO BOOKSHOP* Kasuwar Rimi Kano Tel:📞 *07038339244* ❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤ Kar ku manta da #comment #share #like #follow. ____** *GIDAN GANDU* **____ ❤❤By sadi-sakhana❤❤ Wattpad username:SAKHNA03 ❤36❤ Matsawa takeyi da baya yana nufarta,bata amkara ba sai jin duka taji a jikinta zuwattt,ihu ta saka tana soshe soshe,tareda da dadare, "Dan ubanki saboda kin maidani mutum mutumi wawa soko,shine wato inacan na tafi rani kike zagewa wajen kwartonki koh,toh yau allah ya toni asirinki naji komai,kuma mai rabani dake sai Allah" Kulu tanajin abinda yafada tah daina ihun tareda tike belt din dayake dukan ta dashi da hannunta, "Ohh dama akan hakane kake dukana,toh bari kaji na fadamaka dama tun ranar dana gane cewa wani yasam abinda yah faru na shiryah wa zuwan hakan,wato sameemah ceh tah fada maka koh,dama nasan sai ta fada ai kuma ......" "Dallah rufemin baki munafuka,toh ba sameemah bace ta fadamin a unguwarku naji wasu suna fada,ai dama abin duniya baya buya indai anyishi" "Eh nasan na aikata amma sau dayah nayi kuma daga lokacin ban sake ba,shima kansa na yi masa gargadin kar ya sake kirana tun rananr,kuma koma mai yah faru ai lefinka ne,naga tun ina da cikin mai sunan baba ka tafi ka barni,bakasan halinda nake cikiba har na haifeshi na yayeshi yayi wayo baka nan,sannan daka dawo babu abinda ka bani bakasan mai muka ci ba bare kuma muka saka,komai ma a lokacin ne yah faru,ai nayi kokarima da ban tafi gidanmi na,shidinma jugani yayi akan bazaka dawoba,na kashe aurena na aureshi,nayi nadama nace yadaina kulani" Zuwa yanzu kuka takeyi amma bana dukan da manjo yayi mata ba,na halin dasuke ciki takeyi,durkusawa tayi akan gwiwarta tareda cewa, "Duk da nasan banda mutunci a idonka,saidai ina kwadayin muyi zama irin na ma'aurata na gari badan muba saidan yayanmu,banida ilimi na arabi dana boko haka kaima duk dayane dani,sannan dagani har kai munsan hanyar da muke kai bamai kyau bace,mai zai hana mu gyara,ko makarantar yaki da jahilci mushiga domin musamu ilimin bawa y'ay'an mu tarbiyyah,ni dama ina zuwa wajen matar kawu munkaila tana doramum,rayuwarsu tana burgeni,sannan har yanzu manjo ina sonka wallahi,soyayyar ka ita tasa na kasa kashe aurena na bishi badan wai dan ina tsoron Allah ba a lokacin. Dan allah kadaina shaye shayennan sannan karka sake zuwa cirani dinnan da bashida amfani,ka zauna tareda damu iyalanka mugina rayuwa mai kyau tun kafim lokaci ya kure" Tana gunjin kuka tana fada iyah karfinta,matsawa tayi tah kamo rigarsa da hannunta ta rike gam kaman wanda zai fita yah barta. Shima ganin hakanne yasa ya jefar da belt din tareda tsugunnawa yana rungumeta a jikinsa, "Shikenan kuluna na yafemiki kuma na fahimceki,nima inso ki yafemin,hakika laifinane kam babbba a ciki,inshaallah zan gyara halayya tah,amma ina ga zanje wajen mai gidana nace masa na yarda zan je Kazaure na rike masa aikin bulonsa nacan,inyaso sai mu tafi daku gabadaya na kama mana haya na sakasu a makaranta,dan wannan wajen zayyi wuyar sanja mutum zuwa na gari koda kuwa yayi niyyah" Kara rungumeshi tayi cike da jin dadi,jim abinda manjon yace ,kuma cikin muryah irin ta mutum mai hankali,fito da kudin dake cikin aljihunsa yayi wanda yake tunanin zuwa siyan kwayah dasu yah mika mata tareda cewa, "Ka wannan ki sayi abinda babu kiyi abincin rana,kuyi hakuri da rashin ciyarwar dana yi muku a baya" Da farinciki ta karbi kudin tana yimasa godiyah da kuma fatan neman budin allah. "Yanzu inna haka za'a kawashe duk wannan ubam kayan kayan akaimata,wanda akayi shekara ana tarawa,saikace wata diyar sarki,naga ko mu ma akwati daya aka kawomana shine ita sai ankaimata har akwati uku,gaskiyah bazai yiyu ba" Sahura ce take fada yayar Yunusa saurayin zainab,Iyah Larabace mamar su yunusa wadda aka kira da inna itama tace, "Kema dai kya fada y'ar nan(bata fadan sunan tah na farine)sai wani rawar kafa yakeyi akanta,duk wani dan kudinsa yah kashe a kanta tun kafin tazo,ni wannan tun kafin tazoma na fara zargim inaga farar kaface da itah" Wata ce a gefe tah jijjiga kai ,saboda kaff garin babu wanda bai san inna laraba da kishi da matan y'ay'an ta ba,ga masifa da kuma saka ido,kuma su kansu yaranta mata halinta suka gado a jaraba. Kanwar inna larabance tace, "Gaskiya yaya karkiyi haka,wannan ai sai aji kunyah,ki bari koma menene idan tazo ai sai ayi koh amma ba a nan ba gaskiyah" Dahaka badan tasoba ta bari amma bahakan yana nufin tana son akai kayanba. Tun kafin yamma gidan gandu yah fara cika kasancewar za'a kawo kayan yan mata har guda biyu ,na salma kuma sai gobe. Inna ramatu sai shiga ake ana fita saboda hidimar tarar baki.kasancewar al'adarsu da yamma ake kawowa shiyasa mutanen dazasu karbi kaya daga bangaren amare har sunzo. Guda aka fara rangadawa tun daga zaure saboda masu kawo kayan zainab sun iso,kowa sai san barka yake sakawa ganin akwatinan ta har guda uku. Wata kawar zainab dince wacce suke zaune a dakinsu tace, "Gaskiya zeeey kinyi farin jini a wajen yunusa kuma yana sonki,ji fah har akwati guda uku aka mikk" "Hmm dama an fadamiki so dan karami yake min ai komai yah mallaka ma zai iyah kashemin ga ............." Katsewa tayi da maganar suka leka waje da gudu jin wata gudar wanda tafi tah farko, Zare ido sukayi ganin yanda aka kawo akwati har guda shida kuma ainihin designer. "Kutt wannan duk kayan sameerah ne,tabb to a aiko a auren farko bata samu rabin na zainab ba ma,amma ji akwatinan ta" Ihu da tsllen sameerah suka jiyo a bayansu da alama itama ta ga kayan da aka kawo gidannasu a matsayin nata. Haka aka gama hidimar kawowa kayan aka gama kowa yah watse. Ita kuwa sameemah dama ba ta gidan bare tasan mai akeyi dan da gangan tah tsiri aikin patrol na dare a hanyar masu cin kasuwa dan kawai kar tah dawo
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55