Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 7

Chapter 7

Gidan Gandu Book 1 Complete Hausa Novel 1,251 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

nufi da cewa muyi wacce zamuyi ,toh ni ba wajenki nazo ba ,wurin yar dabar gidannan nazo da ta lahantamin d'a yana nan a kwance kaman bazaiyi raiba" "Ayyyirirri koma wa kike nufi tamin dadai duk da bashi zai hana na fasa abinda nayi niyyah ba" "Kehh duk abinda yafaruma larai ki bari sai daga baya yanzu ba wajenki nazoba" "Ohh kina nufin bakiji abinda dannaki la'ananne ya aikata ba,koda yake bazakijiba saboda ba y'arki yayiwa ba,yanzu dayake shi akayiwa aika aika aikin ji har kinzo neman ba'asin labarin. Toh in ma baki sani ba kisani danki labiru y'ata hanifa ya farkata,kaman yasami fanko saboda tsabar tashanci kuma yayi gado,toh bazan yadda ba,yanzu dakike cewa yana jinya toh yana warkewa zan bawa gardawa sadaka su sake maidashi kwance,dan jinin y'ata billahillazi bazai tafi a banza ba" "Ke wai dankinga nayi shiru ina jiran ki fadi abinda yake bakinki,aikin banza saboda gadon kwadayi yasa ina kuke lik'a masa ita,dama aka ce ai k'uda wajen kwadayi akan mutu,kuma dazakice wai gado dan ma abin kunyar kowa yana da shi a gidansu ,ko kin manta tsoho wanda baya saka wando sai babbar riga kawai saboda bin bazawaran kauye" Hayaniyar ce tafara yawa inda matan kofa ko wacce take lekowa dan kashe kwarkwatar idon ta. Da abin yayi yawa fad'ane ya rukume tsakanin salame da larai kowa yana tsinewa kowa albarka kaman wasu zakaru. Saida mazajen suka fito kafin aka samu aka rabasu dakyar kowa tana huci kaman shanu. "Kai kai mai yafarune haka,mu gidannan babu dama mu tashi a ji shru kaman kowane gidan saidai Koyaushe da masifar dazata kunno kai" Kawu KAMILUNE,mai magana yah fito zai tafi gona,dama shi bai fiye zama a gidanba kl yaushe yana wajen neman kidinsa,matansa ma yahanasu shiga duk wata cakwakiyah da ake a gidan indan yakama wata kuwa da hannunta a ciki toh saidai ta nemi wani gidan badai nasa ba. Jin muryarsane yasasu salame tsayawa fad'an sauran matan kuma kowa ta koma gefe ta kasa kunne dan taji mai za'a ce,dadai lokacin ne kawu shehu shida baba umaru suma suka shigo daga wajen mai shayi da alama wani yaronne yaje ya kirasu, "Wannan yar rainin hankalince mana,dan tsabar su dangin marasa kunyane duk abinda danta yayi bai isheta ba hada zuwa tana wani kumfar baki wai an illah ta mata d'a a gidannan,kuma illatawa bata ga komai ba ma saina tashi yanke nawa hukuncin ehhe" "Hukunci kin dade baki dau hukuncin ba abinda akayi masa ma na yanzu ba shiru zanyi ba barekuma kiyi tunanin daukar wani matakin" "Kai ya ishemu haka wannan yarintar,kun girma ku ba yara bane amma baku da maraba da yaran kuma abin kunyar ma a gaban yaranku kuke wannan abun,ke salame mai akayiwa dannaki kikazo tada fitina da safennan" Baba umaru ne yadaka musu tsawar cikin bacin rai da kuma k'osawa da halinnasu na yau da kullum, Jin an tambayeta ne yasata fashewa da kuka tana shareewa da gefen zaninta kafin tace, "Dan tsabar rashin imani bakuga aika aikar da akayi masa ba,tun daga kasan cibiyasa har zuwa rabin cinyoyinsa an konesu da man gyada mai zafi,babu komai sai fatarsa a waje kawai,kuma anfadamin wani marar imaninne a cikin gidannan yayi masa dan haka bazan yadda ba wannan ai niyyar kisan kai akayi ,yanacan katon saurayi a kwance sai abinda akayi masa tukunna" "Allah ya kara baiga komai ba ma,in duninsa halin bunsuru" Larai ce tayi sauri ta fada tareda d'ane baki kaman ba itah ce ta fad'a ba, "Keh larai banason shiririta ana kwantar da wuta kina kara mata fetur koh?" Baba umaru yana rufe baki kawu shehu yadora da cewa , "Laifinta Toh kagani yayan umaru,bayan abinda dannata yayiwa yar mutane kuma taxo tana fadan wai wani yah nakasa mata shi,ina ruwanmu toh,in zatayi hakuri tayi in kuma bazatayi ba ta kai kara ,muma saimu kao karar in yaso ayi ta shar'ar tunda ita take so ayi tayi, "Ahah baza a kai har haka ba,ke salame tunda kinji mai danki yayi sai kije gida kiyi jinyarsa tunda kinga suma jinyar tasu yar suke,kowa sai yayi hakuri yaran zamanine sai hakuri ka haifesu baka haifi halinsu ba,muma kuma iyayen da na mu laifin ta wani wajen ,allah dai kawai yah shiryamu gabaki daya" Dakyar su kawu kamilu suka kwantar da fitinar salame ta tafi gidanta tana kanana nan maganganu wanda allah ne kadai yasan ranar dazata bari. Sameemah kuwa duk abinda akayi a gidan bata sani ba,saida wayarta tayi Ring ne kafin ta juya ta kalli screen din ,tareda tsuka saboda tashinta a bacci saboda tasaka wayar a kusa da kunnenta, "Alhaji bala" Shine sunan da ta fad'a cikin muryar bacci kasa kasa.......... ❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤ Kar ku manta da #comment #share #like #follow. ____** *GIDAN GANDU* **____ ❤❤By sadi-sakhana❤❤ Wattpad username:SAKHNA03 ❤06❤ "Heelloo alhaji bala yah hidima?" Seemah ta fada cikin muryar barci,wani irin mika alhaji bala yayi jin yanda ta amsa masa cikin sanyin muryah kaman ba sameemah daya saniba, "Lafiyah kalau madam yah hutu da jin dadi" "Lafiyah kalau,wani abune yah faru?" "Ahah babu abinda yah faru gimbiya kawai na kira ne naji lafiyar ki,sannan kuma na sanar dake inkin shirya ko yaushene to kiyi min magana zan aiko mota har kofar gidanku a dauke ,kizo mushakata muji dadin mu,saidai ina rokonki dan allah naji kiran shiryawarki da wuri,dan baki san yanda nake jinki a cikin zuciyah ta bane,akanki babu abinda bazan iyah ba,kawai hadin kanki nake bukata shine kawai cikar burina" Saida ta tabe baki tukunna tace, "Naji alhaji yanzu ina kwance banason a takuramin ka bari idan na tashi nayi tunani zaka ji mai na yanke ,kuma karka sake kirana sai na nemeka tukunna" "An gama gimbiya,ai duk abinda kikace shi za'ayi kawai" Sauke wayar tayi kafin ta kara danna wani kiran,ring daya aka dauka a d'aya bangaren, "Allah yah taimaki shugaba me kike da bukata" "Kai C.I.D(dan leken asiri),ka saurareni da kyau" "Ina jinki" "Ina son duk wani bayanai akan alhaji bala wanda muka hadu dashi a gidan alhaji Sama'ila,tun daga kan iyalansa sana'arsa har zuwa kan karfin siyasarsa,in takama inason bayani kaf akan gidan shata warsa,ka kawomin nan da bayan azahar,sannan kuma akwai abinda zakamin bayan hakan" "Wannan mai saukine an gama shugaba" Ta shi tayi daga kan gadon kafin tah zuba wata uwar feduwa wanda in kana bakin kofar tasu saika jiyota, Wasu manyan karnukane guda uku suka shigo dakin suna karkada jelah,suna sakin yawu a bakinsu kaman zasuci babu. Sameerah ceh wanda take kwance tah buga uwar tsuka tareda cewa, "Aikin banza wai dan tsabar rashin mutunci kare har dakin mutane,su gasu abu kamar kuraye dan muni wannan ai walakancin yayi yawa" "Kehh reza yaga mata kayan jinkinta yanzunnan sannan kiyi mata balli balli a cinya" AI kuwa kaman jira farar karyar take tayi kan sameerah da sauri tana gyara baki,wani uban ihu sameerah ta buga cikin kankanin lokaci sai gata a waje,dakin uwarta ta nufah tana ihu tareda neman taimako. Dakin inna ramatun ta shige tareda rufo kofah tana rafza ihu a ciki. Mutanen gidanne hankalinsu yadawo kan abinda ake,dama kowa yana tsaye bayan an yi hayaniya tsakanin salame da larai, "Wayyo baba umaru ku taimakeni kuna ganin zasu cinyeni da raina wayyyo inna" Kowa yana jin ihun sameerah ga karnuka

Table of Contents

Chapters

55 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});