Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 1

Chapter 1

Gidan Gandu Book 1 Complete Hausa Novel 1,283 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

____***GIDAN GANDU***____ ❤❤By sadi-sakhana❤❤ Wattpad username:SAKHNA03 ** ❤ Gargadi❤** Wannan littafin kirkirarrene,saidai zai iya cin karo da dabi'un wani ko halayyar wata,sannan ba a yarda wani ko wata suyi koyi da mugayen halayyar Wannan littafinba,anyine dan isar da wani sako. Sannan game da marubuta idan kinga wani abu yayi kama da littafinki toh yanayin tunanine yakawo hakan,dan banida niyyar bata wa kowa rai,burina isar da sakon da littafin ya kunsa,wanda in akayi hakurin bani hadin kai har zuwa karshe toh kowa zai ga mai littafin ya kunsa. ❤Jinjina❤ Babbar jinjina ga proficient writer association,Ina godiya matuka. ❤01❤ ..................Gidan gandu,gidane daya kunshi mutane fiye da 300 a muhalli daya banda wanda sukayi aure wasu suka tafi cirani wasu kuma tantirancin su ya hanasu zaman gida,tunda ga baki kofar gidan mutum yasan wane irin gidane saboda yawan kofofinsa tun daga kan kakanni,iyaye,jikoki,tattaba kunne da saurensu. ***** ****** ****** ______lokacin safiyace dan baifi 9:30am na safenba,gidaje a kowa yana kokarin aikin gabansa inda masu himma kam yayansu sun dade da tafiya makaranta,maza kuwa wasu sun tafi gona. Shiru cikin gidan kakeji babu wata hayaniya kowa yatafi harkarsa,bayan yasamu abinda ya sawwaka ya zuba a cikinsa,sai iya kofar kawu shehu wanda dama su kullum cikin fada suke,da inna larai da kuma inna karima.Dakin yan matan gidan ma bakowa sai wata matashiyar budurwa a kwance tana zuba bacci kaman ba gobe,ta dade batayi motsiba can kuma sai ta yi wata mika irin ta wanda ya more da baccinnan,gyara zamanta tayi a bakin katifar tata tana bubbuga kai da kuma jan majina da irin kaman mutum ya shaki kura, "Kai shiyasa dadina da BURGU yasan DULAH (wiwi),mai kyau yanzu mutum zaiji shi a caji,duk wata gajiyarka saikaji ta tafi,inda ana samun mai kyau haka yaushe mutum zaice yayi asarar kudinsa kuma ai............" Katsewa tayi da zancen nata jin wayar ta irin yan nokia dinnan ta dau kara ta cika dakin,juyawa tayi tana yatsina fuska ta dauki wayar kafin ta saka a kunnenta, "Menene??" Shine abinda tace tana daga kiran,sai kuma tayi shiru danjin maganar da ake a daya bangaren, "Hmm indai kaji kira a wajen alhaji sama'ila toh siyasah ce ta kariso yana so ayi masa aiki,toh wallahi kaji na fadamaka inhar ya hau kujerar nan yamanta da mu,to sai yayi dayasanin sanina a cikin rayuwarsa,dan saina masa abinda har ya mutu bazai mantaba,kuma kasan zan aikata,dan haka yanzu ka fada masa,inya amince kazo kadaukeni mutafi a san abin yi,yanzu dama nake maganar ka dan naji dadin dular jiyannan akwai caji baaaba,............shikenan kazo ka daukeni sannan kace arnan yara su shirya ganinan zuwa yanzunnan" Fitowa tayi a dakin tana wani garwaya hanya irin na iya shegennan can kuma sai ta dauki bokati dama da ruwa aciki da alama wani ne ya ajiye, "Keee SAMEEMAH ruwa na ne na ajiye" Juyawa tayi tana kallon mai maganar cikin daga ido, "Toh so what dan nakine,ajiyewa zanyi dan naki ne,inkuma kinga a tawani sako na kwakwaiwarki ya nuna miki ina tsoronki ta kizo ki karba,kin manta ina da labarin guntun sabuluna da kikayi wanka dashi?koh an gaya miki bansaniba,dan dai munayin hankali ne kullum shiyasa muke barin koh ta kwana" "Iyyyeee Ku zo ku jimin wata magana wai sameemah ceh tayi hankali,da kuwa anyi ruwan farin ciki a garinnan,kuma narantse kika shiga wanka da ruwannan saina miki abinda yafi na ruwana,dannima inada wajen zuwa da safennan" "Keh sameerah ya isheki haka,maida min maganar inbaso kike daga ke har mazinacin bazawarinnaki dazaki wajen sa na juya rayuwarku ba,kuma inkin fasa daukar matakin banza shashasha" "Kai lallai ma yarinyar nan,a haifeki a gaban mutane amma ki dunga yiwa mutum maganar da uwarsa bata isa yimasa ,shegiya yar daba kawai" "Hhhhhhh gwanda dakika fadi abinda yake bakinki amma bari na fito nasameki a cikin gidannan yau wallahi mai rabani da ke koh..............hmmm" Sauri sameerah tayi tabar wajen dan yanda taga ran sameemah yabaci ba abinda bazata iya mata ba ,na rashin mutunci,takaicinta daya ma,yarinya karama ta takura musu ta addabesu,gashi sunyi waya da bazawarinta Saminu,yace zaizo yadauketa su tafi bikin abokinsa a Kaduna tana ta murna,yanzu tasan dole saidai ta tafi ba wanka, saboda gudun haduwarsu da sameemah a yau,dan tasan in ba hucewa tayiba,tsab zata aikata abinda tace. Bata dade ba a bandakin ta fito,har yanzu fuskar ta ba fara'a saboda sabanin dasukayi da yayarta sameerah dazu wanda suke uba daya su da itah,dakinnasu ta shige ta nufi hanyar wajen kayanta,dan daki kawai suka hada da yan matan gidan amma kowa shirginsa daban ,gwanda su wani lokacin in wata tayi samuwa ana zama a ci ana dariya da yada zance,amma sameemah in ta shigo da abu a gabansu zata cinye in ya isheta ta bawa karanta BINGO. Mayuka ta fitar lotion masu gyara fata ta mulke jikinta kafin ta dauko wasu kaya na saki irin na farauta amma anyi musu dikin irin na mata riga da wando. Bayan ta gama saka kayanne kuma aka shafa hoda kafin aka dauko bakin jambaki wuluk ta shafe karamin bakinta dashi ,ga kuma kwalli da tayi masa saku kasa da sama,dan saida girar ta kusa hadewa da saman ido,juyi tayi a gaban madubinta kafin ta dauki gyalen ta nadeshi a kafada ta fito daga dakin. A bakin hanyar fitarta daga dakin suka ci karo da wani dan anguwarsu yana rataye da yar gidan inna larai a kafadarsa,yarinyar sai kuka take bazata wuce shekara bakwai ba,Sameemah ce ta fara ganinsa tareda Tambayar "lafiya" "Ahah seemah jar wuyah(haka kowa ke kiran sameemah a waje)wallahi a hanyar shagon ilu naganta a kwance jini yana binta hine dana tambayeta tacemin wai Labiru ne abokin yayanta Manu yayi mata haka" "Ayyah Toh sannunka da kokari zaka iyah tafiya" Bayan ya tafine sameemah ta dauki yarinyar tayi kofar su inna larai din da ita, "Inna larai! inna larai!! Inna larai!!!" Suna cikin habaici kowa yana kofar dakinsa ita da inna karima,sai ta zuyo tareda cewa, "Ke miyene kike ta jundumamin kira kaman zaki cinyeni" "Iyyeh hakanee abin(sameemah ta fada tana ajiye hanifan a gababan inna larai) toh gashinan,yar tatsitsiyar yar kice wani gardin ya fardeta ,kona ce yabudeta a ledarta,saiki zo ki dundumata da ruwan zafi ba masifa zaki tsaya yiba,itama alamu kwadayinnata ya kaita ta shiga sahu tun lokacin ta ba yiba" "Lallai sameemah abinda zakice ma kenan,wanne dan tsinanniyar ne wannan?" "Waye kuwa banda Labiru abokin danki Manu,bake kike manna masa itaba dan kinga yana siya mata shayi da safe,bakuda aiki sai kwadayin tsiya,saiki dundumata ta samu ta ware,ko tayi harkar da kwarin jiki,ni na tafi inna dawo da kaza na dan bata,kota maida jinin da yazuba,in kuma nima bandawo ba tacan tacan,ga wannan kisaya mata ibrofen saboda zafin jiki(tafada tana mikawa inna larai din naira hamsin). Wani wawan tsalle inna larai din tayi tareda buge kudin dayake hannun sameemah,kafin tabita da wani ashar mai dumi. Inna karima kuwa tana gefe tana zuba uwar dariya kamar makogaranta zai fito dan mugunta,komawa kanta zagin yayi,cikin haushi inna larai tayi kanta suka rukume da fada,tana zaginta tana kururuwa kan gari ya gari. Ganin mutanen gidan sun fara sanin abinda yafarune,yasa sameemah zagewa ta fice daga gidan. Tana fita ta samu Burgu a kan mashin yana jiranta,burgu yana ganin ta fito ya tada mashindin yafara diri,dalewa tayi suka fara tafiya,yana bata labarin

Table of Contents

Chapters

55 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});