Chapter 19
Chapter 19
nayi na kalli bongon d'akin ina nuna musu k'eyah,dan gaskiya yah sameer din yah takuramin magana ce kawai banyiba. Tun daga lokacin zama kusada ummah yakemin wuyah saboda Koyaushe yah sameer yana makale da itah,gashi yanzu babu damar tah koreshi ta kirani saboda yanzu babu abinda takeyi da kanta,sai sameer din yayi mata,nikuwa bana shigowa dakin sai kwanciyah ko kuma zuwa neman abinci,duk sanda na je dakin sai ummah tasaka min albarka tareda yimin kashedin zaman duniyah,duk da ina ji amma babu damar aiki dashi a lokacin saboda yarintata nakeci a lokacin babu babbaka. Bayan wata d'ayah da kwanciyah jinyarta mai tsanani,sai yazamana ciwon dayake kafarta yah fara shiga har cikin jikinta,tashin hankali kam babu irin wanda su baba umaru da yah sameer basu ganiba,idan kaga yah sameer a zaune yah zuba tagumi toh tunanin jinyar yakeyi. Babu yanda baba umaru baiyi da ummah ta barni na dinga kwana a dakin inna ramatu,amma haka firr taki yarda,komin halin ciwo da ta shiga tana dawowa hayyacinta zata nemeni,nikuwa yanzu tunda naga haka jikina yayi sanyi sosai,saboda nasan idan mutum yana ciwo sosai mutuwa zayyi kuma in yah mutu bazai dawo ba,har kuka nake idan naga tayi shiru ,sai yah sameer yace min bacci takeyi kafin nayi shiru,dan saina ga kaman tah mutune. Yauma a kwance nake a gefenta saina ji tana riko hannuna,tashi nayi na rike hannun tareda tambayar tah, "Ummah mai kikeso na miko miki?" "Babu komai inaso ki bani hankallin ki ne yanzu" Jijjiga kai nayi alamun ina sauraronta,Murmushi tayi irinna dauriyah kafin tace, "Inaso da farko seematu ki kasance mai hakuri,sannan duk rintsi karki watsar da ahalinki duk da sun kasance masuyin san ransu amma ki barsu watarana sai labari,ki kama mutuncinki a matsayinki na y'a mace,ban yadda kibawa wani namiji dama yah yaga mutuncinki ba,saboda kudi,wahala,koh kwadayi,idan kikayi haka bazan yafemikiba,duk wata huduba daza'a doraki a bayana ban yadda kibita ba sai yah kasance huduba mai kyau ce,in abune baki ganeba ko yah shige miki duhu ki tambayi dan uwanki kinji,sannan duk rintsi ki guji abinda za'amiki wanda zai ji miki ciwo,saboda boye yanayin halittarki daga idon mutane. Allah ya tsare ki daga sharri,yah inganta rayuwarki sannan yah yabaki miji nagari" Duk abinda take fada ina jinta saidai na gagara bata amsar komai saboda bansan mai zance ba. Yah sameer ne ya shigo shima idonsa yana hawaye da alama yaji duk abinda take fadamin,shima tana kallomsa ta rike nasa hannun tareda cewa, "Nasan kai kasan mai kake,Toh inaso kacigaba da bin hanyar dana doraka,sannan ka kulamin da rayuwar seematu domin tata rayuwar zata fi shiga hatsari fiyeda naka,karka bari wani mungun abu yah faru da itah,sai abu na karshe munyi magana da babanku,na bashi wata wassiyyah wanda nakeson yah cika min itah,koda bana duniyha wata rana yah baku wannan wasiyyar inaso ku zama masu cikata,sannan ku kasance masu min addu'a bayana,sann............nan...........uhhh ........uhh Tarine yah sarketa jini yana fitah ta bakinta,amma duk da haka tana rike da hannunsu,cikin dauriyah ta hada hannunsu waje d'ayah,kafin tace cikin nishi "Na baku amanar kanku,kar d'ayah yabar d'ayah cikin halin wahala shikadai,kuzama tsintsiyha madauri d'aya" Tana gama fadan hakan ta sau hannunsu da alama jikinta yasake,suna kallo tana fadan wani abu wanda basajin mai take cewa har kuma suka ga idonta yah rufe. Kallon yah sameer nayi ganin yanda yayi wani shuri kaman an daskareshi, "Yah sameer yanzuma ina bacci tayi koh,kace min zata tashi idan anjima,kaji yah sameer" Kallona yakeyi kawai fuskar sa da alamar tausayawa idonsa yana zubar da hawaye,batareda y ace komai ba yah rungumeni a kirjinsa,nima a sannan babu abinda nake bukata sai naji wanda zai saurari kukana,hannuna nasaka na zagaye bayansa tareda sake kankameshi,mun dad'e a haka kafin ya dago fuskata muna kallon juna,saida yah share fuskata kafin yace, "Kiyi Shiru haka,ummah batason kina kuka ,sannan muma watarana zamuje inda ta tafi ,kidaina kuka haka bari na kira su baba yanzu " Saida yaja numfashi tukun cikin yanayi na juriyah da alama yana cikin mawuyacin hali shima,jijjiga masa kai nayi ina jan majina kafin shikuma yah fita ya barni dagani sai gawar ummah nah. Tsura mata ido nayi ina ayyana abubuwa da yawa a raina,ciki harda maganar da mukayi da ita nida yah sameer mintuna kadan da suka wuce,d'aga kaina nayi ina kallon baba umaru wanda suka shigo shida yah sameer da kuma inna ramatu,wani irin ihu inna ramatu ta rantab'a tana tsugunnawa a wajen,baba umarune ya wuceta tareda zama a gaban gawar inna hajara, "Ke matace tah gari hajara mai sunan matar annabi ibrahim,kuma kema kin gado mai sunanki wajen yin biyayya ga mijikinki cikin dad'i da rashinsa,indai a lahira shedar mai mijice ke saka mata su shiga aljanna toh na shedeki matata,allah ubangiji yah yafemiki duniya da lahira sannan yayi miki rahama daga cikin rahamarsa😭😭" Saida yah kare mata kallo yana zubar da kwalla kafi yah ja mayafi yah rufe mata kanta,shiru inna ramatu tayi tana sauraransa daga ji kasan ranta bayason yanda baba umaru yake yaba halayen ummah na kirki. A zaune muke a tsakar gidan munyi zugum bayan an tafi kaita gidanta na gaskiya,har sannan zuciyata ta kasa gaskatamin cewa na rabu da ummahn tawa farincikin raina. Mutanene suke ta shigowa wasu na fita wasu na shigowa,har babu inda wasu zasu zauna. Wasu mutanene suka fara shigowa gidannamu bayan anyi kwana uku da rasuwar ummah,wanda ranar ne yakama ana sadakar uku,tun daga yanayin jikinsu mutum yasan ba y'an garinmu bane,baba umaru aka kira yazo yagansu bayan an kaisu d'akin da ummah take a da.mamaki ne ya isheni ganin yanda baba umaru yake gaisawa dasu kaman yasan su,toh yaushe yaje wajensu har yah sansu haka,oho. Sum dad'e dan saida suka kai har wajen la'asar kafin suka sauke buhun shinkafa dana sugar dakuma jarkar manja suka tafi. Mai hali baya fasawa inna ramatu tana cikin kukan munafurcinta,tana ganin wannan kaya ta share idonta tana washe hakora,(Allah yah shirya). Yanzu ummah tayi wata guda da rasuwa mutane kowa yah manta da itah inka d'auke ni da yah sameer sai kuma baba umaru,nikam ma nice wadda mutuwa tafi bankad'a saboda cin zarafi tun ba'a kai ko'inaba nafara ganinsa a cikin gidan,su kuwa si yah sameer in suka fita aikinsu sai dare nagansu,toh dama shima rashin lafiyar ummah ne yake sakawa yana shigowa gidan,Amma yanzu tunda babu itah dare yake dawowa. Dakin ummah shiya zama na yan matan gidan,kowa anyi mata shimfid'i,amma nikuwa sai dare yayi na tura kofa na kwanta a wajen,saboda duk sun saka shirginsu su Badariyyah da kuma manyan yan matan gidan irinsu hafsa,shukura,da kuma lami,dukkansu yayan kannen baban mune mata wanda sun kasa zama a gidamsu sunzo suna takura mana,saidai babu wanda zaiyi magana sai an tab'a d'ansa nikuwa wazayyi magana tunda babu tawa uwar. Tun abin baya damuna saboda yarinta yamzu har ya kai na fara ganewa,sau daya na je wajen yah sameer na fadamasa cewa ba a bani abinci na koshi,yah tsina fuska yayi yana juya kansa,da alamar na takura masa, "Kee bafa zan yadda kina takuramin ba ,dan kawai ummah tace na dunga kula,fisabilillah kina ganin dawowata kenan fah amma kina cemin wai ba'a baki abinci kin koshiba,nima kina ganin d'an kad'an suka bani amma nayi shiru nake ci haka,kiyi hakuri kawai kisha ruwa ki kwanta" Kallonsa nake da mamaki kaman
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55