Chapter 47
Chapter 47
wata yah shigo,da sauri yah duka yah gaisheta tareda mika report zai fitah,Sunan sa ta kira tareda cewa, "Am zo zaka dan yimin wani aiki mana,wannan zaka raka zuwa dakin da muka ajiye yan kamen jiyah" "Okay ma'am," "Ku bishi ku kalleshi na baku wannan alfaramar" Dan tsabar mamaki duk cikinsu babu wanda yayi magana,sai kawai tashi da sukayi domin bin wanda tace musun. KO a jikinta kuwa tah cigaba da abinda takeyi ,kaman dama dai duniya bata san suba. Bayan tafiyarsu da kusan minti talatin mutane da dama zunzo karbar yan uwansu,dan office dinnata yah cika har wasu suna tsaye,duk maganr da sukeyi bata ko dago kai bare basu amsa. Su baba umarune suma suka dawo office din bayan sunje sunga baba shehu,wanda bayansa yayi burd'i burd'i da dukan bulala,bakincikine kwance a ransu,musamman ma Manu wanda shi ubansa ne,kuma sa'anni suke da sameemah din ,buga table din yayi har saida takardun wajen suka zube, "Ke Wacce irin halitta ce wai,tum dazu muke magana amma koh amsa mana bakiyiba,wane irin laifi ubana yayi miki kika yimasa wannan hukuncin,kuma dan zabar ke baki imani kika yimasa dukan dayafi na kowa a wajen,magana nake yi nima amatsayin bansanki tunda naga dan kin sami matsayi tun ba'a je ko ina ba kin watsar da yan uwanki,sun zama sune abin farautarki,butulu kawai wanda bata san zafin iyaye da yan uwa ba" Cikin zafin nama sameemah tah zabga masa mari dama a tsaye yake a bakin table din ta,wanda hakaan yasashi hadiye sauran maganar dayake shirin amayarwa,tashi tayi ta tsaya lokaci guda tah sauyah daga kamannin da take,nuna shi takeyi da yatsa kafin tace, "Kai waye da har zakazo office dina kana fadamin magana,koh dan kaga kana dan uwana?,toh baka da wannan ikon kuma bazaka samu ba,a ganinka bansan mai nakeyi ba ne,har zaaka fadamin bansan zzafin iyaye ba kasan mai kai ubannaka yayi da kake jin zafinsa" Rintse idonta tayi tareda kokarin control din jijiyoyin dasuke kwance akan goshinta, "Ban so fada maka abinda yah faruba har da mutanen gidan ma banso su sani ba amma shiahhsiginka yasa saina fadamaka inayso duk abinda zaka ji ma kai yah shafa,...........a kwance na ganshi akan karuwa a dakinta suna aikata masha'a ,mai kake tunanin zanyi,dadi zanji kenan,iyah fadaamka danayi nasan zaka ji zafi,amma bazaikai nawa ba tunda kai kwantance zan yi maka amma ni zahiri nagani......" Tun kafin ta gama fada baba munkaila ya daga mata hannu,dan shima ba kdan ba abin ya bugeshi sosai. Jan Manu sukayi suka bar office din wanda yazama tamkar gunki,kallonta ta mayar kan sauran mutanen office din wanda yawancinsu daga wanda tazo karbar danta sai mai karbar mijinta ,wata yar ta wani kuma kanwarsa koh kuma yar yayanka da sauransu, "Ku kuma mai kuke jira da bazaku bacemin daga ni ba,babu wanda zan saki saina ganan masa azaba kaman yanda yaganawa zukatan jininsa,da kuma masu sonsa,dan tsabar baku da hankali wai su bijiremuku su tafi shashahnci amma kuzo kuna yar karamar muryah a sakesu,yaushe duniya zata cigaba a samu raguwar yan banza idan har zuciyoyi bazasu tsaya su kawar da so su hukunta masoyinsu ba. Ban yards da irin wannan son ba ni " Da sauri kowa yah fita daga office din babu sauran magana tunda aka ga yamda tayiwa dan gidansu ma,wasu suna cewa ta kyauta wasu kuma suna cewa zaluncine,amma duk da haka babu mai magana *wai an ce fadan dayafi karfinka saika mai da shi wasa*. Kaman yanda tayi alkawari kuwa saida baba shehu da sauran masu laifin suka cika kwana uku kafin ta sake su,office tace akawo mata baba shehu wanda har saida ya rame a iyah kwana ukun,rigar jikinsa duk tayi wani iri,kansa a sukunye aka shigo dashi saboda kunyar da yake ji. Wasu kaya na maza yadi ta wullah masa tareda nuna masa bandakinta na office din, "Ka Shiga nan ka yi wanka akwai ruwa sannan ka sanja kayan jikinka" Ba uhm ba uhm uhm,sanna babu musu yah dauki kayan yah shiga bandakin. Ya dan dsde da alamun gasa jikinsa kayeji kafin yah fito. Abinci tah bashi mai rai da lafiyah yah ci yah koshi,tukunna tace, "Ina fatan kaga yanda ta kasance koh?,idan har kuna cin kasa ku kiyayi tah shuri,yanzu ba da bane an sauya tsarin kungiyar nan,sauran ma nayi musu gargadi,idan har kuka kuskura nasake kama wani a wannaa wajen ba ma iyah nan ba,toh ba iyah bulala zanyiba,wallahi kawu shehu dandakeka zanyi yanda akeyiwa Akuyah,ai ka tara y'ay'a da sun isheka,toh idan baka kama kanka ba zaka mutu babu mazakutah,ni nan ni zan rabaka da itah,idan kaji kayiwa kanka,yanzu idan ka shirya muje na kaika gida,sai a gyara hali kuma". Shidai har ta gama abinda zatayi bai ce komai ba har ta fita a office din yabi bayanta shima. Mota tashiga suka tafi,duk da lokacin tashi ba yyiba amma tabar aikin a wajen mataimakinta kawai. Suna shiga gidan kowa kallo yah bisu dashi,shikuwa baba shehu kofarsu yazo zai shiga,inna larai ce tayi tsallae ta tare bakin kofar tana masa wani kallon nasan mai yake faruwa. Bayyi mata magana ba sai tsayawa da yayi. Yana kallomta. Sameemah ceh da haushi yakamata ganjn zasu fara fadannasu a gaban yara tace, "Wai kekam inna larai meyasa kike hakane,ke har kina da karfin gwiwar dazaki yi wata magana akan laifin wani,hakan ma mijinki,nagan daman kin san yana aikatawa ba wai baki sanj ba,kawai yanzunne akka kamashi hannu dumu dumu,kaman yanda kema yasan halin dakike aikatawa. KO kin manta lokacin da kike bin manyan anguwa akan zaki dawo dakinki lokacin da shima ya ganki da malam mai gani har hanji na anguwar kan tudu ya sakeki idan kuma............" "Ke kinga dakata haka yah isa haka naji ,banason wani tone tone,shegiyar yarinyah kai,sai kace kedin allah da annabi kike bi yanda yakamata,naji zan barshi ya shiga amma ba dai ya tabamin kayan amfani ba sai yah tsarkake tukunna" Shidai wucewa yauyi ya barta a wajen tana ta sababi kaman aikota. Can wajen isha ne bayan anyi magriba,baba umaru ya aika a kiramasa dukkan yan matan gidan. Har bakin turakarsa suka je kowa ta samu wajen zama ta zauna. Gyaran muryah ya fara tareda godiyah ga Allah tukunna. Nasan kunyi Mamakin tara ku danayi ,badan komai bane saidan na gargadeku sannan na baku umarni,a gaskiyah na gaji da ganin masu hira a kofar gida,kaman ku su sameerah,sannan kuma da jawo magana wato irin su sameemah. Saurayi zainab ya bada uzirin cewa bai gama giniba,ga kuma wani aiki daya samu yana bukatar zuwa service,dan haka ina mai baku umarni kowa a cikinku ta fitar da miji,dan duk tareda za'ayi auren babu wadda zata sake zama na gaji haka sai na jj da masu tasowa. I'd an kuma baku fitarba toh in lokacin yayi koma waye zan aura ma yarinyah,zabi yarage gana ku. Ku ta shi Ku tafi na sallame ku. *+______________________+* *ABIN YABO BOOKSHOP* Kasuwar Rimi Kano Tel:📞 *07038339244* ❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤ Kar ku manta da #comment #share #like #follow. ____** *GIDAN GANDU* **____ ❤❤By sadi-sakhana❤❤ Wattpad username:SAKHNA03 ❤33❤ Kowa tashi yayi yah nufi harkar gabansa masu surutu sunayi,ita kuwa sameemah hakan bai dameta ba dan duk cikin zancensa babu wanda ta saka a mizanin gaskiyha bare har yah dameta,ai zancene ma ace wai itah ce zatayi aure. Da haka zancen
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55