Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 25

Chapter 25

Gidan Gandu Book 1 Complete Hausa Novel 1,266 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kartaji tusa ba,saidai ta mutu a kaita da safe. Bugo kofar nayi bayan nashiga wanda yasa dukkan su suka tashi a razane suna kallona,nima kallonsu nayi batare da nayi musu magana ba na koma na kwanta. Bayan shekara daya da tafiyar shaheedah mukayi sauka a makarantar mu'allim nafi kowa kokari da kuma kaifin hadda,kuma dama duk wanda yafi kowa ilimi toh za'a tambayi wanda yake zaune dasu shaidar halinsa idan an ga yah shiryu sai a sallameshi. Da sassafe muka shiryah domin zuwa wajen walimar,cikin kaya iri daya,na maza daban na mata daban,mu'allim na zaune akan kujera duk sanda muka hada ido said yayimin Murmushi,nikuwa kallonsa kawai nake,wai fah yanace danna shiryune na ke bada haddar,baisan carbinsa nake tsoro ba,dan duk sanda ya dakeni dashi kwana nake ina jin azaba,kaman ana kwaramin wuta,shiyasa nake binsa kawai a rabu lafiyah. Tunanin na katse lokacin dana ji ankira sunana,SAMEEMAH UMAR,tashi nayi zuwa wajen karatun na fara. Da karfi nake cikin kwarewa,saboda burina shine su sallameni a wajen nima naje naga me akeyi a cikin garin. Kabbara naji yah dauka lokacin dana gama wajen da aka bani,da ni watace dadi zanji amma maimakon haka saima gani nake bata lokacin su sukeyi. Da haka aka gama walimar da kuma karatun kowa yah kama gabansa,da niyyar gobe za'a ji wanda yayi na daya a bashi kyautukansa da kuma sallamarsa zuwa gidansu. Bamu muka dawoba sai tab ana kiran magriba,bayan munci abinci mun yi komaine,na kira,sunan su khairah ina gyara zama akan katifa ta,dukkan su nutsuwa sukayi,dan sunsan hankalinsu nake bukata a lokacin, "Yawwa inaso na gargadeku,idan aka tambayeku ni wacece naji wata tayi zancen abinda nake aikatawa,har kukasa aka ce bazan tafiba hmmmmmm,basai na fadaba kawai" Khairah ce ta cuna baki kafin tace, "Toh dama ko kin hanamu ai shaidar karyah zamu bayar a kanki dan ki tafi muma mu huta" Hairah ce tayi saurin gwabe bakinta tareda yimata kallon ta shiga hankalinta, Nikuwa tunda naji abinda tace nasan banida matsala tanan bangaren sai kuma a ji da gobe kuma. Da sassafe na tashi yau saboda zumudi mai zai faru,cikin sauri muka shiryah domin zuwa jin sakamako. Bayan anyi taro kowa yayi shiru yana sauraran mai gabatarwa can naji sunana yana amsa kuwwa kaman a cikin mafarki,dagaske fah ni aka kira wai na lashe gasar karatun qur'ani da kuma litattafan addini,tab lallai sunyi kuskure,tsinke tunanin nayi na tashi ina tafiyha cikin nutsuwa har naje gaban mu'allim,Murmushi yayi min tareda mikamin kyautata yana cewa, "Hakika nay I miki murna sameemah ke yarinyace mai hazaka da kuma dagewa,allah yah albarkaci rayuwarki sannan ina muki albishir da cewa a yau an sallameki daga gidan horo na yara zakije wajen danginki ki cigaba da rayuwa kaman ko wane da mai yanci" Banyi murnar karatun ba da kuma addu'a abinda na sani shine fita waje domin neman shaheedah shine kawai a raina,amma a fuskata murmushi kawai nayi tareda nuna masa na ji dadi sosai. Haka taro yah Kare kowa yah karbi kyautukansa mukuma nida sauran guda ukun da aka sallamemu kaya masu kyau suka bamu ba uniform dinmu ba. Tun kafin na shigo dakinmu su nanny sun hada min kayana uniform kuma sun dauke abinsu,su hairah nagani a,zaune ko kallon inda nake basuyiba,nima ban kallesuba,lokacin danazo fitane nace musu sai wataran,su ma toh suka bini dashi, na kama hanyata nayi hanyar waje inda za'a daukeni a mota. Bayan mungama sallama da kowa muka dauki hanyar tafiya,sauran mazane suna ta murna zasu je gida. Daya daga cikinsu aka sauke sai shima dayan da akayi tafiya mai nisa dashi aka saukeshi. Ni kuwa tafiya muke tun suna hakuri har suka gaji sukayi magana ganin nayi shiru bana da alamar nuna musu hanyar gidanmu, "Keh sameemah a ina zamu saukeki ne?" "A gidan dayake farkon hanyar dazaku shiga" Toh kawai sukace,a bakin wani gida mai baki get suka saukeni,kayana na dauka na shige cikin gidan kaina tsaye ina daga musu hannu,saida naga wucewarsu da wasu mintina kafin nafito daga cikin gidan ina lellekawa ko wani yah ganni a cikin gidan,saidai cikin sa'a babu wanda yaganni harna fito na tari taxi. A cikin taxi dinne na rokeshi yabani aran wayarsa, da farko bai niyyar baniba amma dana marairaicemasa akan gidanmu zan kira sai yah bani. Number wayar shaheedah na saka,cikin sa'a kuwa sai ta dauka,da farko tayi Mamakin ganina saidai ban barta ta cikani da surutuba na tambayeta address din gidansu,tana fadamin in fadawa driver da haka har muka isa kofar gidansu kafin nabashi kudinsa ina yimasa Godiya. Da murna ta rungumeni tana tsalle kaman zata cinyeni,cikin gidan muka shiga gashi mai kyau saboda babanta yana da kudi sosai. Mahaifiyar tace ta tarbeni cikin mutunci da ta fadamata ni kawarta ce ta makaranta. Satina daya a gidan su shaheedah komai yana tafiyah normal amma kuma matsalar daya shine yayanta yah takuramin waishi sona yakeyi ,saidai abinka da dan iska ina ganinsa nasan jirgi daya ne mudashi amma da alama ita shaheedah bata fahimci hakan ba,kuma duk matsalar daga wajen mamarsu ne domin itah ce take sangartasu batareda sanin mahaifinsu ba. Yau ma a zaune muke a falo nida shaheedah mamarsu batanan ta tafi shopping,sai shaheedah ta shiga wanka nikuma ina zaune da waya a hannuna,banzata na kawai naji hannu yana bin cinyata ina daga ido naga yah shaheed ne,abinne yaban mamaki ganin abinnasa har ya kai haka. Matsawa nayi gefe batareda nace komaiba,shima sake matsowa yayi yana wani bina da mayen kallo,fuskarsa ya matso domin yah sumbaceni bansan lokacin dana zuba masa wani gigitaccen mari ba akan fuskarsa,wanda yayi dadai da shigowar mahaifiyar su ta dawo daga kasuwa. Zubar da kayan siyayyar tayi tana bina da kallon mamaki,dan a duniya babu abinda takeso yah yayannata guda biyu ,shiyasa ta tsani jinin abinda zai tabasu ko miyeshi. Lokacin da aka kai shaheedah gidan horo ma itace tayi kutun kutun aka dauko mata yar ta. Matsowa tayi inda nake har sannan idonta bai dauke a kaina ba,ganin haka ne yasa shaheed yayi saurin cewa, "Ummeeh dama ban fadamikiba wai fa dan kawai ina yimata wa'azine saboda itace take hurewa shaheedah kunne lokacin da suna gidan horo" "Gidan horo kuma,amma naga shaheedah tacemin kawarta ce daga makaranta" "Karyane it's ce shugabar tantirai a gidan" Kallon su kawai nake batareda nace komai ba,dan ko mamaki banyiba tunda hakan ba bakon abu bane a wajena. Bayan sun gama zancen sune ummeeh ta kalleni tareda cewa na bar mata gidanta ,daga kai kawai nayi alamar naji,juyawa nayi domin komawa dakin shaheedah domin tattaro kayana,kicibis mukayi ta idah a bakin kofa da alama taji duk abinda mukace,bance mata komai ba sai rabewa danayi na wuce dakin ina tattara kayana. Rike hannuna tayi tana jijjiga kai alamar karna tafi,dafa kafadarta nayi ina cewa, "Ahah shaheedah dole na tafi amma ba rabuwar kenan ba,nima tunda akayi haka yanzu nafison nayi zaman kaina ba nawani ba" "Amma sameemah.........." "Karkice komai dan kinsan ba sauraronki zanyi ba" "Shikenan amma zan baki number BINLAD,saiki nemeshi nasan zai baki inada zaki zauna dan suna neman irinki,nima ina zuwa cikin satinnan dan akwai wani patrol da zasu je" "Shikenan hakan yayi ni bari na tafi saikin shigo,kuma sannan ki fadawa yayanki kar ya bari na hadu dashi a hanya ko kadan,ke kinsan mai zai faru dan haka ki

Table of Contents

Chapters

55 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});