Chapter 54
Chapter 54
bakin mai shelar: Toh jama'a ga wani aurem ma wanda yazo a bazata saidai muyi fatan Allah yasa a samu zaman lafiyah tsakanin amrayah SAMEEMAH dakuma angonta SAMEER. Kowa ka kalli fuskarsa a cikin gidannan yana cikin firgici saboda abinda yah ji,yam uwan inna hajarane basu ce komai ba dan kaman dama sunsan abinda yake faruwa musamman ma inna rabi. Ba ga iyah cikin gidanba hatta mutanen dasuke waje saida suka shiga cikin rudu akan abinda yake faruwa. Shikuwa sameer sunkuyar da gansa kawai yayi dan ji yake kaman kunnuwansa basu jiyo masa dadai ba na auren da ya jiyo sunan sa mahaifinsa yah daura masa da yar kanwarsa kwayah daya tall wacce yake da itah,kuma yake tunanin jininsu yah kusa fiye da kowa a gidan. Su burgune suka kamashi tareda shiga dashi cikin kidan dan koh kafarsa baya motsawa sosai,banda numfashi babu abinda yake fitarwa da kyar,shidinma barazanar karewa yake a makogaransa,babu abinda yake sakawa a ransa sai tambaya guda dayah. "Tsakanin nida sameemah shin wanene wanda ba dan gidan gandu ba kenan?" Gangar jikintane gameda tunanintah suka tsayar da itah a da'irah guda daya,tareda hanata damar sake motsawa tun bayan lokacin dataji BAK'IN SAK'ON,dayah jiyarci cikin dodon kunnwanta,dan ji takeyi da zasuyi arba da manzon sakonnan da sai ta raba kan sa da gangar jikinsa nan take batareda da nadama koh danasaniba. Idanuwanta ne kawai suka samu karfin gwiwar bijirewa sakon da kwakwalwarta suke basu na su tashi suma a aiki,saidai suna iyha kokarinsu naganin suna dakkomata hoton mutanen dasuke kallonta da ido a zare kaman itah ce wacce ta isar da sakon. Tafi dakika sittin a wajen bata san inda kanta yakeba,dan ta rasa ma mai yahanata barin wannan duniyah a yanzu mai cike da zallan rudani, Itama tambaya tayiwa kanta cewa, "Tsakanin mu wanene wanda ba ummah na ce haifeshi ba, NI KOH SHI???." Saida tasamu tah yiwa kanta wannan tambayar kafin komai na haske a idonta yadauke ya barta da bakin duhu mai cike da zullumi da rudani. Ganin tah fadi ragwaf a wajenne bayan sandarewarta na tsawon awa guda yasa akayi kanta tareda daukarta zuwa dakin baba umaru,dan shine kadai dakim da babu kowa a cikinsa a lokacin. Haka aka cigaba da biki saidai ba kaman da ba,kowa kuzarinsa ya ragu sannan kuma yana dauke da tambaya idam za'a amsa masa amma kowa yasan babu wanda zai zauna yayi masa bayani a lokacin. Dare yanayi aka zo daukar amare domim kaisu gidan aurensu,kawacce tasha kwalliya dadai yamda jikinta zai iyah dauka. A wajen daukar amaryah iyaye sunzo daukar salma yayinda su kuma y'ay'a suka zo daukar sameerah,dukkansu gida dayah aka kaisu saidai kowacce da part dinta. Part din salma a cikin gidane yana kallon na hajiyha mairo,yayinda na sameerah kuma yakewani bangare daban,dan sai an shiga wata kofah ma tukunna,sannan kuma za'a iyah fita ta ainihin get a kofar sameerah iyah karamar kofah ce tah hada ta cikin Gidan. Tum kafin a kawo salma da sameerah bayan daurin aure wata mata ta shiga dakin hajiyah mairo babu klwa sai su kadai,ta zayyane musu duk wani abu dayake faruwa,kama daga alakar salma sameerah har zuwa yanda rayuwar gidannasu take. Numfasawa hajiyah mairo tayi kafin kankamce ido tana cewa, "Lallai wato abin hakane koh,sun auri dana saboda su mallakeshi sannan kuma sun auri mijina saboda nima su gajeni,to kuwa hakan bazai yiyuba dole saina dau mataki da kuma fansa,wato dukkansu a siri sukayi musu bada son ransu suka auresu ba,ni nan ina nan zaune gahotar bansa mai ake cikiba,tabbna ai dole ma na dau mataki" A can Gidan surukan zainab kuwa wani daki aka kaita guda dayah sai dan wani waje na bandaki,hakanma inna laraba sai surutu takeyi wai an mata giinin bulo da bulo an sakata sauran matam y'ay'an ta da kuma itah kanta suna giinin kasa............hmmm toh fah. A rigingine yake yana kallon rufin dakin,dan tunda aka gama daurin aurennan aikinsa kenan koh magana mai karfi bayayi sai dauriyah kawai irin na mazajen sojoji,shi da yake zancen ana gama daurin aure zai tafi sai gashi har ana shirin kwana uku da aure amma har yanzu bai tafiba,bashida aiki sai tunani da neman mafita wanda har yanzu ya gaza samowa amsar ma,babu abinda yake ji aransa sai tausayinsu daga shi har sameemah wanda tun ranar yau tana cikin kwana na uku kenna amma koh mosti batayi ba . Manjone yashigo dakin tareda tsugunnawa a gaban sameer din,karakto da fuskarsa yayi yana kallon manjon. "Yanzu sameer kana ganin wanannan rayuwar zata kai ka,inaga mafitah shine kaje ka samu baba yah fitar dakai daga cikin zullumin daka ke ciki" Dan murmushi sameer yayi wanda daga gani na yakene kafin yace, "Ni bansan ma mai zanyiba a halin yanzu,nakasa samun mafita" "Dama bakaine zaka samu mafitaba kamata yayi kaje kasamu baban" Kimanin kwana uku da daurin auren,zuwa lokacin mutum duk san sa da jin abinda yake faruwa na auren su sameer sai da yah hakura yah tafi badan yasoba. ******* ********* Wata irin jan iska tayi mai karfin gaske,saida ta gama gauraye duk ilahirin jikinta kafin tah fesar da itah ta karfi kaman tayar trailer tah fashe.wani mikewa tayi daga kan gadon tana karewa dakim kallo kaman mai son tuno wani abu daya shige mata duhu. Wani irin huci tayi kwayar idonta tah koma tamkar jini na yan sakanni kafin suka koma yamda suke. Inuwar mutum ta gani yana shigowa dakim wamda hakan yasata kawar da kanta,dan a halin yanzu bata bukatar kowacce irin halittace tah kusanci inda take,bata dago taga waye ba har gama abinda yah ke shima yah fice,da alamar mai shigowar yah fuskanci yanayin da take ciki na rashin son ganin kowa a tareda itah. Tun safe tah tashi har wajen la'asar tana zaune bata motsaba,inna rabi ce ta shigo dauke da kwanon abinci a hannunta, "Yar nan yakamata kici abinci,yau fah kwananki uku bakici komaiba" Har ta gama surutuntah sameemah batace ko juyo da fuskarta ba bare ta kalleta. Matsala tayi da niyyar dafa kafadarta,aikuwa da sauri ta ja da baya ganin yanda sameemah ta buga mata wani arnen kallo mai kamada na karashiyah. Saurin barin dakin tayi jikinta har rawa yakeyi dan tsoro. Baba umaru ne yashigo dakim tareda cewa, "Sameemah yakamata zuwa yamzu ki kwantar da hankalinki ki rungumi kaddara,dan shima kansa yayannaki yaui tawakkali ba kaman keba,kashi har kwana uku sunyi da auren ki ya,kamta akaiki dakinki kema kaman sauran yan uwanki" "Aure ,dakina, yayana, tawakkali,toh duk nabisu da azababben gudu babu wando tsirara dan malafar ubansu,kuma kaima idan baka fita a harkata ba inban hadaka da duk munafukan da akwai hannun su akan danyen aikin dakuka mini ba na saka ku a daki daya na kona ku ba,harda shikansa dan banzan da kake kira da mijinnawa,duk abinda kuka aikata ma dole zaku amayar dashi yai basai gobeba,koda bazai amayuba billahillazi saikun amayo da hanjin da gurbatacciyar garkiyar lamarin yah taba.............." TAMMAT BIHAMDULLAH!! Ananne na kawo karshe litaffin gidan gandu,sannan duk wata cakwakiyah da za'ayi a cikin gidan gandu takare,yanzu sai a gidajen yan matan gidan, littafin zai cigaba..................Tambayoyinku dazasu samu damar amsuwa a littafi na gaba sune: #shin wace irin hargitsatstsiyar gaskiyah ce da su baba umaru suka boye akan rayuwar su sameemah? #wace irin rayuwa su sameemah zasuyi da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55