Chapter 43
Chapter 43
ta dauka tana kallo hade da murmushi ita kadai tasan mai take rayawa a cikin ranta. Wayar ta ce tayi kara tana dauka taga surayyah ce,kayan hannun nata ta ajiye kafin ta daga kiran. "Hello Allah ya taimaki ogah" Aka fada a daya bangaren, "Dama Bayan an gama shagali munga ogah burgu yah bamu kayan uniform ne na aiki,dama ogah abinda wurine haka" "Me kike nufi baku shirya bane" "Ahah min shiryah ogah allah ya bamu sa'a toh" "Yau Ku tabbatar kun gyara office din da duk wani abu daya kamata,ran monday kowa yasa uniform yah fito aiki,idan kuma naga mutum yasaba lokaci zai fadawa yan garinsu,kafin lokacin zan tsara wa kowa aikinsa da inda yakamata ya yi aiki,sannan zan duba tsofin maikata idan sun cancanta kuma zasuyi aiki dani toh zan barsu amma wasu dole zan sallamesu. Dafatan kin saka a speaker kowa yana jin abinda nake fada koh" "Eh kowa yana jinki shugaba,bari muje gida mu shirya saimu tafi gyaran office din,kuma ran Monday da asuba zanje,ai mun fi kowa jin dadin aikinnan" "Ya is a haka ban as on surutunki nan surayyah,kudai kuyi yanda nace kawai" Tana jin surayyah tana surutu amma ta shareta ta kashe wayar ta,shiyasa wani lokacin shirinsu da surayyah sai a slow,akwita da surutu da kuma lalaci,kubra da lubna sun fita nesa ba kusaba,saboda koh a maza ma sai an tona a samu kamarsu. Tun daga bakin kofah umman su surayyah take jiyo feduwarta a zauren gidan har ta iso tsakar gidan. Ummah bata kulata ba sai cigaba da tsinar shikafarta da tayi,shima nazeef dayake zaune suna hira da ummah kallonta kawai yakeyi, "Gaskiya umma ke yar gata ce fah" "Da akayimin me mai sunan uwata?" "Duk yayanki aikin damara sujeyi,nice ma babu wanda yayi zaton zanyi koh goge gogene sai gani da dankareren aikin vigilantee,ran monday dinnan mai zuwa za'a fara kwatance damu a garinnan,kuma wallahi babu mutunci kan ta ko uban waye,tunda shigaba ta bamu lasisi" "Dallah rufema na baki,a wane aikinnaki da bai taka kara ya karyah ba" "Kai ji nazeef dinnan,yo ba gwara namu ba da wannan shegen aikin sojojinnaku da mutum bai isah yayi abinda yaga dama ba,kullum hannunsa yana gefen kansa shi a dole ga mai biyayya" Haushi ne yakama nazeef inda yah tashi zai maketa,ummah ce ta hana tareda cewa, "Mai kake ci nabaka na zuba,ni bakaga kyaketa nakeyi ba,ai baza'aje ko ina ba zaka jita da ogar tasu,ina wannan yarinyar ce,kyaleta da ita kawai" Ahah ummah albarka zaki saka mana zamu fara aikin damarar muma muji mai wasu suke ji a ciki,har suke tada mana jijiyoyin wuyah" "Allah yasaka albarka" Shine kawai abinda ummah tasu tace,aikuwa daga jin haka surayyah ta hau wani kirkirar doron da da bata dashi, "Shikenan ai tunda kika saka albarka ummah to kowa ma yah kushe,kuma gyara gariannan sai inda karfin mu ya kare,sai mun kafa namu tarihin" Tana shiga daki kuwa bata wani dade ba sai gata ta fito da uniform dinanta ta janjame belt dinnan kaman zata miyar shi cikin cikkinta itah a fole tayi damara. Kallon su nazeef sukeyi suna boye dariyarsu dan karta gani, "Yawwa ummah kallifa uniform din yanda sukayi min" "Eh nagani kam,sunfi wannan tsukakkun wandunan naki,yau kam babu cin abinci da sauri ne,ko kuma yau baza'a koma ba ne?" Zaro ido tayi sai sannan ta tuna ashe zasuje shiryah office,komawa dakin tayi da gudu tana cewa, "Wayyo na manta Ashe fah ance mukoma,yau inaga tsire shugaba zatayi da nama na idan taji,ummah hada abincin gani nan fitowa yanzu nan" Jijjiga kai nazeef yayi dan ganin ahirmen kanwar tasa, "Wai ni ummah yau ban jita da safe ba,ko yau ma bata kwana a gida bane?" "Eh amma ta fadamin wai dinner zasu je na shugabar tasu ta samu kujera sanann kuma suyi shagali nasu daban,har gari ya waye,kasan shahshancinsu ai,tun wancan satin take lissafin shagalinnan,mudai addu'a zamuyi tunda yanzu ta daina zuwa kwana a wani wajen ma a nemeta a rasa,amma wannan sai da ta fadamin su da sameemah ne da kowa,kaga ba lallai ne ayi badala a wajen ba,saidai sharholiya kam wannan wajibine" "Toh shikenan Allah yah kara shiryawa ,indai zuwa wajen seemah alkhairi ne ana ganin sanji ai sai aiyi ta yimusu addu'a gaba dayansu" "Hakane abinda muke fata kam" *+______________________+* *ABIN YABO BOOKSHOP* Kasuwar Rimi Kano Tel:📞 *07038339244* ❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤ Kar ku manta da #comment #share #like #follow. ____** *GIDAN GANDU* **____ ❤❤By sadi-sakhana❤❤ Wattpad username:SAKHNA03 ❤30❤ Manjo ne a kwance akan wata katifa wanda da ita da babu ma duk daya ,sai nishi yakeyi yana daddaga ciki,ga fuska tayi suntum kaman yan mata zasuyi kwalliya sai sheki takeyi. Haushine ya ishi kulu ga wutar da take kokarin hurawa taki kamawa ga kuma dawainiyah da manjo. "Kulu zo ki gyara min wuyannan nawa yayi tsami" "Kai Dallah kaima ka rabu da ni,dame zanji wai,da wannan shegiyar wutar ko kuma da kai daka dameni,aikin banza lokacin dakake cin kudin ai bansaniba saida wahala tazo za'a zibgemin yau ga jaka" "Yanzu kulu ni kike fadawa haka ,ina mijinki" "Miji ? Muna miji dai,ai nayi kokari ma yini gudan da aka kawoka wane shegen ne ya leko a cikin yan gidannaku ya ga ya jikinka,har uwar da ta haifeka ma bata san me kake cikiba,ta dorawa kanta bakin kishi akan wacce ko yawo take da bakin jaki bata isa da itah ba(sameemah),daga ganinta da mai mota ta kwallafa wa ranta sai y'ay'an ta sun aureshi,sai kace itah nata dan motace dashi ake zaune dashi" "Yanzu kulu ni kike zagi dan kinga ina kwance kuma harda uwata" "Eh an zage kam,mai zakayi iyee?,kai ba gwanda kowa ma a cikin gidannan da kai ba,kafi kowa rashin amfani ,dan mugunta aka tashi aka hadani da kai,kuma duk inna ce ta bataka itah a dole ga mai da bata san laifinsa,gashi nan ta cuceka ta cuceni nima da nake ta fama" "Haba habibiyata share hawayenki wallahi ina sonki sosai,kuma na miki alkawari kodan farin cikinki zan zan shiryu idan na warke na fara sana'a" "Babu wani dadin baki ne dan nayi jinyarka saika warke ka koma gidan jiyah" "Bazan komaba kulun majatan uwar gida sannan kuma amaryar manjo" Murmushi tayi najin dadi kafin tazo ta gyara masa kwanciyar,sai nishi yakeyi babu dauriyah. Sameerah ce zaune a bakin katifarta sai tadi takeyiwa sameemah wanda take danne danne a waya, "Uhm naceba yar uwa mai yah farune naga kwanannnan sai zirga zirga kikeyi,koh wani abune yasamu" Dan tsabar mamaki lokaci daya salma da sameemah suka dago suka kalleta jin yamda ta kira sameemah din,da farko kam ma saida sameemah ta kalli salma dan ta zata da salman take magana,amma sai taga ita take kallo. "Uhm wani abu nakeyi,na riga ma na kammala sai kuma fara aiwatarwa" "Ayyah allah yah taimaka,yah saurayinnan naki dana ganku tare kuwa" Murmushin gefen baki sameemah tayi dan ta dago sameerah din,bare kuma salma wanda itah dama kar tasan kar ce itada sameerah, "Yana nan kalau shima" "Uhm amma yaushe zaki hadani dashi mu gaisa kuwa" "Banida iko da rayuwarsa duk sanda kika ga dama kika nemeshi zaku iyah gaisawa banda business da hakan ni" Shiru sameerah tayi daga haka dan taga babu alamar samun nasara a zancen. Zainab ce ta shigo dakin tana rusa ihu kaman
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55