Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 41

Chapter 41

Gidan Gandu Book 1 Complete Hausa Novel 1,265 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

gada kaje,shine kacemin wai kana wajen abokanka,toh bari kaji na fada maka dan gidan alhaji bala ne yake son seemah,dan jiya ma yini sukayi suna hira a cikin wata dan kareriyar motarsa,baka ga yanda innarku ta dau fushiba saboda basu sameerah yakeso ba,Nima da zai soni tun yaushe na fige wannan auren masifar ga.........." Bata kare maganar ba manjoya zabga mata mari tareda cewa, "Shegiyar yar kundun uba kai,ina tsaye kike cewa zaki je wajen wani saboda kinga yanzu na fara girma bana dukanki kullum" Bata bari yah karisa fadanba ta ture kujerar da take kai tayi dakinsu da gudu. Daga rigarsa yayi ya share gumin da yake tsatstsafo masa,dan yasan idan sule yaji labarinanna bai san yanda zasu kare ba sam,da haka ya samu kwarin gwiwar fita wajen, saidai zuciyarsa bata daiNa dukan tara tara ba,dan kudi kam ya cinyesu babu dalikinsu a wajensa. Saida su sameerah suka hau mashin kusan sau uku kafiin aka kawosu dadai inda saidai su isa da kafarsu saboda duhuwa da kuma matsin wajen,zainab sai ware ido takeyi dan dama ita kadai ce bata san wajen ba su sunsani. Wata hanyar suka nufa wanda zata kaisu wajen bokan da suka zo dominsa. A wajen wata bishiyah suka tsaya saiga dariyar sa ta na amsa kuwwa a wajen. Lokacin daya bayyana a gabansu saida zainab da saka wata uwar kururuwa dakyar inna ramatu ta riketa tana mata alamar gargadi da ido. Kara rikicewa tasake yi jin muryar sa mai kama da aradu tana dukan kasar wajen (hmmmm sumayyah kiji ta fah,amma take raina kawarki dan tana kallonta kullum). "Ki Shiga hankalinki ba a yimana yarinta a nan wajen,kinzo karbar sa'a ne ba nuna tsoroba,madubinmu ya nuna mana cewa idan akayi aiki zaki mallakeshi yanda kikeso har sai abinda kikace shi zaiyi,uwarsa data kawoshi duniya ma bata isa ba" Ai zainab daga jin haka ta gyara zama tana washe baki,zuyawa yayi yana kallon inna ramatu kafin yace, "Ke kuma ki tashi tsaye,domin aikin da mukayi akanta lokacin ta dake yarinya ba mai karfi bane,domin uwarta duk da mun nakasata tana kokarin yin ibada akan yayanta,toh sihirin dayake saka ta rashin mutunci da kuma jin batason kowa yah matso inda take da sunan yana sonta toh ya karye" Inna ramatu kaman zatayi kuka tace, "Malam kayi wani abu akai,naga alamar har tafara yin samari masu kudi,dan ina zaton morar nan ma yaronne yabata" "Bashine yabata na mahaifinsane ya bata ,dukkansu sonta sukeyi,saidai akwai aikin da za'ayi idan kun amince" Cikin sauri suka fara jijjiga kansu a tare, "Zamu maida soyayyar yaron zuwa kan babbar yarki sameerah,duk da bazawara ce amma haka zai nace yace duk duniyah itah yakeso,saboda soyayyar da iyayensa suke yimasa haka zasu amince da hakan,ita kuma zamu kara yin wani aikin a jikinta wanda zai kara saka kiyayyarta a cikin zuciyar mutane kaman yanda kuka fada" Sameerah wanda tunda aka fara magana tayi shiru,amma jin ummaruje da ko kallonsa bata san zatayiba ance zai sota har ya aureta ai tuni ta jita a wata duniyar daban. "Yawwa boka dama inaso idan da hali,a rabata da duk abinda ya shafi gidan alhaji bala,saboda kar idan nayi auren ta kawomin cikas,saboda naji kace uban ma yanasonta" "Eh kin fad'i wani abu,za'a nesanta ta da duk wata kaunar namiji a zuciyar ta indai da niyyar aurene,saidai ke anan zaki zauna akwai turaren da za'ayimiki wanda zai sa shi kwarewa cikin kogin sonki" Duk da bata son zama a wajen bokan tunda ta san halinsa,amma yau kam bata damuba saboda babban shirin da za'ayi mata,itama zata faso cikin manyan mata. Wani dauri yabawa inna ramatu wanda za'a saka wa mijin zainab din,sannan da wanda zatayi matsi dashi idan aka zo auren. Haka inna ramatu ta karba tana godiya suka taho itada zainab din,babu alamar damuwar barin yar ta da tayi wajen bokan *kai wa iyah zubillahi duniyah ina zaki damu,allah yakara tsare mana zuri'a,ya hana mu dogaro da wani bayan shi*. Kaman yanda sameemah ta fadawa shugaban yan vigilantee kuwa,karfe tara ma a garin nnsu tayi masa tareda shi da tawagarsa,duk da a fuskarsa kasan baya farinciki da abinda zai aiwatar saidai babu yamda zaiyi,*farillah ne tusa ga mai bacci*. A wani babban hall akayi taron wanda sameemah ta dauki nauyin komai,kama daga tarar baki har zuwa shirya waje da sauransu. Sai wajen karfe goma kafin ta shigo da kayanta na damara anyi masu dinki mata sun amshi jikinta sosai,dayake dama ta iya tafiyar sojoji sai hakan yabada wani style mai zaman kansa. Su kansu manyan bakin basu san sanda suka lume a kallonta ba har ta ison kan presentation floor din. Rigane da wando irin na kayan vigilantee sai wani babban belt daya zagaye hips dinta,ga kuma takalmi mai kaman na sojoji amma na mata,kitsone a kanta amma ta sau jelar ta kasan hular da take kanta. Babu kwalliyah a fuskarta banda dan lip gloss din da ta shafa,saidai fuskar nan babu alamar fara'a,dan dama bata dariya,a ganinta zubar da girma ne. Shikansa speaker saida yayi dan gyaran muryah har sannan yana satar kallomta kafin yafara abinda ya kawoshi wajen. Ba wani bayani sosai yayi ba saina yamda take gwagwarmayah a garin,sannan kuma yah kara da nasa aji moton irin na yanayin aikinsa,wato da abinda tayi da wanda batayiba,sannan da dalilinta na karbar aikin dan san kawo cigaba a garin. Tafine ya dauka raff raff a wajen musamman ma yaranta wanda suke cikin audience. Shugannne ya fito shima da kayan aikimsa a jikinsa saidai akwai yana yi tazarar ster tsakanin nasa da na sameemah. Godiyah yah fara mikawa kafin kuma yayi nasa dan takaitaccen bayanin. Yaransane ya miko masa takardu da kuma file wanda suke dauke da cewa ya yarda da zaman sameemah akan kujerar aikin,wanda zata zagoramci garin karkashin ikonsa. Mika mata fike din yayi da hannu daya itama ta miko hannun da niyyar karba,wani kallo yake binta dashi na allamar kinyi kuskure,yayinda itama take aikamasa kallon ina daidai da kai. Mutanen da basu san mai yake faruwa na gani suke kaman tausaya mata yake akan aikin. Alhaji bala da kuma Mahmoud dukka sun halarci taron,saidia alhaji bala ko kallon inda take bayyi ba,saboda shi kadai yasan takaicin da ta kunsa mar. Alhaji Sama'ila kam har taya murna yayi mata,yana wani cusa kai saboda idan bukatar alfarma ta zo,su samu da rangwamemi. Mic aka bawa sameemah domin tayi bayanin nuna godiyar ta gameda irin nasarar da ta samu. Karba tayi tana gyara tsayuwa,inda gun yayi tsitt kowa yana jiran yaji mai zatace, "Da farko dai ina godiyah da duk wanda yah halarci wannan taron,sannan ina yiwa kowa fatan komawa gidan lafiyah,gameda nasarar dana samu kuwa tabbas nayi farinciki,saboda ni kadai nasan dagewar danayi akan hakan,dan haka aiki sai inda karfina yakare. Sannan bazan yadda da shigowar wani gabana ba ba tahanyar da ta daceba,kowaye shi koda kuwa uba nanne sai na dau mataki akai,Shirina akan aikin nan kuwa nikadai na santa sai kuma idan wanda yayi abin da bai daceba zai gani,da kuma lokaci idan yah ara mana. Nagode sai anjima" Dukkan maganar cikin tsare gida da gargadi tayi ta gama,hakan yasa ko tari babu wanda yayi har ta gama maganar tayi shiru. Sallamatr kowa akayi saboda taro yah kare an bar wanda yah sauka da

Table of Contents

Chapters

55 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});