Chapter 8
Chapter 8
a kofar wajen amma babu wanda yayi gigin karisawa kusa dasu,bare su had'a dashi, Baba umaru ne ya d'aga muryah yah kira sameemah wanda take daki a zaune kaman ba itah ce ta saka su ba,saida akayi kira kusan uku kafin tah fito a dakin tana mitstsika ido kaman ba itaba, "Gani baba mai yafaru" "Gaki kaman yah,ki debe wannan karnukannaki kina gani zasu yiwa yar uwarki illah ?,kuma sannan ki debesu a gidannan yanzunnan" "Bazan Hanasuba har saita bani hakuri in ba haka ba kuwa wallahi sai sun mata balli ballin dana saka suyi mata,gobema ta sake zaginsu a gidannan in zamanta sukeyi" Sameerah kaman jira take dama tanajin mai ake cewa, "Kiyi hakuri bazan sakeba dan Allah ki hanasu karsu min fata fata" "Shikenan allah yah ceceki,kehh reza zo ki tafi yawanki yanzunnan,saidai barin gidannan babu inda zasuje,inda wanda yake bani abincinsu ya daina daga yau,ai sun mafi bil'adaman dasuke gidan mutunci,tunda su basa yin tazubardin da y'an gidan sukeyi" Tana gama fada tabar wajen ,batare da jira jin mai wani daga cikin wajen zai ce ba. Kowa shiru yayi yah tafi harkarsa,ita kuma sameerah ta fito tana share hawaye tareda jan zuciyah,fitasari yana bin gefen cinyarta. Zainab ceh (kanwarta wadda take binta saidai sameemah ta girmeta da kadan),tah kalli sameerah suna hada ido ta tuntsire da dariyah tana nuna fitsarin dayake bin kafar ta,itama sameerah fitsarin dayake bin ta takallah wanda sai a sannan ma ta kula da shi, "Kuttt keh dan buhun ubanki ni sa'arki ce kikemin dariyah iyee" "Hehehe niba sa'arki ba ce ina na isa,saidai ga wacce itama ba sa'arki bace ai ta saka ki fitsari a wandoπππ" Sameerah ceh tabi bayan zainab da gudu a zuciye,sai kuma inna ramatu tayi saurin dakatar da itah, "Keh dakata ina zakije da wannan fitsarin koh mahaukaciyah ta maida ki,bayan tura miki kare?,gashinan ai kin kaso aurenki kinzo yarinya karama tana miki yanda ta ga dama" "Kai ji inna da wani zance,naga ke kika nace saina aureshi saboda yana kawomiki kayan dad'i,da kika gane yana dukana kuma d'an shaye shaye ne,sai kika shiga kika fita kika raba aurena dashi,kuma yanzu kizo kice na kashe aure na,sameenu ma kullum sai dad'in baki idan nace yah fito aure sai yacemin zai tafi,yoh ya kikeso nayi iyeeh" "Toh yah isa haka ba tone tone nace kiminba wuce ki cire kayanki,dukkanku baku da wani ishashshen hankali kaman kuna cin k'asa" Wayah C.I.D yayiwa sameemah akan cewa yana kofar gida hakan yasa ta fita domin karbar abinda yah kawo mata, A zaune yake akan dakalin kofar gidannasu,yana ganinta ya taso tareda mika mata abinda tasashi yayi mata. Wani abu tah mika masa baki sannan sukayi kus kus babu wanda yakejin mai suke cewa, "An gama shugaba ranki yadade " Baba umaru ne yadawo daga masallaci anyi sallahr azahar ya wuce ta gefensu ita da c.i.d.din,har yawuce kuma ya dawo, "Kehh sameematu idan kin gama dashi din kizo ina san ganinki" "Tohhh" Lokacin da ta karbi abinda take bukata maimakon ta tafi kiran da mahaifinnata yayi mata sai wucewa daki da tayi kaman basuyi yace ta zo ba. Sai can wajen la'asar ne baba umarun yasake aika yaro ya kira masa itah. Nan ma saida ta gama sha'anin gabanta kafin ta tafi dakin baba umarun inda yake kirannata, KO sallama batayiba ta nemi waje ta zauna tana kallon bangon dakin , "Baki iyah gaisuwa bane?" "Na iyah " "Toh miyasa bazakiyi ba,koh sai ance kiyi?" "Banayine nasaba kowa gaisheni yake bana gaishe da kowa" "Toh nima harda ni,ni zan gaisheki kenan,mai yasa kina girmane amma komai yana kara tabarbarewa" Hade girar sama da kasa tayi da alama an tab'o inda yake mata kaikayi wato fad'a, "Tun dazu ka kirani ,amma toh kayi hakuri mana wani abu nakeyine,ni kasan banason fadannan,banaso ana min fada kuma ka sani" "Hmm mm allah yah shiryaki,toh naji kinji labarin alhaji babba(uban gidan gandu kenan,yah tsufah tukuf shine baban su baba umaru) bashi da lafiyah?" "Eh naji su zainab suna fad'a" "Toh kinje kin gaisheshi? Kokuma sai yah mutu ki leka gaisuwar sa" "Haba baba yanzu akan wannan ne dama ka kirani ,kuma fah kunsan mutuwa zaiyi shine kuma za'a fatamin lokaci akansa,habba dan allah,a dinga yimin adalci mana" "Keee sameematuh gyauton uwaki,nake ganin ki kamar kinada hankali ashe babu komai akanki kema sai wiwi din,ki tashi ki bani waje ,kuma ki tabbatar kinje kin dubashi,dan uwanki ma wani satin zasu taho ,sun samu hutun sati d'aya" "Tabbb AI wannan mai zubin aranan,hmmm ashe nasake shirin taryarsa kenan,dan rashin mutuncin nawa yayi sanyi,kar naje yah zo ya sameni da wanda ya sanni dashi,gwanda na yi sabo fill" "Innalillah yanzu koshi d'an uwannaki ma baki barshi ba,ashe ba iyah y'ay'an innarku ramatu kikeyiwa rashin mutuncin ba har shima baki barshiba" Toh kai ma baba umaru..........." "Karki sake cewa komai tashi kije yah isheni haka dan Allah,allah ya shirya ku kawai shine addu'a ta a kullum. Tana shiga daki kuwa taji su zainab suna zancen zuwan yayannata,wanda suke uwa d'aya uba d'aya itada shi,su kadaine y'ay'ayan inna Hajara,wanda tah mutu tun sameemah tana shekara bakwai,shikuwa MAJOR SAMEER tun bayan mutuwarta da kwana bakwai yabar ma garin gabad'aya ,inda yabi wani Soja a anguwarsu. A can yayi makarantar sojojin a wajensa sannan yah fara aikin sojan,saboda kwarewarsa da kuma zafin nama har yakai matsayin Major da kananun shekaru. Yanzu shekarar sa biyar da aure,inda yah auri matarsa Saleemah y'ar gidan shugabansu,da d'ansu guda daya mai sunan baba umaru,(farouq),saikuma ciki ta saleemah take dashi dan karami a halin yanzu. Babu wanda yasan wace wainar ake toyawa a gidan major sameer din saboda sai yayi shekara biyar ma bai zoba,dan tun sanda yayi aure yakawo matarsa bai sake dawowa ba sai wannan zuwan da zaiyi wani sati mai zuwa,suna can a porthacourt shida matarsa da kuma aikinsa. "Kee salma sinji wai yayah sameer zaizo wani satin shida anty saleemah," Zainab ta fad'a tana washe baki, "Toh miye dan zasuzo din ,ni wlh na tsani matar nan tasa ta wani makaleshi ko zuwa bayayi bare ya samu wata ya aura,sai ita kadai kawai" "Heeehhehe yarinya kice kishi kike,koh kina cikine a yi y'ar hadi gida keda shi" Sameerah ta fada tana turo daurin dan kwalinta gaban goshi,wanda tun dazu chatting take a WhatsApp batace komai ba sai yanzu " "Kee sameerah banason iskanci kishin uban me kuma,mai zanyi dashi " "Mai zai yi dake dai,kina nan guntun alhajawa sun lakace sun bar saura,kinga dan kyakykyawan matashi mai kudi kinaso ki shiga daga ciki" "Kutumar Uba lallai sameerah sai yanzu nagane inda kika dosa,kinaso kice kishi kike dani dan kinga bakya kasuwa,babu kowa sai wannan kanjamemmen sameenun mai kama da biri,Wanda koh daura min shi akayi zan cire na zefar ke kuwa nan har durkusawa kike kina rokonsa kar yah tafi" Wani wawan duka sameerah ta kaiwa salma a kumatu,ai kuwa suka hau kokuwa,zainab ceh ta tashi ta fice dan ganin abin yayi yawa,dama itah tsoron masifah ne da itah kamar farar kura. Sameemah kuwa tana zaune tana kallonsu saima dauke kai da tayi kaman ba'a haliccesu a dakinba. Wayar tah ce tayi ring ta zuya ta dauka,saidai batajin mai ake fad'a saboda surutun da su salma sukeyi,wata tsawa ta daka musu cikim bacin rai.Dukkansu shiru
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55