Chapter 34
Chapter 34
ce,kuma layinsa na gida aka kira ba na aiki ba amma duba da yanayin aikinsu ga kuma dama kanwarsa wanda yakeji kaman yah hura wauta yasaka ta ita ma ta bata. "Salam wa yake magana" Muryar wanda yajine yasa shi sauke wayar na yan sakanni,saida ya dan washe da Mamakin kafin yamayar da wayar kan kunnensa, "Eh nine ,kina magana da mahamood ne" "Dama nasan dashi nake magana ai,basai nayi maka bayanin waye yake magana ba,dan daga yanda ka sauke waya na wani kankainin lokaci nasan ka ganeni,dama nakira na fada maka ne cewa;kanwarka da kuke ta wahalar nema tana wajena tun shekaranjiya,idan kuma ta cika adadin danake jira banji kayi abinda nakeso ba,toh har Iman(yarsa)da kuma uwarta zan hada na yi gaba dasu,saika zaba koh su kokuma takardar wajenka" Komawa statue(gunki) yayi kafin yah saita saboda yin magana, "Uhm naceba amma taya zan san.........." "Karka damu ga vedion ta nan yana shigo maka,gobe nakeson kayi saigning din,saboda akaita wajen manya da wuri,mukwan lafiya a ci gaba da rarrashin tsohuwa" Sauke wayar tayi tana kallon surayyah wanda ta daina kukan karya da rausaya jikin lokacin da aka dauke camera daga kanta,saidai kuma akwai alamar bataji dadin maganar da akayi ba,saboda ta so a tambayi kudi masu yawa ko ta samu kasonta,amma ji yadda aka tsaya akan wata paper ta banza,cuna baki tayi tana kukkumbura fuska itah a dole ga sakaliyah. Tsawa sameemah ta daka mata duk da bawani finta tayi da yawa a haifeba,amma yanda takeyi kai kace itah ta haifeta, "Banason shashanci,nariga na fadamiki abinda nake da bukata karki sa nayi magana biyu,kodan kinga ina miki gentle,toh wallahi sa'a kika ci,dan koh shi yayannaki banason sakashi dole ta wata hanyar ne da tuni an wuce wajen. Ki shirya gobe watakila zaki koma gida,dan nasan zai yi signing ko daga jin yanayinsa" "Amma nace miki inasob shiga kungiyar nan fah" "Saikin kawo saka hannun yayunki ko iyayenki,idan ba haka ba karki bari musake haduwa dake,bazaki ji da dadi ba kwata kwata " Tana fita daga gidan horon bata zarce ko ina ba sai club,dan yau yanda yayannata ya bata mata rai tanajin idan dai ba shaye shaye tayi na fitar hankaliba toh akwai matsala babba,dan shedanun kanta babu abin da suke bukata sai jinin wanda yah bata mata rai a lokacin,saidai idan har ba babbban kuskure mutum yayi ba toh bata yimasa irin wannan hukuncin. A table din dayake karshen club din ta Zauna tayi shiru kaman mai nazari,muryar wani gaye taji yana yi mata magana,amma ko daga kai batayiba har ya gaji ya zauna dan kansa. Bartender (mai kawo odar)ce ta zo da book list a hannunta,tambayar sameemah ya shigayi akan mai takeso,itadai bata kalleshi ba sai nunawa da tayi da hannunta kan abinda takeso,dayake tasan mai sameemah tace ,wucewa kawai tayi domin isarda bukatar customer dinsu. "Yan mata ina ta magana amma bakice komai ba,gashi da alama kina cikin damuwa,koh zamu dan yi dance ne ina ganin zakiji kin dan sakko,ko kuma bari nayimana oder wata zazzafar giyah yanzu zakiji kin daina jin abinda kike ji," Har yayi surutun yagama sameemah bata dago tackalleshi ba,saima wasa da farcen hannun ta na dama da takeyi,abinne kaman yafara isarsa hakan yasa ya cigaba da magana, "Beb bakice komaiba,bai kamata ki dunga jin haushiba da irin wannna kyawunnaki ya kamamta kiji dadin rayuwarki gashi kuma......." "Kai bakone a cikin garinnan?" "Eh nazo wani aikine meyasa kika tambaya" "Saboda nasan da kasanni bazaka zauna anan ba,dan haka ka bace ka bani waje tun ban huce a kanka ba gaye" "Amma beb hakan bai miki kyau ba sam,sunana Tukur ana cemin TK,ke ya sunanki" "Dama ni na tambayeka sunanka ne ,bare ba fadamaka nawa sunan" Suna cikin hakanne matar ta dawo da wata yar karamar kwalba an nade samanta da leda said kumu murdaddiyar wiwi suma kusan goma a kan wani plate,tun kafin ta ajiye Tk yake Mamakin wanene yake shan irin wannan giyar mai karfi anan garin. Saida yaga an ajiye a gaban sameemah kafin hankalinsa yakoma kansa dukka. Yar karamar kwalba ce amma babu wanda zai iyah shanta haka ba tareda ya sirka ba,idan kuwa ba haka ba mutum zai iyah shiga coma ko kuma yayi akallah sati daya bai tashiba idan yayi sa'a. Mantawa tayi da wani jarababbe a gefenta saima bude kwalbar da tayi tana zubawa a cikin bakinta har zuwa makogaranta. Shikuwa gogan kaman television haka ta KO ma masa,koh A bai sake cewa ba har ta sauke kwalbar ta kuma dauki kwarkwaro daya na wiwin tana kyasta masa lighter. Busawa take hankali kwance saidai duk wanda yake kallon idonta yasan akwai sauran bakin ciki a cikinsu. Sun dad'e a wajen a zaune har sannan bai gaji ya tafi ba saima kallonta dayake tayi har takusa tashi da wiwin itama,lokacin dare yayi sosai dan a kalla shabiyu zata kusa gotawa,tashi yayi ya bar wajen koh sallma bai mata ba,itama kuwa bata kukashiba har ya fita a cikin club din da Mamakin ganin ko layi bata faraba bare kuma bacci ya dauketa na giyar. Sameemah bata tashi daga kujerar da takeba har saida ta ga babu ala mar wiwin da gama da su tukunna,fitowa tayi ta nufi motarta tana wani rausaya idonta har wani sanja kala yakeyi. Figar motar tayi duk da darene amma hakan bai hanata fara rage haushinta akan motar ba. Wata kwana tayi ta shiga layin gidannasu babu kowa sai filin wajen,a gefen motar sameer ta faka motar kafin ta fito tareda rufeta. Har takusa shiga cikin gidan said kuma taji kaman alamun mutum a bayan ta,tsayawa tayi domin jin menene zai faru,gyaran muryarsa taji amma duk da haka bata juya ba,shima kuma zo gabanta ba din ,duk da yasan ta gane waye yake bayannnata. "Daga ina kike da wannan daren,wanda in namijine ma yanzu yah koma gida,tun dazu kowa ya shiga gida har mazan amma ke sai yanzu zaki dawo?" Juyowa tayi suna kallon kallo itah dashi babu alamar maganar dayayi mata ta shigeta saima haushi da maganar tasa tayi mata, "Daga club nake,shiyasa kaga nayi dare ko kana da business akan hakan ne" *+______________________+* *ABIN YABO BOOKSHOP* Kasuwar Rimi Kano Tel:📞 *07038339244* ❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤ Kar ku manta da #comment #share #like #follow. ____** *GIDAN GANDU* **____ ❤❤By sadi-sakhana❤❤ Wattpad username:SAKHNA03 ❤24❤ "Daga club nake ko kana da business kan hakan ne,har yanzuna sai wani ya fadamin abinda zanyi,abinda naga dama nakeyi sannan banason wani yah dunga shiga lamarina,lokacin da wasu zasu fadamin mai zanyi yah wuce yamzu nice da alhakin jan ragamr rayuwata saboda nikadai nasan yadda nake fiye da kowa" Duk da karamar riga ce a jikinsa amma kana ganin yanda tsokar jikinsa ta murde saboda maganar da sameemah take yimasa,cikin zafin na ma kuwa yasake kifa mata wani marin har saida tayi baya amma ta tirje da kafafunta, "Ke Wacce irin yarinya ce,har ana cemiki daga inakike kina cewa wai daga club kike,gani kike abinda kike na arzikine,ko kuma rashin hankali,dakike cewa kinada hankali toh ko dabba bazayyi abinda kikeyi ba ,sannan nasake ganin kina mayar min maganar son ranki tana fitowa daga bakinki kina fadamin,idan bakiyi wasaba saina karyaki a gidannan kafin na tafi shashasha kawai" Saida ta bari yah gama fadar duk abinda yake bakinsa kafin ta dago da idanuwanta wanda
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55