Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 18

Chapter 18

Gidan Gandu Book 1 Complete Hausa Novel 1,265 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ni danjin da wa kuke zaune" *** *** *** *** Da farko kaman yanda kukaji sunana SAMEEMAH,saboda tunda nayi wayo haka na tashi naji ana kirana,abinda yha faru kuma kafin nayi hankali toh banida masaniyah akai. Mahaifiya ta hajara batada lafiyah,kullum tana daki kafafunta suna ciwo,ko yau she nice nake gyara kaya idan tah bat'a sannan na kai mata abinci idan kuma taci na fito dashi,shikuma yayanah wanda shima muke uwa d'aya dashi wato yah sameer,shine yake wanke kaya idan tah b'ata saboda ni sannan ban yi wayon yi mata hakanba. Watarana da safe na tashi daga bacci da safe lokacin banfi shekara shida ba,saboda tun bankai shekarun yin wasu abubuwan ba nake koyah,duba da halin da muka tsinci kanmu nida ummah tah,shikuma yah sameer namijine kuma yayi girma koyaushe suna gona shida baba umaru ,don su manjo ko me za'ayi bazasu jeba,kuma haka inna ramatu take d'aure music gindi suyi abinda suka ga dama. Bayan na yi shara da kuma gyarah dakin da muke,inna ramatuce tah shigo d'akin tana ta zage zage wai ummah tah bata iyah aiki kuma ta hanani ni na gunga tayasu aiki,ummah ceh takalleni bayan ta d'auke idonta daga kallon inna ramatu wadda tah kama labulen kofar ta rike tana ta masifa kaman tanayi da y'arta ba kishiyarta ba, "Seematu tashi kije ki tayasu wanke wanken kinji keda su sameerah kuyi" Inna ramatuce tayi saurin cewa, "Su sameerah bazasuyi ba itah kad'ai zatayi ,ai su jiyah su sukayi lokacin da kika aiketa karb'o maganin munafurci,yanzu haka ma na cutar damune mu da y'ay'anmu" Ummah bata kulataba saini ce,da abin yah k'ona min rai nayi magana,saboda maganin da take magana akai,manjo fah ummah tah aika a wani kauye kusa damu amma yak'i zuwa,saboda yah sameer yah tafi aikin kud'i shida yaran unguwarmu,amma haka inna ramatu tace bazaijeba saini ta aika naje na karb'o duk da aikan yayimin girma,amma ji abinda take cewa kaman batasan mai ake cikiba. Tun kafin nayi magana ummah tah katseni tareda cewa, "Seematu maza je kiyi wanke wanken allah yayi miki albarka" Kallon ummah nayi da takaicin yanda take bin duk abinda sukace kaman wasu iyayenta bayan itah ce duk babba a gidan idan ka d'auke IYAH MAI KALWA(mahaifiyar su baba umaru,matar alhaji babba,kakarmu kenan). "Amma ummah kince fah nayimiki tausa lafafunki suna ciwo?" "Eh ba sosai bane kije kiyi inyaso saikimin daga baya" Dan takaici haka badan nasoba na bi bayan inna ramatu ina zobara baki. Na dad'e tsaye a gaban wanke wanken ina kallonsa saboda bala'in yawansa kuma wai ni zanyishi,kwallar da ta fito a idona na share kafin na tsugunna na fara shirye shiryen farawa. Na shafe kusan awa d'ayah inayi duk kayan jikina sun jik'e jarab da ruwa,ban kulaba sai ganin Badariyyahn nayi ta watsomin kwanuka tun daga sama,har saida wani kwanon silver yah bigeni a kan goshina,kallonta nayi amma ko nuna alamar mutum yana wajen batayiba sai kama hanya da tayi tah juya,tana karairaya itah a dole ta fara k'irgen dangi. Ihun yara na faraji wai ankawo gyad'ar baba shehu ,da gudu nabar wanke wanken na zura da gudu domin nima kar ayi babuni. Kan gyad'ar muka hau nida su salma da manu muna tah tsina,karar duka naji akaina kaman saukar aradu,ihu nafaryi tareda tashi daga kan gyad'ar dan ganin waye,inna ramatuce take dukana wai ta bani aiki bangamaba kuma na tafi kan gyad'a. Dakinmu na shiga dasauri na tsugunna a gaban ummah ina kuka,kad'e kurar da take jikina tafayi saboda birgimar danayi a tsakar gida. "Toh kiyi shiru haka" Ta fad'a tana duba inda yah tsage a jikina yana had'ewa da kansa,nima kalon wajen nayi har sannan ban daina kukan ba, "Nasan kuka ne irinnaki amma ina babu zafi?" Jijjiga kai nayi ban bata amsa ba, "Ni abinda nake tsoro seematu banason kina lalfi suna dukanki,idan wata rana kikayi laifi suka gane cewa ciwo a jikinki Yana mannewa da kansa bansan mai zance ba,maganganune zasuyi ta fitowa wanda bazasumin dadiba sam" D'aga mata kai kwai nayi alamar naji,kafin ta bingire a wajen na fara bacci. Na manta ma da tausar danace zanyi mata itama kuma bata tasheni ba ,saboda dukkan mu tausayin kanmu mukeji. Abubuwa da dama sun faru a satin ciki harda zafin da rashin lafiyar ummah yah k'ara,yanzu har yah kai koh tashi tah zauna bata iyah yi sai an taimaka mata,shikansa yah sameer ko yaushe yana d'akin,nukuma nakan fitah wasa,wajen yara a waje,saidai in anyimin abune zan dawo gida kokuma in dare yayi ,dama masu iyah magana suna cewa *sai gida wai an doki kare a kayi*. Fitowa nayi daga dakinnamu aikuwa cikin rashin sani na shambe kalwar IYAH,wacce tah shanyah a Rana tana jiran ta dan sha ta curata dan taci kasuwar gobe,tsayawa nayi nai shiru dannaji ta ganni koh bata ganniba,cikin daga muryah kuwa irin ta masifaffunnan muryarta ta doki dodon kunnena. "Keeeh dan kusun uwarki uwarkice tace kibimin takan kalwa koh kuma tashen rashin hankalin danaji dama ana shedarki dashi,dazaki zo ki takamin kalwar yanzu idan nace uwarki tazo tayi zata minne,tana nan da itah ba gurguwa ba itah ba mai kafafuba,bata tsinana komai saidai a zuba abinci a kai mata ta cinye. Cikin yanayin dama na saba da masifarta nayi ficewata wajen wasa,dama ana ta jirana nice nake acting din boss a wasan. *+______________________+* *ABIN YABO BOOKSHOP* Kasuwar Rimi Kano Tel:📞 *07038339244* ❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤ Kar ku manta da #comment #share #like #follow. ____** *GIDAN GANDU* **____ ❤❤By sadi-sakhana❤❤ Wattpad username:SAKHNA03 ❤14❤ Tun lokacin dana fita bani na dawoba sai wajen la'asar,muna had'a ido da yah sameer wanda yake gefen ummah a zaune yah watsamin wata uwar harara tareda cewa, "Ke dan ubanki daga ina kike iyee" Shiru nayi ina mitsitstsika ido,saboda kogi muka bi malam sule yaje kamo kifi,kuma nasan sarai an hanamu zuwa,kawai rashin ji ne irin nawa,ummah tayi saurin fansata daga amsar dazan bashi,saboda a duniya ta tsani a dunga dukana domin guje tsoron a gano yanayin yanda jikina yake,ni kuwa ko a jikina itah ce take rawanta da kid'anta ita kad'ai. Saurin rab'ewa nayi na koma gefenta na zauna,can gefe dashi saboda kar yah bugeni dan nasan halinsa sarai,mungun yaro ne shi,kama hannun ummah nayi na rike tareda cewa, "Ummah ya jikinnaki kinji sauki koh?" Tun kafin ta bani amsa yah sameer yayi saurin cewa, "Zaki tambayi yah jikinta mana bayan tun safe kika fitah gidannan bance da rana ba,sai yanzu aka ga k'eyarki,saboda shegen yawo irinnaki" "Kai kai sameer,nikam banason kana hamtararta kaman ba kanwarka ba,idan batayi wasaba mai kake so tayi,yaro ai dole sai yayi wasa,kayi addu'a ma da ta dawo lafiyah" Tabb yah sameer dinner zaiyi wata addu'a wai na dawo lafiyah yo na mutu mana,na fad'a a raina,ummah ce tah katseni da tunanin danake musamman da taga ina hararar yah sameer din tagefen idona,tasan sarai yanzu zai bugeni idan yah kula da mai nakeyi masa, "Ke seematu tashi ki d'auko abincin ki a gefen daki can,har yayi sanyi baki ci ba tun rana" Toh na amsa dashi kafin na tashi na d'auko ,ina budewa na saka hannu na fara ci,lomar farko dana kai muka had'a ido da yah sameer,ya mutsa fuska yayi tareda cewa, "K'azamar banza ,ji yadda take ci babu wanke hannu kaman ba yanzu tah dawo daga wasan k'asa ba" Juyawa

Table of Contents

Chapters

55 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});