Chapter 33
Chapter 33
maman najwa mutumiyar taki koh,dan ma naga su yah kubrah suna yi mata nasiha,da kuma su zuzunmasta,batayi sallar ba kuma fah?🙄😲,gashi kalau take rasss). Malam ne yayi gyaran muryah ai kuwa kowa yayi shiru aka cigaba da cin abinci. Bayan sun yi wanka sun shirya saida suka shiga gidan kawunsu wanda suke uwa daya uba daya da inna hajara kuma kaninta. Surfe sukeyi a tsakar gidan matannasa lokacin dasu sameemah suka shiga,gidane mai fili sosai saidai sun shareshi kall abin sha'awa,iyah matannsa suka gaisar basu sameshi ba ya tafi cikin gari cin kasuwa,kudi sameer ya rabamusu sai godiyah sukeyi da saka albarka. Shikuwa malam mansur lokacin da suka zo tafiyah kayan gona ya hada musu irin su wake da gyda ,da yake lokacin kaka'a ce,amfanin gona ya dawo gida.itama iyah tayi kokari,dan jarkoki ta cika musu da kindirmo da kuma shima man shanu ciki leda,godiyah sukayi sosai dai kafin suka kamo hanyar dawowa gidan. Wayar sameemah ceh tayi kara inda tafara magana cikin tsare gida, "Bance kuyimin shirme ba ina dawowa in anjima dinnan,ka saka wani yah wankemin motar nan kafin na dawo dan akwai aikin da ban kammala ba na shekaran jiyah,sannan ku tabbatar yarinyar nan kun kula da itah yanda ya kamata,idan har nazo naga ba yanda nace ba duk ranku zai baci..................yadai fi muku,ina zuwa yanzunnan" Tana sauke wayar suka hada ido da sameer tah madubi yana kallonta da alamar tambaya,itama dayake tasan yau kawar da idonta tayi kaman bata san yana kallonta ba. "Wace yarinya kike magana akai,yar gidan uban waye?" "Yar Gidan uban wani ce mana" Tsayar da motar yayi yana huci jijiyiyin jikinsa sun tashi sunyi wani rudu rudu,saleemah ceh ta make a jikin kujerar ta ganin yanayin daya shiga,sake kallon sameemah yayi ta cikin madubi har idonsa sunyi kala, "Me kike nufi,bayan abinda nakeji na dabanci har kidnap din yara kikeyi ashe?" "Yanzu idan kidnap dinne ina ruwanka dan farouq na dauke ko me,ni banaso ana min katsalandan a rayuwata,akwai wanda yake daukar dawiniya tane,ko kuma kayanka na taba kake tada jijiyar wuyah,saika bari idan na taba naka sai kamin abinda ka ga dama mtseww" Tun kafin ta gama tsukar yah kifa mata mari a fuska,abinda ba'a taba yimata na tunda take bayan ta girma,kallonsa take da idonta wanda suka fara canja kala zuwa jawur,saurin rufesu tayi dan tasan a lokacin idonta sun fita daga kalar dasuke,sannan tana koarin saita rawar da jikinta yakeyi. Shikuwa juyawa yayi ya tashi hanyar suka cigaba da tafiyah,har sannan bai daina masifa da kuma kirafin halayyarta ba na raini da kuma rashin kamun kai. Tana jinsa duk abinda yake fada saidai a lokacin ba tashi takeba tukunna ta hucin da zuciyarta takeyi take tukunna. *+______________________+* *ABIN YABO BOOKSHOP* Kasuwar Rimi Kano Tel:📞 *07038339244* ❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤ Kar ku manta da #comment #share #like #follow. ____** *GIDAN GANDU* **____ ❤❤By sadi-sakhana❤❤ Wattpad username:SAKHNA03 ❤23❤ Suna isowa kofar gida tun kafin yah tsayar mota sameemah tayi saurin ficewa daga motar kaman ana harba ta ceàudirect zuwa kan gadonta,ta dade a kwance kafin ta dago saboda ringing da wayarta tayi,saida ta ga mai kiranne kafin ta tuna da cewar ashe tana da wajen zuwa fah. Cikin yanayin daga mutum yagani yasan tana bukatar hutu amma hakan bai hanata tashi fita wajen ba. A bakin kofar gidan suka hadu da burgu ya kawo mata motar da ta bayar a wanke,karbar key din tayi ta su ka shiga sai gidan horonta inda ta bayar a ajiyemata yarinyar. Kofar wajen a bude suka ganta hakan yabawa sameemah mamaki saidai bata ce kkmaiba sai shiga gidan da tayi kawai . Su mungun dawa ne a zaune sun baje suna karta,saikuma wata yarinya a tsakiyarsu itama da katin wasan a hannunta,wani saurin bugawa tayi tareda tsalle tana murna saboda nasarar da taci a wasan. Babu dan kwali a kanta sai dogon gashinta madaidaici wanda ya baje saboda rashin daureshi da ribbon,dogon wando ne a jikinta da kuma riga t-shirt bak'a anyi mata adob fari. Dukkan su surutu suke basu damu da tsayuwar sameemah a wajenba wacce ta kama kunkumi tana kallon ikon allah. Saida burgu yayi magaana kafin kowa yah nutsu ciki harda yarinyar da take tsalle da murnar cin wasan,mungun dawane yah gyara murya kafin yace, "Eh wato dama shugaba abinda yafaru shine,itah yarinyar ce wai gwanda da muka daukota kuma zatayi vidion anayimata azaba ma kodan yasaka hannun,wai dama ya takura mata" Dakatar dashi sameemah tayi tareda cewa, "Banason wani shashancin zance,ba abinda na daukota dan nayiba kenan,tsakaninta da shi bai dameniba" Matsawa baya yayi jin mai tace,matsawa kusa da yarinyar tayi tareda cewa, "Menene sunanki inason jin takaitaccen bayani game da tarihinki" *true life story ne na yarinyar wanda yah faru da gaske,saidai zan kara wani abu ba kaman yanda aka bani labarinba,amma zan sanja suna saboda yanayin tsaro* "Sunana Surayyah kuma ni kadaice a gidan mu y'a mace,sannan kuma nice ta karshe a gidan wato y'ar auta,Saida mafi yawan yayuna suka girma har suka zauna da kafarsu kafin aka haifeni,Akwai soja ,yan sanda,morpol custom da sauransu,kuma dukkansu yawanci aikin d'amara sukeyi. Mahaifiyar mu bata yimin fada dukkan abinda nakeso shi nake,gashi allah yah yini da rawar kai kuma da farin jinin mutane,sanadiyyar rashin mutuncin danake yi a gari ina jawomusu abin magaan yasa suke yimin horo mai tsanani,amma duk a banza ina warkewa zan koma. Haushinsu nakeji kaman na kashesu,inaso naga suna bani kudi sosai amma babu wanda yake bani komai,dan haka ni koma menene zanyi idan ta kama ma kuce saceni kukayi,suna da kudi sosai kuma nasan su abba zasu tashi hankalinsu har sai an bada kudin. Nima saiku dan bani nayi harkata" "Toh naji labarinki saidai ban daukoki dan nayi kudi dake ba,na daukoki ne dan nasa yayanki yayimin saigning akan wata paper game da wani aikina. Batun kudi kuma zaki iyah yi dakanki,saidai abu daya zanyimiki ,nayi niyyar dan taba lafiyarki dan yasan da gaske nake,amma tunda naga kema da hannunmu ce zaki iyah yin pretend a matsayin mun dakeki saboda abin ya tafi miki a sauki" "Toh shikenan naji shugaba,amma inaso na zauna a cikin kungiyar nan,saboda nima nayi zama a cikin yan daba a unguwarmu" "Ahah ban karbekiba ,baki cika abinda nake bukata ga yan kungiyata ba,saboda ke kina da yadda zakiyi wato bin maganar yayunki,amma idan har kika karbo saka hannunsu a paper toh wato sun amince toh zan karbeki,yanzu zan kira creator yah sanja mikk kama irin na wanda yasha duka,zamu fara buga wasa da yayanki tunda naji shima dan taurin kai ne" Bayan wasu mintina kuwa mai kwalliya yazo,inda surayyah ta zauna aka gama kirkirar ciwo kala kala a jikinta,kai kace dama ciwon gaskene. Lesson na dramar dazatayi aka fara bata kafin lokaci n action din yah fara. A can gida kuwa su mahmood in hankalinsa yayi dubu toh ya baci,saboda batan layar zanar da surayyah tayi tun shekaran jiya,babu kuma labarin ta ko kadan,tun abin suna zaton karamine har yazama babba,kuma shi kadaine babba wanda yake garin,sauran dukkansu suna garin aikinsu. Karin abun ma kuma mahaifiyar su da ko abinci taki ci sosai dole sai an kawo mata yar ta. Yanzun haka yana tsaye a cikin gidansa itama matarsa tana nata korafin na kudin ankone ya ga kiran waya,da bazai daukaba saboda bakuwar lamba
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55