Chapter 40
Chapter 40
halin na barin mutane su gama fadar abinda yake bakinsu,kace kasan labarina,amma bayaninka ya nuna baka sani ba,saboda da kasani da bazakayi furucin da kayi yanzu ba" Fitowa tayi da dan kunnenta wanda yake yin yar danjar wuta ta ajiyemasa a gabansa,ido ya zaro yana kara karewa abin kallo,tabbas Camera mai recorder yake gani. Kasheta tayi kafin ta gyara zama,wasu takardu ta mika masa tareda bashi damar dubawa. Gumine ya yanko masa lokacin daya gama karantawa,(ba komai bane sai taksrdun ban girma da aka bata a kasar Brazil lokacin da suka je horo). "KO baka fada ba na karanta abinda yaje kan fuskarka,kuma nasan kasan labarin Raudah da take jikin paper,idan naga dama zan iyah neman kujerarka da takardun kuma na samu. Yaronka kuwa karamin alhakine,dan zan iyah kutse cikin yanar gizon asibitin na sanja information dinsa kaf,zuwa abinda naga dama,kuma babu wanda zai gane. Dan haka umarnine kasa ka hannu a takardun nan,ka taho dasu gobe zuwa garin mu ka dorani akan kujerar dana ce maka ina so,idan kuma ka kiyin hakan,.............hmmmm toh zaka sauka akan taka kujerar ka bani,sai ka zabi abinda kaga yafi maka" Tana gama fadar hakan ta fice a office din ta barshi yana goge gumi da handkerchief . Bata yiwa su burgu wata doguwar magana ba,sai kawai alama da ta musu akan su zo su tafi. Da gajiyah amma dauke da farincikin samun nasara ta isa gida,sabani wancan zuwan da bata samu abinda takeso ba. Yau tayi akan zata hadu da ummaruje dan haka tun yamma yake shiri kafin ma rana ta danyi sanyi,dayake ya fadawa mahaifiyar sa inda zaije wato hajiyah mairo,itama sai murna takeyi dan haka kawai take some sameemah din. Itama sameemah a bangarenta shiryawa tayi,duk da bata arziki bace dan kwalliyar wandunan nata tayi amma tayi kyau sosai. A motarsa yazo dan haka tana zuwa gaban motar ta shige. Kowa zai wuce sai yah kalli motar saboda kyanta,kuma ga hasken allah dan kowa yana kallonsu a gaban motar kasancewa ba mai tinted bace. Tunda ta shigo motar ummaruje yaje murmushi wanda ita kuma hakan ne yasa taji ta takura,dan ta tsani taga mutum yana ta murmushi ko dariyah,shiyasa zama da mata yake mata wuyah,saboda basu da aiki daga gulma sai dariyah da shewa. "Barka da fitowa baby" "Wacece babyn wai ni?" Mamakin tambayar da tsyi masa yayi amma sai daure yah cigaba da magana, "Gaskiya nayi farinciki da har kamarki wannan kyaky kyawar ta bani izinin nazo ganinta" Surutunsa yake tayi amma bata sake cemar komai ba saima cewa da tayi, "Uhm Idan ka gama nizan shiga ciki a gajiye nake sosai,ka gaidamin hajiya " Baiji dadin abinda tace ba amma haka yah daure tareda mikamata wata bakar leda a kusan cike da kaya. Kallon ledar take taredashi kafin tah yunkura zata ba motar,saidai tsyawa tayi jin abinda yace, "Dan allah karkiyi haka,wannan kyautar ba daga hannuna bane ummah ce tace na kawomiki,idan na koma dashi bazata ji dadiba,koda bazakiyi amfani dashi ba at least ki tafi dashi. Fizgar ledar tayi ko sallama batayi masa ba,shima a nasa bangaren Murmushi kawai yayi tareda cwwa, "Farkon farawa ne" a ransa. A can gida kuwa tun kafin sameemah ta shigo har zance ya baza cikin gidan har da makwantai cewa sameemah tana hira da dan gidan alhaji bala a mota,bakin ciki idan yayi dubu toh ya taru a cikin ran matan gidan gandu,dan tsohuwar gaba ce tsakaninsu da jinin inna hajara wanda suna ganin babu ranar dazata gushe a cikin ransu. Musamman ma uwar gayyar wato innna ramatu,cikin hade fuska taja su sameerah daki daomin taji ainihin tushen zancen,duk da tah leka amma hakan bai isheta ba. Zama tayi akan gadonta mai rumfa yayinda su sameerah suka zauna a kan kujerar dakin kwallo dayah kaman rai. "Wai ummah mai kike fadane ban ganeba" "Bazaki ganeba sameerah amma indai har asirin dayake kan sameemah yah karye toh akwai matsala,dan haka basai gobe ba a yau komin dare zamuje wajen malam domin yimana sabon shiri,tsugunne bata kama mu ba,ba iyah ni kadai ba har da sauran matan gidannan" "Toh Wai ummah ina ta magana amma kin saKa mu a cikin duhu" Masifah ta darara musu tareda cewa, "Dallah ni kuyimin shiru,maza kowa taje ta dauko mayafinta mu tafi,har ke sameerah dake,saboda akwai tsumin danake so ayimiki,dan babu shakkah ina jiyo tashin hankali yana tunkatowa" Duk su ukun tare suka fito daga dakin,inda sukayi kisibiss da sameemah tah dawo daga waje da leda a hannunta,wanda kowa yah gani yasan ba abune na harkar karanta a cikiba. Wucesu tayi tana waka ta shige dakinsu,inda sai a lokacin dukkan su suka dauke idonsu daga kanta suna jijjiga kai tareda cewa........uhmm! Toh nima uhmmmm.........😀😀😀😀 *+______________________+* *ABIN YABO BOOKSHOP* Kasuwar Rimi Kano Tel:📞 *07038339244* ❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤ Kar ku manta da #comment #share #like #follow. ____** *GIDAN GANDU* **____ ❤❤By sadi-sakhana❤❤ Wattpad username:SAKHNA03 ❤28❤ Duk da dare yayi amma haka inna ramatu ta dage akan dole sai sun tafi waje malami,dakyar suka shawo kanta aka bari akan sai gobe da hantsi sai suje. Can Bayan isha kowa yana kofarsa saiga inna larai da dan mayafi ta shige dakin inna ramatu. Sun Dade suna dan kuskus dinsu kafin ta fito ta koma kofarta. Kaman hadin baki kuwa tana komawa itama inna karima ta shiga kofar,itah kam sai can wajen dare kafin ta tafi. Gabadaya gidan shiru yah koma banda munafurci babu abinda yake zagayawa a gidan,ko na menene oho....... Da safe gidan da wani yanayi daban yah tashi, Sameemah tah shiryah ta tafi wajen shirye shiryen hawa kujerar ta Sukuwa su sameerah sunyi hanyar zuwa wajen malamin sa'ar su. Yayinda innna larai kuma tace tah tafi gidan su in jita da fada. Itah kuwa inna karima dayake gidan su babu nisa tun a jiyan taje gida,dawowarta ne ta shiga kofar inna ramatun. Sauran kofofin kuwa kowa yana fama da tasa matsalar,musamman ma kulu habibiyar manjo🤣🤣🤣🤣. Shigowa yayi daga wajen mai shayi yana daga wata babbar riga ko waye yah bashi ita oho,kulu ce ta kalleshi da kallo mai kama da harara kafin tace, "Kai manjo sai ka cemin wai ka tafi shan shayi saina ce ka kawo kidin sabulu da abinci rana kacemin kai baka dashi,wai a ina kake samun kudinne,dan nasan mai shayi ba kanin ubanka bane da zai dunga baak kullum a kyauta ai" "Ke kulu wallahi ki shiga hankali ki,na hana ki yimin magana kaman dan ki bakyaji koh,toh ba kudina bane ,kudin sadakin sameemah ne nake dan tabawa a matsayina na yayanta" Tsayawa tayi da hurar wutar da takeyi tana kallonsa da alamar neman karin bayani,ganin bazai sake magana ba gashi kuma ta matsu ta ji mai yake faruwane yasata sake tambayar sa, "Manjo wace sameemah kake nufi" "Sameemah dai ta gidannan akwai wata sameemah a garinnan ne bayan itah,shegiya mai suna mai wahalar samu,anayin kwatance mutum yasan ita ce" "Amma waye yabaka sadakinnata ne" "Waye kuwa banda amininna sule maye,kinsan irin kaunar da yake mata kuwa" "Ahah bansaniba amma daga ganinka baka da labarin abinda yah faru a kofar gidannan koh?" Matsowa yayi kusa da kulu yana baza kunne kaman wata mace a wajen son gulma, "Ke fa dam in mai yake faruwa kinsan daga ni har sule bama gida mun tafi karkashin gada" "Ohh dama karkashin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55