Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 3

Chapter 3

Gidan Gandu Book 1 Complete Hausa Novel 1,270 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

"Banjin sunan zazzakar kazar ba?" "In min hadu zakaji abinda yafi suna ma" "Shikenan idan kinshirya zamuyi waya " Bata sake cemasa komai ba tafice daga cikin parlorn. Bayan sun gaisane shida alhaji Sama'ila,sai yayi shiru kaman mai tunani yana ta murmushi shikadai,alhaji Sama'ila ne yakatseshi ta hanyar cewa, "Amma alhaji BALA naji dadai kuwa harkar da kuka kulla kaida seemah jar wuyah" "Au Ashe kajimu,gaskiya na samu dami a akala dan dagani zatayi dadin harka sosai" "Hmm alhaji bala kenan,anya kuwa kadauki dami mai kyau kuwa,karfah ka dauki dan maciji ina........,.." "Kai kai alhaji Sama'ila menene kuma na wannan maganar,babu abinda yafaru kabar ma wannan zancen muyi abinda yakawo mu kawai". A wajen fita waje kuwa bayan sun zo hawa mashin,burgune yakalli sameemah da Mamaki abinda yafaru, "Amma shugaba maganar da kukayi keda wannan alhajin anya ba matsala kuwa" "Me nake Tunani,ka fara mantani ne,gaskiya yakamata ma na fara sabon aiki dan ina ganin nayi laushi dayawa tunda har kuke min wannan kallon kaman kuna gaban kannenku mata na gida" Basu sake cewa komai ba sai burka mashinansu dasukayi kowa ya dale,dan da alamar sun jiyo gargadi da kuma fushi a cikin muryar tata. Acikin gidan gandu kuwa tun safe ake abu daya har rana ta fara zafi lokacin daura abinci amma babu alamar zasu daina hayaniyar dasukeyi. Inna larai kuwa tun ana jiyo muryarta da karfi harta fara dushewa saboda masifah,kawu shehu ne yayi sallama ya dawo daga gona,tun daga wajen kofar gida yakejin masifar da akeyi wanda inda sabo yariga ya saba,saidai daya shigo gidanne yakula da kofar tasa cike take da mutane kaman ana rabon kudi,karo sukayi da baba umaru (baban su sameemah)wanda shikuma gadin makarantar primary anguwar yake wanda antashi kenan ya dawo gidan, "Ahah shehu yadai kana kallon gaban ka kuwa?".a kokuma maganin abinda yafaru?,ai kin fi kowa dabbanci da irin wannan kwakwalwar taki,baku da aiki sai shege kishi da fada,shi kadai kuka iya kawai" Baba umarune ya rike kawu shehu wanda yake ta zazzagawa larai masifa saboda tsabar ransa yabaci,daki ya wuce yadauko yarinyar wanda jikinta yayi zafi rau saboda Zazzabin daya hau Jikinta. A hanyar fita suka hadu da mazan gidan guda biyu,da Sule dakuma Bashari wanda dukkansu yayan baba umaru ne, "Yawwa kai sule bi bayan kawunka shehu ku tafi asibiti ,kai kuma bashari zo mu tafi wajen yan sanda" Hakan kuwa akayi kawu shehu suka tafi asibiti,wanda ganin zasu tafi yasa inna larai dauko gyalenta tabiyo su har waje,saida baba umaru yasaka baki kafin kawu shehu yabar ta bisu asibitin,saida tayi ta rusa musu ihu tukunna aka barta ta tari mashin tabi bayansu. A wajen su baba umaru kuwa,saida suka bi layi tukunna suka samu layin yazo kansu,dan sandanne yakalli su baba umaru amma idon sa yafi tsayawa akan bashari da alama yaganeshi, "Malam muna tsaye amma bakace mana komai ba" "Eh ina jinka menene yake tafe daku" Saida suka tsara masa, abinda yake faruwa tas kafin ya yamutsa guska yace, "Hakikanin gaskiya babu inda zamuje kamo wani dan ya taba wani mutum a gidan gandu,saboda kuma da wani a cikin gidanne ya aikata mukaje kamoshi da kyar zaku bari dan sandan yafito da ransa in ya fito ma to saikun sanja masa kamanni kuwa. Toh fah yadai gidan gandu?? ❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤ Kar ku manta da #comment #share #like #follow. ____** *GIDAN GANDU* **____ ❤❤By sadi-sakhana❤❤ Wattpad username:SAKHNA03 *wannan shafin sadaukarwane kwacokam ga,@sumayya yarima,@Aisha dakuma @hajiya,allah yabar kauna ga duk masoyana,hakika ina godiyah sosai* Bari muga nagaba kuma😀😀😀😀 ❤03❤ "Baba kayi hakuri fah dan yayan gidankune suka jawo,lokacin da mukaje kamo manjo dan gidan malam IDI a gidan ya saci mashin din wani saurayi kuma yayi masa duka,naga wannan shegiyar yar takace ta aiko mana arnan yaranta sukayi mana faca faca da ofishinmu,waima dan bata gari ba da kanta tazo ba,dan haka babu inda zamuje,in labiru kuke zance ma,dazu wasu samari suka kawomana kara wai sun nemeshi sun rasa a baking rafi lolacin da suke shan rake dazu,dan haka ku tattara naku ya naku kubar nan wajen tun wuri" Cikin sanyin jiki na rashin sa'a suka bar wajen,wanda dama shi bashari baiyi magana ba,inda wajen tsara yan matane da bleaching toh ya rufe kofah,amma harkar yan sanda kam,matsoraci ne shi sosai na bugawa a taro. Fitowa sukayi daga police station suka tari acaba wanda zai kaisu asibitin da aka kwantar da hanifan,nan ma saida akayi ja inja da mai adaidaita sahu kafin ya daukesu,suna cikin tafiyane bashari yagyara zama yafara magana wacce baiyi ba tun sanda aka shiga police station din, "AI baba umaru in fada maka,mutanennen basuda imani,cewa muka cemusu anyiwa fah yarinya fyade amma ji yanda suke wani nuna halin ko inkula,hmmm abin duka babu sanda" "Dallah can yimin shiru da fuska kaman ta sabuwar fatalwa,waiku adole yan gayu,duk kun shafa mai kun mele fuska kaman wanda aka bi da dutsin guga,zaka ce wani abin duka babu sanda in anbaka sandan uban me zaka iya idan an baka sandan,akwai abinda ka iya ne banda shegen zuwa wajen yan mata,duk wani dan kudinku anan yake karewa da kuma sayen tsukakkun wanduna" "Kai baba umaru ku bakwa gane zamani,idan ta ganka baki babu wanka ai babu rabin zance,ai idan ta ga fuskarka fara tas ga kuma wandonka irin sabin gwanjonnan yanzu zakaga ana love wallhi in ba kaiba sai rijiya" "Kai bashari zaman mu lafiya kayimin shiru anan wajen tammmm" Shiru kuwa yayi da bakinsa bai sake cewa komaiba har suka iso asibitin da aka basu gadon. A wajen cashier suka hadu dasu inna larai a tsaye suna jiran layinsu ya iso saboda ganin likata(kasar tamu kenan allah yah ya fiddamu cikin wannan hali). Kudin wajennasu bai isa ba ,saida baba umaru yaciro guntun sanjinsa kafin aka bawa mai karbar kudin. Bayan sun samu an basu gadone,baba umaru yah kalli kawu shehu yana mayar masa yanda sukayi da yan sanda a police station dazu,tun bai karisa jin mai ya faruba ya fara masifa saboda tsabar ransa ya baci, "Hmm dama nasan za'a rina,wai an saci zanin mahaukaciya,duk sun bata yayannan basuda aiki sai jawo magana acikin gari,kowa acikin su bayason laifin dansa toh yanzu wa gari ya waya ,gatanan ina tatura yarinya kwadayi anyi mata aika aika tabar mutane da wahala" Inna larai ce ta goge idanunta da yacika da hawaye ta dubi kawu shehu cike da masifa tafara magana, "Kai shehu ya isheka haka,kawai zaka samu mutane da shegiyar masifa,zaka ce wani mun b'ata y'ay'a ,aikai suka iyo kaidin na allah ko kanace bamusan mai kake aikatawa,dama wanda yayi ai sai anyi masa,kuma dama kyan d'a yagaji ubansa,kai suka iyo,dan haka kadaina wani jingina laifin akaina eheee" Kunyace takama kawu shehu ganin yanda inna larai tafere baki ta masa wankin babban bargo da masifa kaman d'anta gashi dakin Da'aka kwantar dasu da mutane. Sallama baba umaru yayi musu ganin yanda abin yafara zama na tone tone maimakon zaman jinya,fatan samun lafiya yayi musu yai hanyar gida na fatan allah ya kyauta aransa. Yana shiga gida inna RAMATU(matar baban SAMEEMAH ,uwar su sameerah )ta tari baba umaru da barka kaman ba itaba,da Mamakin sa yah kalleta saidai ya boye baice komaiba,ruwan sanyi ta kawo masa da shinkafa fara da mai da yaji da akayi da ranar. Saida yah wanke hannun sa

Table of Contents

Chapters

55 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});