Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 46

Chapter 46

Gidan Gandu Book 1 Complete Hausa Novel 1,260 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

akeyi tsakanin sameemah da saurayin,saurin mike wa yayi yana gyara wuyansa wanda ya bada kara kakkkk,dantsensa ya daga yana murdawa domin bata tsoro,ba karyah kam namiji ne majiyin karfi wanda zai iyha firgita duk wanda yaga dantsennasa amma babu alamar hakan daga wajen sameemah,saima kara matsawa da tayi tana bashi waje ya gama motsa jikin. Cikin sauri yah shammaceta ya kinsa mata naushi a fuska saida ta juya,dago da fuskarta ta tayi tareda yimasa murmushi kaman babu abinda yah faru,wani naushin yakara kawo mata inda tayi saurin rike hannunsa da nata hannun,jijjiga hannunsa yayi da niyyar janyewa amma yayi yayi yakasa kwacewa,mitsitstsikawa tayi sai ji kake kururrs kurus. Wata kara ya sake yana kallon yanda yatsuna hannusa suke kokarin tashi a aiki,amma duk da haka yah kara kawomata daya hannun,wannan karon ba iyah Yatsun ta karya ba harda tsintsiyar hannun,sannan ta kara masa da wani duka a akan gwiwarsa hakn yasa Ya zube a gabanta akan gwiwoyinsa, "Yanzu mai zaka ce game da aikina,koh kana da wani saurin bayanin da kake son isarwa gareni,idan kuma karaya uku bata isheka ba saina kara maka wani ,hadda wani kawo naushi da karfi kuma wai ga mace koh kunyah bakaji ma" Saboda ranar ba wani bacin rai takeji ba dan ma taji furucin da yayi ne,gashi a aikin banza yah jawo wa kansa duka. Dakin da aka kai su kawu shehu ta nufah,suna hada ido da shi yayi saurindauke kai, "Zaku Zauna anan za'a dan yimuku horo kafin kowa yah tafi gidansu,wanda kuma suke a wani garin za'a saka su motar garinsu" A wajen park din motarta suka hadu da wanda yake kula da saurayin da yah sha dukan, "Yawwa kaje ka duba shi ayi masa dorin karayarsa zuwa gobe zamu kaishi wajen yan sanda" "To shikenan sai gobe toh" Daga haka ta bar office din ta nufi gida. Tun a bakin kofar shiga gidannasu da hangi sameerah suna fira da ummaruje sai wani sunne kai takeyi itah a dole ga mai kunya,shikuwa har wanj lekata yakeyi yaan dariyah. Tun kafin ta fito daga cikin motar ta karemusu kallo tass,duk da abin yabata mamaki amma kawai tah watsar abin aranta dan bata ga dalilin sake tunawa dashi bama. Kashe motarta tayi kafin tazo bin ta kusa dasu zata wuce,hakan bai ishi sameerah ba ko tana tunannin bata gansu bane,?oho "Lah sameemah kin dawo ne,ga ummaruje ku gaisa mana,tun dazu nake cemasa bari kizo ku gaisa amma yace wai na daina yimasa zancenki amma bari kiji daga bakinsa ma" "Ahah basai najiba nima ban nemeshi ba ai,dama kece kike neman na hada ki dashi nacemiki idan kika nemeshi kuka gaisama babu abinda ya shafeni gashi kuma kun gaisa din na gani,kuci gaba da gaisawarku kawai" Har sameemah ta saka kai zata wuce kuma sai sameerah ta sake cewa, "Naji ummaruje yace wai dama ke kika je har gidansu wajensa koh?" Abinne yabatawa sameemah rai dan rainin hankalin yakuma fara isarta ga kuma gajiyah da ta kwaso yau din,komawa tayi har wajen, kafin ta kankance ido ta fara cewa, "Ke sameerah wallah in baki rabu dani ba ranki zai baci,me kike nufi shidin daya fadamiki yana tunanin wajensa najene?toh ki fadamasa duk da naga kaman wannan bashine a gabana ba tunaninsa yana wani wajen daban,wannan gangar jikice,toh idan yadawo hankalinsa kice masa ba wajensa najeba,wajen ubansa naje domin yi masa gargadi,kuma dama koda bai fita a rayuwata ba zan fitarda shi,dan ko a farcen kafar mutum din da zai iyah rayuwa dani bai kaiba,sannan ke kuma ...........hmmmm ban ma yi hakuriba ki shigo gida kisameni kawai idan banyi bacciba. Kwafah taja babba saida sameerah taja da baya kafin ta bar wajen zuwa cikin gidan. Yawwa shirin yayi aiki akan ta hankalina ya kwanta tunda yanzu baya ranta kaman yanda bata ransa itama yanzu,shikenan zan wataya saboda nasan nawane ni kad'ai. Fadin sameerah kenan acikin zuciyarta. *+______________________+* *ABIN YABO BOOKSHOP* Kasuwar Rimi Kano Tel:📞 *07038339244* ❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤ Kar ku manta da #comment #share #like #follow. ____** *GIDAN GANDU* **____ ❤❤By sadi-sakhana❤❤ Wattpad username:SAKHNA03 ❤32❤ Tana shiga gidan yara suka fara kallonta har da manyan,ganin kayan dayake jikinta wanda basu saba ganinta dashiba,saboda lokacin data fita da safe basu tashiba bare suga fitarta. Duk da yanda suka kewayeta amma bata kula kowanne daga cikinsu ba,domin abu ne mai wuyah mutum yaganta tana kula wani daga cikin yaran gidan. D'aki ta shiga ta cire kayan kafin tah kwanta,ta dad'e tana tunanin yanda rayuwa take gara mata,amma kasancewarta mace mai nuna juriya yasa babu wanda yasan halin da take ciki. Kiran sallah akeyi amma koh a jikinta ,gashi yanayin lokaci na magriba ba'a son kwanciyah,amma baga sameemah ba kam,wanda sallar ma batayiba bare kuma ta kiyaye lokacin kwanciyah. Fiiiiiiifiiiii kake jin feduwa daga zaure,saida ta bayyano kafin ummah tata ta rike baki,itakuwa zata so taga ranar da surayyah zatayi hankali,da kuwa tafi kowa farinciki. Duk da kallon da umma take yi mata bai sa taji wani koh dar a ranta ba saima kokarin zama da takeyi zata nada labarin abinda yah fafu a wajen aikinnata zuwan farko. Dakatar da itah tayi kafin tace, "Kai mai Sunan manyah,wane zama kuma zakiyi bare bada labari,bakyajin ana ta sallah a masallataine,ki tashi kije kiyi sallah ina yaso koma mainenee zanji daga baya" Kobare fuskar tayi tana dadare da buga kafah a kasa,sai ka ce ba itah ce ta shiga har gidan wasu tah kamo mai laifiba dazu. Da haka dai ta wuce badan taso ba ta tafi yin sallah. Idarwar ta keda wuyah taji wayarta taNa kara,kaman mai kiran kuwa yasan sanda zata sallame sallah. Duba screen din tayi inda sunan burgu ya bayyana a gaban wayar ,dauka tayi tareda murmushi saboda tuna alkhairi dayake mata a kwanakinnan ba dare ba rana. "Aslm yar ummah ya kika shiga gida lafiyah" "Lah lafiyah kalau karamin ogah,yah gajiyar aiki" "Tabi jiki sosai,ki mikamin godiyh a wajen umma mana" "Zataji sosai" Da haka suka cigaba da hirarsu suna ta wasa da dariyah,har zuwa wani lokaci. Tun kafin kowa yah tashi sameemah yau ma tabar gidan. Saidai yau babu wani aiki sosai saboda jiyah kusan suka kammala ayyuka da yawa daga zuwansu. Can wajen rana tana aiki a takardu aka cemata ana sallama da itah,bada izini tayi akan a shigo,bata daga kai tah kalli wanda suka shigo din ba har sai da sukayi gyaran muryah tukunna. Baba umaru ne da Manu da kuma baba munkaila,dayake bayau ta fara rashin mutumci ba fuskewa tayi tana kara daure fuska tareda kishingida akan kujerarta tana juyawa. "Uhm ina jinku mai yake tafe daku?" Baba munkaila ne ya harzuka dayake dama yah fisu zuciyah, "Ke seematu kinci gidanku,wajen ogah daya kama mana dan uwa mukazo bakeba sannan dan rashin tarbiyyah kina kallonmu ko gaisuwa babu ko,wai tukunna ma uban me kikeyi a cikin wajennan dakuma kayan ma'aikata" Duk fadan da yake yi bata cemasa komai ba har yayi yah gama, "Toh malam duk naji bayaninka ,shugaba da kake nema nice shugabar wajen,batun kuma kama dan uwanku da akayi tabbas anyi haka kuma bazan sake shi ba sai yayi kwana uku kaman kowanne masu laifi da muka kama jiyah,ina fatan ka gama jin amsar tambayoyinka,idan kuma basu gamsheka ba zaka iyah tambayar daya daga cikinma'aikatan," Tun kafin ta rufe bakinta kuwa saiga

Table of Contents

Chapters

55 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});