Chapter 11
Chapter 11
yadawo yazama babban dan daudu yan nan yana raba shaddodi da atamfa ,yayah shehu zai koreshi karima ta hanashi" "Toh wata sabuwa kenan,allah yah shiryah" "Ameen dan annabi" "Ina su mustapha kuwa,yayinsu nagani a masallaci shi ban ganshiba" "Hmm mustapha suna d'aki da fitila ta tunda dare yah farayi,wai malamar makarantar safece ta bada assignment kuma gobe zata karba shine sukeyi,tun yamma suke abu d'aya ,wai ance duka ne da itah sosai,ni gaskiya ma har karatun ya fita a kaina bakaga fah yanda suka tashi hankalinsuba kamar ba suba,aka ma d'an mutum a yita duka kaman jaki" "Hmm matsalar damuke fama da ita kenan,allah yah kawomu zamanin da y'ay'a suke samun d'aurin gindi daga wajen iyayensu,yanzu mahaifah sun zama agwagi sai yanda d'a yakeso shi zasuyi,yaushe toh za'a gyara tarbiyyahr yara idan kowa yah boye laifinnasa d'an kuma yanaso ya fad'i laifin d'an wani. Toh ki kiyayeni da zancen hanasu zuwa makaranta,wata rana ai sai labari,kin fison su zauna a gidan su zama irin sauran yaran koh?su da karnuka babu banbanci? Ko bayan raina ban yadda y'ay'a na su tashi sakaka ba babu nunawa yaro dadai kaman goyon gwauro" "Shikenan malam amma da zuwa kayi kace a rage dukan yayi yawa" "Ba inda zanje bazaki bar zancen nan ba koh?,maza ni shiga ciki ki dauko min tuwona,yunwa nake ji" "Allah yah huci zuciyarka malam" "Ameen" Sai can wajen goman dare sameemah tah dawo daga yawonta,kowa yah shiga kofarsa bayan an gama shagalin cin Kayan dad'i Wanda litty yah kawo,tun daga baki kofar dakinnasu takejin shewa ana rangad'a gud'a kamar za a kai amaryah,dan liti ta samu a bakin gadonta a zaune ,sauran yan matan kuma wanda suke nan,suna zaune sun bashi duk hanlalinsu yana tsara musu yanda harkar jin dad'i take ,da kuma abubuwan da mace zatayi ta haska a dunga yayinta,sameerah ceh cikin jin dad'in bayanin da dan liti yayi tai caraf tace, "Banza muke tah bulayi bara a kufai,ashe ga dan uwanmu nan yasan dawar garin koh yah kikace salmah?" "Hakane kam ,ai zamu faso said dai kiji ana labarinmu" "Eh Toh naji kuna so ku haska,amma bazamu shiryah ba idan kuna kirana da d'an uwanku,ku kirani da litty koh kuma sister,yanzudai ku gyaramin wajen kwanciyah said gobe muga yanda za'ayi,ke kuma miye kike tsayeh tunda kika shigo" Dukkan su juyawa sukayi suna kallon sameemah wanda tayi tsayuwar sojoji ganin abinda yake wanzuwa a dakin,tab'e baki sukayi had'e da cewa, "babu ruwanka da itah litty,wannan y'ar bakin cikice,bari mu gyara maka shimfid'in shema'u tunda bata nan satinta d'aya da tafiya har yanzu bata dawoba" Har suka gyarawa dan liti wajen kwana sameemah tana zaune batace musu komai ba saima waya da take yi,kuma a wajen shema'un shine a kusada da itah,dan duk dakin tafi kowa saukin kai da daukar komai ba komai ba,yanzuma ta tafi garin su mamartane wanda bata gidan saboda an basu hutun makaranta,itah kad'ai ceh sameemah take yiwa maganar arziki itah ma kuma ta d'au sameemah tamkar y'ar uwarta ta jini,babu ruwanta da su salma wanda suke uba d'ayah. Saida sameemah tah bari dare yayi sosai,tah gama abinda take,tana wajen tsakar gidan tana jan wiwi a kwarkwaro,saida ta tabbatar tah dau caji mai kyau,tana jinta a can kololuwar sama,inda babu wani shegen daya kaita kafin tah koma d'akinnasu. Saida tah kare musu kallo,kowa ta kula da irin kwanciyar da yayi,kafin tah fito da wata zambad'ed'iyar bulala wanda tah bawa burgu aike yah kawo mata daga gidan horo. Kakkad'ata tayi tak'ara juyata,kafin tayi wani Murmushin gefen baki na mugunta, D'agawa tayi iyah karfinta kafin tah shek'awa dan liti wannan bulalar a gadon bayansa,wata irin mika yayi tareda mikewa tsaye yana k'andarewa, " Shshshs, yimin shiru kuma kayi kneel down,idan kuma ba hakaba wallahi zansa karnukan nan suyi tah yagar naman jikinka" Dan liti yana had'a ido da karnukan masu jajayen idanu wanda duhun dare yasa yake ganinsu kamar kurayeh. Yawu yah hadiye mukut kafin yayi yanda tace, Kara d'agawa tayi tah zambad'a masa iyah karfinta,lokacin data sauke masa tah uku kasa zama yayi ,dan azaba bai san sanda yah dungura ba yana kikkifta ido😂😂😂,(ga mari ga tsinka jaka,@rahama zo ki cece shi keda @chuchu,uhm irin su umma najma kam bazata iyah zuwaba). Jambad'a masa bulalar take tayi gashi ta hanashi kuka ko kad'an ,ganin zata kasheshi kwanansa bai kareba ne,yasa shi takarkara ya zunduma wani uban ihu tun daga mak'oshinsa irin na ainihin gardawan nan (shege ashe yasan shidin na mijine). Su sameerah ne suka tashi a firgice wanda ba iyah su ba ma duk yan gidan ma babu wanda baiji ihun dan liti ba saboda yanayin dare. Samunsa sukayi a zaune sai karkarwa yake ya had'a gumi shirkif kaman anyi masa wanka da ruwa. Ta shi sameerah tayi zata bar dakin domin kiran wani a cikin gidan,saidai cak ta tsayah daga dorah kafafunta a bakin fita daga d'akin,saboda wani mugun gargad'i da sameemah tah antaya mata, "Kina fita daga dakinnan zaki zo kema ko jone dashi ,dan duk wanda ta min shshshigi da itah zan had'a" Tofahhhh ❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤ Kar ku manta da #comment #share #like #follow. ____** *GIDAN GANDU* **____ ❤❤By sadi-sakhana❤❤ Wattpad username:SAKHNA03 ❤09❤ Dukan tsiyah sameemah tayi wa dan liti,tun yana kuka a cikin d'aki har suka fito waje amma bata bar dukansa ba,kowa fitowa yayi dan ganin mai yake faruwa kaman ba dareba, "Zaka sake Shiga dakin mata ka kwanta?" "Ahah bazan sake ba kiyimin rai na tuba" Tsayawa tayi da dukan ,wanda cikin daga muryah inna karima ta fara magana, "Ehhh lallai yau kam abin yayi yawa,dan tsabar rashin mutunci daga shiga daki saiki masa wannan aika aikar,dan kawai kinga kashin arzikin da uwarki har ta mutu bata samuba koh?,toh bazan yadda da wannan rashin mutuncin ba kuma..........." Tun bata rufe bakiba sameemah tasake zabga masa bulalar,tana sake magana ta kara sake zuba masa ita,ganin hakanne yasa inna karima tsuke bakinta tayi shiru,saidai takaici na duniya yah isheta, "Keh karima kike ko ma waye?har yanzu bakisan halina ba koh?,a gabanki dazu da yamma nayi masa kashedin ya dauke kayansa a d'akinmu amma yayi kunnen uwar shegu da ni,ke kuma da kikasan abinda zan iya aikatawa idan na tarar bai d'aukeba kika kasa jamasa kunne. Sannan na dawo nasameshi a dakinmu kuma ma saboda tsabar raini a kusa da gadona wa'ennan shashashan mutanennan suka yi masa shimfidi koh,ba laifinku bane ,laifina ne da na ke daga muku kafa. Toh bari kuji billahillazi daga yau idan nasake kafa doka wani yah karyah ta a gidannan hmmmm,yayi kuka da Kansa koda kuwa bak'one idan yazo a sanar dashi. Kai kuma" Tafad'a tana kallon dan liti, "Iye na'am ina jikinki madam" "Idan nasake kamaka a hanyar dakinmu saina cire maka kafa guda d'ayah,kai koh a cikin gidannan na shigo naganka da kayan mata kana zaune a cikin mata ,saina yi maka hukuncin dayafi wannan,ku kuma zamu hadu daku ,zakusan kun sauke gardi a dakin danake kwana" "Naji Ranki ya Dade kuma inshaallah bazan sake ba ,nidai karki sakemin irin wannan hukuncin,ni gobema zan bi motar sassafe na bar garin bazaki sake ganina ba" "Yadai fi maka" Kowa juyawa yayi ya nufi wajen kwanciyasa aka bar dan liti a wajen yana kakkarwa ,karshe dai a wajen yah kwana. Da safe kuwa kaman yanda dan liti yafada
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55