Chapter 9
Chapter 9
jira abinci, tambayesu kaji data fito tana masifarta wa ta bi ta kanta balle ya tanka, gaskiya ni ba shegiya ba ce da ubana kafi kowa shaidawa tinda Saida ka Kai masa sadakina ya baka aurena, shegun sakararru na inda suke." Tana rufe baki Jamila ta zabura sai tau! saukar mari, Haulatu ta rike kuncinta tace "Kika mare Ni? Wallahi baki isa ba sai na rama, itama ta zaburo tana jiran a dabance, Hayatu yai saurin riketa "Kyaleta Haulatu itace babbar kwabo ta yada girmanta.". Su ma bakin suka bata hakuri, da kyar aka ciwo kanta ta hakura suka iza keyarta ta shiga daki. Maimakon jamilan tayi shuru sai cewa tayi "Ai da Kun Kyaleta tazo ta rama din yau in gwada muku yadsa ake kirba mutum in lallasata in mata dukan da uwarta bata taba yi mata tunda ta fito duniya. Takaici ya kama Hayatu ya harzuka ya dumfareta yace "Bari ni in karairayaki kafin ki lallasata, tana ganin ta dau faskaren icce ya dumfareta ta sheka daki ta danne kofa gudun kar a sabauta ta. Suka bar su Rahima tsirma-tsirma a tsakar gida, yana basu hakuri, suka dawo gida su basu ci abinci ba su hankali bai kwanta ba.. Tun a lokacin bata sake marmarin zuwa ba, gidan Ya Haseeb Kuma iya yin Aunty Zuwaira ke damunta 04/09/2020, 00:24 - Anty saliha: ...RAHIMA...doc by Jami 9 Sauran watanni uku kacal su zana jarabaea akayi bukin Maryam ta auri Alh Abbas dinta, matarsa guda da yara shidda maza da mata suna zaune a sabon fegi. Da alamun Maryam ma Bata dace da Uwargida ba sai abinda Allah yayi kenan domin ita ma ba baya ba wajen kishi da rashin hakuri sam bata yarda a takata ko a wulakanta ta. An dai yi buki an kare lfy babu wani gagarumin tashin hankali sai 'yan kunji -kunji ko Kuma don Alhaji Abbas namiji ne daya iya rike gidansa ba kamar Hayatu ba da ya zama shakulatin bangaro, yayi sake iyalinsa suka fi karfinsa. A kwana a tashi Rabiu da Rahima sun kare jarabawarsu sai adduar Allah yasa ayi nasara. Bayan sun huta na sati biyu ta rokeshi ya kaita gidan 'yaruwarta, ya amince ya dauketa suka tafi. Sun shade awa uku suna hira amma Rabiu bai sa niyyar tashi ba, Maryam tace "Ni fa ban gane ba shin ba tafiya zaka yi ka bar min ita anjima ka dawo daukarta ba?" Ya kwashe da dariya "Kina nufin in koma gida Ni kadai? Gaskiya ba zan iya ba, kafarta kafata." Maryam ta kalli Rahima "Say something kinji Wai ba zai barmu muyi hirar zumunci ba." Ta danyi dariya "To shin din bare ne?" Yace "Kyaleta kawai ta nuna min 'yan ubanci alhalin an zama daya Ni da Rahima. Maryam ta daga Kai "Ai ga alama nan na gani tun zuwanku, Ina ruwan Romeo & Juliet. Yayi dariya "Kuma ba a hanaku ba." "Ah ah Wannan irin soyayyar sai ku yara, Ni mijina tsohone bayan haka ina yaga wani lokacin soyayya Yana can yana neman mana na sakawa a bakin salati." Rahima ta jinjina "Ke din yadda kike?" "To naji na amince Amma don Allah Rabi'u ka tsahirta mana kona rabin awa ne, magana Nike son yi da ita, zancen na Mata ne Kasan akwai sirri." Ya kalli matarsa "Kin amince in tai in dawo Nan da awa guda?" Rahima tayi masa irin kallon soyayyar nan tace "Is okay, nagode." Ya mike ya sumbaci gefen kumatunta "Sai na dawo kenan.". Yana fita Maryam ta juyo gareta "You surprised me, I was impressed Kar dai ince kun kamu?" Ta kishingide ta amsa "Ina zaton hakan Nima, a hankali so da kaunar mijina suka rinka shigata saboda duk da kasancewar sa yaro matashi ya iya tafiyar da al'amarin rayuwar aure yadda yakamata, ko ya fahimci feelings dina ne ya bi duk hanyoyin da suka dace ya mallaki zuciyata, idan kinga irin kishina da yake sai kin rike Baki, ya fara fadin Wai anya zai barni inyi aiki kuwa, ga kulle, idan kuwa ya bari na fita to ki tabbatar da tare zamu fita, ke al'amarin nasa tun Yana ba Hajiya shaawa ta fara nuna damuwa tace tun kafin aje ko Ina zai bullo da sabon al'amari? Ni kuwa maimakon ya dameni ko inji haushi sai dadi nike ji, Ina Kuma ji a zuciyata muddin ya tsaya kan va zanyi aikin ba zan amince don ko kusa ban son abinda zai batawa masoyina rai." Maryam ta kura Mata idi sosai tace "Tabbas kina kaunarsa amma har yanzun da sauranki baki shiga matakin da Zaki ji amsarki ba, akwai sauran lokaci tukunna." Rahima tace "Haba dai duk nike ji dinnan da saurana?". "Kwarai kuwa idan lokaci yayi zaki fada min da kanki, yanzun kashi talatin kike dashi cikin dari kina awo aiki ko rabi baki Kai ba." Ta nisa "Ashe in Kara zage damtse tun kafin bakon dake tafe ta/ ko ya kutso kai ana hanamu shakatawa." Maryam ta bude baki cikin mamaki "Lah kema ciki gareki Rahima? Labarin da zan fada miki kenan Nima, shikenan za mu yiwa Umma tagwaye sunan da take kiranmu." Suka rungume juna suna adduar Allah ta inganta musu ya Kuma saukesu lfy idan lokacin yayi." Bai Kara ko minti guda ba, awa dayan na cika suka ji horn din motarsa suka kalli juna, Rahima ta mike ta dau Jakarta ta gyara mayafinta tace "Mu zamu tafi sai kinzo kenan?" Tace Insha Allah, uhhmm did he know about the pregnancy?" Tace "No but yau zan sanar dashi tunda na tabbatar" Suna fita Maryam ta riko hannunta ta mika masa tace "Rabiu manya, to ga matarka, ban cinyeta ba balle in gutsuri namanta " Ya sosa keya "Ba haka bane Aunty... Ta katsesa "Kwarai na fahimta to Allah ya bamu alkhairi, sai nazo." A wannan ranar wani sabon nishadi ya rufesu suka jima suna hirar soyayya kasancewar a ranar suka shekara daya cif da aurensu, sunyi nafilfili da adduoin godiya ga Allah SWT kana suka kwanta. Bata yi hanazarim shaida masa batun cikin ba Saida dare ya tsala ta tashesa daga barci, ya tashi ya kunna fitila ga zatonsa ita a bata da lfy yace "Lafiya? Ta kura masa idanu tana nazarinsa, duk da cewan barci ya farka yai Mata wani irin kwarjini, fuskarsa sai sheki, ya Kara kiba da haske, tayi ajiyar zuciyar, Rabi'u yarone matshi amma girman jikinsa kansa ayi kuskuren shekarunsa, suna mugun kama da Hayatu sai dai ya darashi tsayi da jiki, Hayatu farine mi yar doguwar fuska,mutum ne Mai fara'a da son mutane ga ban dariya, kusan ko yaushe ka gansa hakoran nan bude suke Yana dariya, da wuya ayi masa Abu ya bata masa rai har yai fushi, wadannan kyawawan halayen nasa yasa yake da jama'a da abokai babu iyaka. Ya kagu da kallon da take masa ya girgizata "Wai shin lfy. Tayi "yar dariya "Hakan nan kawai kwana nan sai inji kana matukar burgeni ko kallonka nayi sai inji wani dadi a zuciyata.". Ya zumburi baki cikin wasa "Kawai kika tasheni barci don ki kalleni kinji sanyi a ranki ne?" "To me zanyi maka da dare Nan, kishi ko yunwa?" Ya janye matashin da take rungume dashi a cinyarta ya maida kansa ya kwanta a wurin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66