Chapter 48
Chapter 48
zai amsa, idan aka nemi jin kansa dasu zai yi jin Kan, idan aka nemi yayewar tsanani zai yaye.. Ki tabbatar da kafin ki fara kowcce adduar kin fara gabatar da shimfida, watau istigfari da salatin Manzon Tsira, idan kin kare kuma ki sake rufewa da salatin. Idan zaki yi addua ki rinka girmama rokon, ki daukesa da muhimmanci, ki rinka na ci, sannan ki dunkule bukatarki ki roki Allah Kai tsaye, ki yawaita tuba da yin adduat tare da sauran jama'ar musulmi Kar kiyi ta rokon ke kadai. Babban muhimmin abu game da addua shine tawali'u da rage aikata sabo da tarar lokuttan da aka yi nuni ana amsar addu'ar. Misali idan cikin dare ne tsakiya da karshensa don ance a wannan lokacin ne Ubangiji ke tashi da kansa yana Kiran Ina me neman biyan bukata in biya masa.. Kinga Wanda duk ya dace da wannan lokaci yayi kyakkyawar sa'a.. Akwai farkon asubah da karshenta, sai lokacin da mutum ya fuskanci abokin gaba wajen yaki, lokacin saukar ruwan sama, bayan kiran sallah da tsakanin kiran sallar da tada ikama, ko ki fuskanci alkibla ki rokesa, amma inda Ubangiji yafi amsar addua shine yayin da bawa ya kaskantar da kai cikin sujada ya roki Mai dukan zai amsa. Saboda haka yanzun ma ki tashi mu gabatar da sallar nafilar da ma'aurata keyi mu nuna godiyarmu ga Ubangijinmu da ya kaddaremu yin wannan aure, mu rokesa ya tabbatar mana da dukkan alkhairinsa ya kade mana kiwanne irin sharri. Ta mike tsaye ta saka hijab dinta suka natsu, ya shiga gaba ta bi bayansa suka gabatar da nafilar, bayan sun idar ya juya gareta ya dafa kanta ya sake rokan Ubangijinsa alkhairinta da neman tsari daga sharrinta, daga nan ya umurceta da suka karanta suratul Ikhlas kafa 3 ko11 suyi taswili zuwa kabarin Rabiu, iyayensu da dukkan musulmi da suka rigamu gidan gaskiya. Duk hakurinta ta kasa danne zuciyarta tunanin Rabi'u da mahaifiyarta da bata taba sani ba a rayuwarta. Kuka take Mai tsuma zuciyar Mai saurare, hankalinsa yai dubu ya baci, ya fara rarrashinta "Rahima kiyi hakuri Allah ya gafarta musu, meye na zubda hawaye bayan munyi musu addua shi suke matukar bukata daga garemu" Hawaye ya rinka kwaranya daga idanunta, ya mike tsaye cikin damuwa ya kamata suka shiga toilet "Ki Yi hakuri ki daina kukan nan haka, wanke fuskarki." Ya umurceta. Tayi abinda yace, suka dawo dakin, ya zaunar da ita a bakin gadon ta zuba tagumi, ya fita dakin, zuwa can ya dawo dauke da babban tray dauke da warmer da plates da kwalin mango juice dana fresh milk da cups ya dire a gabanta yace "Kinga ni yunwa nike ji tun rabuwarmu ban ci komi ba, sauko mu ci abincin." Bata musa ba saboda itama yunwar take ji, cikinta kamar an washe mata tas! Ta bude warmer din, gasashshen nama ne irin Wanda ba'a bari ruwan jikinsa ya kafe dinnan, sai kamshin kayan yaji, ga tumatur da albasa an yanka kanana, miyaunta ya tsinke tun kafin ta saka yanka daya baki,, ai tana taunawa Saida ta lumshe ido saboda dadin naman, Maggi da gishi sun kama radam... Kallon reaction dinta yake yana murmushin nan nasa, sai da yaga ta sake taunawa ta hadiye yace "Yaya, yayi dadi?" Ta gyada Kai "Don Allah a ina aka samo ne?" Ya girgiza Kai "Sai mun cinye za kiji." Ta zage taci naman nan har ta fi shi, ya zuba mata madarar ta shanye tayi gyatsa tayu hamdallah harda sude hannu. Suna karewa ta yunkura zata kwashe kayan, ya dakatar da ita da "No yau aikina ne, bari in Kai in dawo in baki labarin inda na samo naman." Ya fita ta bi bayansa da kallo tayi zugum. 'Anya wannan rawar jikin da Ya Haseeb keyi yau baids wata manufa can karkashin zuciyarsa kuwa? Ah to ta gane mana, cin nama banza ne da dare balle ga ango da amarya?" Ba'a jima ba aka dauke wutar lantarki sakamakon kakkarfar iskar data taso hade da saukar ruwa mai karfin gaske hade da tsawa mai firgitarwa, ga walkiya na gilmowa har ta cikin window dakinta.. Rahima ta tsorata ba shiri ta haye bisa gado ta kudundune kanta cikin pillow tana salati. Dakta ya dawo dauke da wata 'yar torchlight a hannu yana haskawa, yana shigowa ya maida kofa ya rufe, ya Kara tabbatar da duk windows ma rufe suke sai yan ragar da iska ke shigowa tunda ba kura, yace "Yanzun Malam Hassan zai kunna gen gidan yayi duhu ko?" Ba amsa, ya haska ya ganta a kudundune, ya karisa yace "Rahima mene kuma ke damunki yanzun?" Bata dago ba ta amsa "Wallahi Allah ya hakicce ni da tsoron tsawa sa wal .. bata karisa ba, aka buga wata tsawar ratsa--tsa-tsa...walkiyar ta gilmo cikin dakin, ta saki pillow ta cakumeshi ta rike gam tana makyarkyata... Dariya ta kama shi "Ni ban taba ganin matsoraciya irinki ba, maimakon ki rinka karanto adduoi sai ki rinka boye fuska?" Ta Kara cusa kanta a kirjinsa tace "Me zan karanta?" "Ya kwantar da ita tukunna ya fara rada mata "Cewa za kiyi *tsarki ya tabbata ga Allah Wanda tsawa take tsarkake shi da yabonsa da mala'iku don jin tsoronsa* A hankali ta rinka maimaitawa har taji tsoron ya gushe, to sai Kuma me? Sai fahimtar halinda take ciki, gaba daya jikinsu manne suke, kunya ta rufeta, ta nemi juyawa ya rada mata *Kin San hukuncin matar data juyawa miji baya ko* Bakinta ya mutu, magana ta gagara sabida yanayin data tsinci kanta ciki, jikinta yayi likis, kasala ta rufeta, tunda ya gane ta bada kai bori ya hau, daman ya riga ya hau tudu, gangara kawai yake nema, sun hade su n manne da juna, sun shiga rudani, gaba daya ji sukai tamkar basu taba wani rayuwar aure da kowa ba sai yanzun. Suna cikin yanayin ana ci gaba da zabga ruwan sama, tuni Rahima ta manta tsoron tsawa da walkiya, shi kuwa addua yake yana kara godewa Allah daya nufesa da auren daya daga cikin matan da ake Kira *SA'IDA* Lokacin da ruwan ya tsagaita barci ya rinka fisgarta ta rinka mashalo ita ba barci Mai nauyi na ita ba a farke ba yayinda ya rinka kallonta cike da so da kauna maras misaltuwa. Cikin dan barcin daya sure ta tayi mafarkin tana tsaye bisa wani tsauni tareda Haseeb da Rabi,'u, zuciyarta ta cika da murna da farin cikin ganinsa, ta matsa da hanzari domin ta kamo shi amma tana isa kusa yaja da baya, ta sake bin sa, ya tsaya ya riko hannunta ya matsa kusa da Haseeb shima ya rike hannunsa ya hada da nata ya manne yace "nagode daka rike amanar dana baka, ka rike matarka da kyau...ya juya gareta yace 'Ke Kuma ki bi mijinki zaku kasance cikin amintattun masoya da suka samu ingancin aure.. Mamaki ya hanata magana sai kokarin riko shi take yana ja baya har ya bace daga nan wani mashahurin haske ya lullubesu ita da Haseeb .. Ta farka babu inda jikinta bai kyarma saboda gigita, tunda ya rasu bata yi mafarkinsa ba sai yau, ta rumtse ido ta karanto *Allahumma innee a'uzu bika min sharri maa ra'ayta fee manaamee wala yadhuru nee fee deeni wa dunyayaa* Nan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66