Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 64

Chapter 64

Rahima Book 1 Complete Hausa Novel 1,209 words 0 views Progress saved
Download Book

baiwa ce meye problem dinta kuma tunda ta dade da tsunduma cikin kogin soyayya mai zurfi da fadi, ta kurbi ruwan kogin da ya kunshi dandanon zuma, gishiri da madaci, tasan dandanon zakin zuman soyayya, ta shaidi gardinta ta hadiye tsaf har da neman kari, wajen dandanon ruwan gishirin ma ta hadiye rabi ta watsar da sauran, ya rage sauran ruwan madacin data guntsa cikin baki yana kokarin shigewa cikin makoshi tana kokarin fiddo shi don ko alama wadannan ruwan ba ruwan sha ne a gareta in dai domin soyayyarta da Haseeb ne. Tayi ajiyar zuciya, so in har tana so ta amayo wadannan ruwan madaci da suka riga suka gauraye bakinta ya zama dole ta warware problem din dake tsakaninta da mijinta. Ta tashi ta nufi bedroom dinsa tayi knocking ta tura kofar a hankali. Kwance yake ringingine ya dora dukkan hannyensa ya dafe goshinsa, dim light din dake dakin bai hana ta ganin yanayin dake yake ciki ba, ta matsa ta zauna gefen da yake kwance, sanyin air condition da kamshin turaren *Emotion* da qira'ar sheikh Abdurrahman Sudais suka da yake saurare cikin suratul Rahman suka sanya mara wani irin natsuwa cikin ranta. Bai nuna alamun yaga shigowarta ba ma balle ta tanka, hhmmm tasan halin gogan nata, miskili kafi mahaukaci ban haushi but ko shi ana janyo ra'ayinsa da rarashi da dabara, idan haka dole ita ta ajiye nara miskillancin a gefe... Ta Kira Ya Haseeb can kasa so very softly.... Cikin muryar data sakar mata kasala yace "Lafiya ba kiyi barci ba har yanzun?" Ta Kara sassauta murya "Abinda ya hanaka barci shi ya hana min.". Ba tareda ya motsa ba yace "In har akwai problem dake damuna kin sani, so nagode kije ki kwanta." Tsawon minti biyar ta rasa yadda zata bullo ya saurareta abu ya faskara saboda bai yi niyya ba.. Ta mike tsam, a zatonsa ficewa zata yi... Zuciya ta kule shi ya rumtse ido, tabbas Rahima kan dole take zaune dashi... Ta matsa daf dashi ta duka ta riko hannunsa na dama ta dora bisa cikinta tace "Da ni da abinda ke ciki muna matukar bukatar kulawarka, idan ka juya mana baya yanzun zamu zama abin tausayi, kaine bargon dake lullubemu da so da kaunarka, yanzun ji nike tamkar wace aka sabule fatar jikina na zama exposed to sanyi, rana, iska da kowace irin cuta domin rashin kyakyawan kariyarka. Please do forgive me, Ya Haseeb baka san irin nauyinka da nike ji ba, kwarjini da muhibbanka na cika min ido har yasa komin rashin kunyata ba zan iya tunkararka da wani zancen Kai tsaye ba, Allah yai maka wannan baiwar, still Iam so sorry I didn't mean to hurt you." Kalamanta suka rinka ratsa shi suna shigarsa ya rinka jin wani ni'imtaccen sanyi cikin zuciyarsa da kokon ransa. Farin ciki ya taso ya shafe radadin dake kewaye da ruhinsa. Cikin hanzari ya bude idanunsa ya ganta tsugunne a gabansa, ya yunkuro ya tashi jiki na kyarma ya rungumota, suka sauke wani gwauron numfashi tare da sumbatar juna.. Ya sassauta rikonta ya lakace mata hanci yace "I have only one weakness my dear...and that weakness is you please don't take advantage of it to hurt me." Rahima ta Kara makale mijinta tace "You're my love, my life and my everything Ya Haseeb." Duk da cewan sun taba zuwa Maiduguri wannan karon tafiyar ta musamman ce domin sunan diyar aminiyarta Hjy Fatima suka tafi, sai dai kash Yayan nata yai mata na 'yan duniya,suna isa garin ya shafawa idonsa toka yaki yarda ta sauka gidan aminiyarta dai *Lake Chad Hotel* inda yai musu booking *V.I P Suit* Bayan suna da kwana da biyu suka shiga ciiin birnin na El-Kanemi. Tun zuwanta na farko Rahima ta yaba da birnin sosai musamman karamcin da 'yanuwan Hjy Fatima da mijinta Alh Ahmad Sheriff suka nuna Mata, basu manta da alkhairin Dr Haseeb da matarsa suka yo musu a Kanon Dabo ba. Daman ai shege kadai ke manta alkhairi. Kwanansu uku suka sallemesu da dimbin alkhairi, kyautar turarukan wuta da humra da lapayoyi saida ta kasa godiya. Daga can Bauchin Yakubu suka yiwa tsinke wai zai kaita ta gani abokansa da suka yi makaranta tare suka Kuma dade basu ga juna ba. Suna shiga garin, Rahima taji wani irin natsuwa ta musamman na shigarta, hakika Allah ya albarkaci jihar da wani irin kwanciyar hankali mai shigar baki irin yadda taji a ranta. Da ganin yadda jama'ar garin ke Kai kawo cikin sukuni bisa titi kasan jihar na daya daga cikin jihohin Arewa da Allah ya karesu daga hargitsi da tashin hankali. Kai tsaye gidan abokinsa dake cikin gidajen jamiar Abubakar Tafawa Balewa suka wuce inda suka sami kyakkyawar tarbo daga iyalin shahin malamin. Nan aka barta da muhawara da zuciyarta kan cewan tsakanin mutanen Bornu da Bauchi su wa suka fi karrama bako? Gaba dayansu suka fita gari din ba ido abincinsa, cikin University suka fara shiga, suka nufi fadar Mai martaba Sarkin Bauchi Allah yaja zamaninsa, daga can sai Yankari Reserved, Zaranda Hotel nan ma zasu gaisa da abokinsa, matarsa da Rahima suka wuce kasuwar Wunti domin sayayyar tsaraba Tsarin garin ya burgeta, ta rinka kwatanta wajen yawon bude na Kyarimi park dake Maiduguri da Yankari Game Reserved, duka jihohi biyun sun bata sha'awa, wajen alkhairinsu kuwa tsakaninta da jama'ar garuruwan sai adduar da fatan Allah yai musu sakayya, ta Kuma gode da kauna. 22/09/2020, 22:36 - Anty saliha: ..RAHIMA..doc by jami 53 Kwanci tashi cikin Rahima ya isa haihuwa, Ubangiji ya kawo nakuda da haihuwar cikin sauki saboda tsananta adduoi da suke tayi, ta haihu a gida tareda taimakon kawarta nurse Shafa'atu da Auntyn ta Zuwaira, ta haifo diyarta mace sak kamanin Dakta. Murna da farin cikin 'yanuwa da abokan arziki bai faduwa, Uban kuwa dawowa gida kawai yayi ya tadda mai jego da diyarta, yayi kamar zai lashe su, gashi Allah ya jarabce shi da son diya mata. Ba tantama Hajiyarsa aka yiwa namesake "Ummulkurthum. Ana sauran kwanaki kadan su cika arba'in aka wayi gari babu Alh. Muhammad mahaifin Zuwaira. Wannan babban rashi ya girgiza Haseeb fiye da kowa, Zuwaira taci kuka har ta gode Allah, ta rame ta fige tayi baki duk ta lalace, mijinta da 'yaruwar zamanta suka rinka bata magans tareda nasihohi har ta dangana taci gaba da yiwa Allah godiya da ya nufeta da shiriya ta rokesa gafara ya yafe mata kullum yana sanya mata albarka kafin Allah ya amshi rayuwarsa. Gaba dayansu suka nufi aikin Hajj da shekara ta zagayo, inda Rahima ta sauke farali, Haseeb da Zuwaira kuwa sun taba zuwa. Tana yaye Muhibba ta nemi iznin komawa B.U.K yin masters, ya amince saboda sanin muhimmancin ilmi bai tauye ta ba taci gaba da karatu. Tana cikin shekara ta biyu a makarantar ta sake haihuwar mai sunan Ummanta Habibatu suna kiranta Ummi. An haifeta ba jimawa Zuwaira ta samu nata rabon itama ta haifi Ummul Salama. Allah mai jin rokon bayinsa kenan, Haseeb ya roka an amsa, ya bashi 'yan mata uku reras sai fatar Allah ya raya masa ya shiryasu hanya madaidaiciya. Tunda Zuwaira ta daina fita fita zuwa Dubai da Saudiyya yawon saro kaya suka sake hada gwiwa da suna ba Hayatu yana dauko musu kayayyakin da

Table of Contents

Chapters

66 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66