Chapter 37
Chapter 37
tace "What's so hard to believe? Mijinki mutum ne mai saukin Kai, ga wanda ya fahimcesa,Nima dane nike masa muguwar shawar but mu'amalar da muka yi na dan lokacin nan na fahimce sa sosai kema zaki fadi more nan gaba." Tace "Hhmmm ni ba abinda ke damuna illa yadda zan kallesa a matsayin mijina idan ya dawo, gaskiya ban san abinyi ba." Ta kyalkyace da dariya har tana kwalla "Kenan Ni zan fada miki abinda za kiyi? To tunda abin ya zama haka bari ya dawo shi zai sani." Tana gama magana tayi gaba ta barta nan, dole ta rufe kofar falonta tunda maigadi ya rufe gate Maryam na tafiya. Ta leka dakin da Uwale take taga har tayi barci... Ta shiga bedroom dinta ta shige toilet inda ta sake yin wanka ta dauro alwala, ta fito tayi haramar sallar nafila., tayi adduointa ta kare kana ta haye gado da niyyar samun isashshen barci don wartsake gajiya, amma barci ya gagara, har zuwa karfe ukun dare tana juyi dalilin kekashewar da idanunta suka yi, ba alamun barci ko kadan Tunanine ya addabeta, to yanzun ita Rahima ta tabbata matar Yaya Haseeb kenan ko, shin akwai wadanda Allah jarabta irinta kuwa? Anya rayuwarta zata taba komawa normal? Yes ta sani kowacce rayuwa da irin kaddarorin da aka rubuta mata, yau kaga fari gobe baki, yanzun yau kaga abinda kake so gobe ka samu kishiyar hakan, yau murna gobe ko jibi akasin hakan ba don komi ba sai don Mahakiccinmu ya gwada karfin imaninmu da kasancewar bawa bai taba dauwama cikin abu guda. To ita a matsayinta na musulma wace ta yarda da kaddara mai kyau ko maras ya zama wajibi a gareta tasa hannu biyu ta rungume ta duk da kasancewarta mace mai rauni. Tunanin marigayi suka kutso Kai daidai lokacin Wanda ya haddasa gudanar hawayenta suka fara jika pillow, Allahu Akbar! Ta fadi a fili, rahamar Ubangiji ya ni'imta makwancinsa, sunyi rayuwar aure ingantacce duk da sunce zo mu zauna zo mu saba, zamantakewar su abin koyi ne ga ma'aurata, Bata taba tunanin aurensu zai zo karshe da wuri ba, Amma kash! Mai katse dukkan wani hanzarin mutum ta kusanto ta rushe dukkan ginin da suka fara dorawa... To shin yanzun zata iya dora wani tubalin don gina sabon rayuwar aure da Yaya Haseeb? Idan tasan zuciyarta tasa fa? Ya zata iya tarayyan miji da Aunty Zuwaira gashi tun ba a kai ko ina ba ta fara jin sabanun da ya shiga tsakaninsu? Ta juya gefe guda tace Oh Ya Allah gani gareka, kai ka kaddaro min auren nan , Kai kasan dalili, Ina rokon ka tallafa min tafiyar da al'amarin auren nan nan cikin sauki tareda jagorancin ka. Bata samu barci ba sai bayan data idar da sallar asubah, ta sureta kenan aka Kira wayarra dake kusa da itaa Ta dauka ta sallama ido a rufe. Amsarsa tasa ta bude tangaran.."Ba dai na tashe ki daga barci ba ko?" Ya tambaya bayan amsa mata sallamarta. Shock ya shigeta faras daya, zuciyarta ta fara ras-ras... "Are you alright? Ya sake tambayar ta amsa da Kai, nan take ta tuna bai ganinta tace "Komi lafiya." "Ban amince ba, your voice is very low what's wrong." "Wallahi ba komi." Ya amsa "Hakan dai kika ce, anyi sha'ani lafiya ba wani problem ko" Rahima tace "Aljamdulillah." Is the house ok?" Ta sake amsawa a natse. Daga daya bangaren Dr Haseeb ne ke tuhumar me yasa take bashi short answers,wata zuciya tace baka disconnecting wayar ka huta tunda ba hirar ya kirata suyi ba, a nasa tunanin ma gaisawa kawai za suyi but ya kasa aje wayar ya rasa kalmar fadi Kuma sai kame,-kame. Ya nisa ya sake tambaya "Ina Abdul? Yana lafiya ko?" "Yana wajen Unma." Yai shiru yana murzan goshinsa da yatsu biyu, ya rasa dalilin kasa aje wayar, dalili ya wuce matsayinta na matarshi da son cika amanar da ya dauka? Can yaji muryarta tana tambayar "Ya patient?" Ya amsa "Alhamdulillah, he's progressing well, nagode. "Masha Allah Ubangiji ya bashi lafiya." "Ameen bari in barki ku huta zan kiraki gobe Amma idan da abinda kike so ki yiwa Hajiya magana.". Tace "Ba wata damuwa insha Allah may be dai inje in dubosu zuwa jibi." "A ina kika taba ganin amarya na yawo? Ki bari saina dawo mu tafi tare." "Ta amsa shikenan." "A shafa min kansa, nagode. 🦈🦈RAHIMA🦈🦈 28 Ta sauki mintoci heart beat bai koma normal ba, watau a takaice so da kaunar Ya Haseeb na neman mamaye mata ruhinta, ta girgiza Kai wannan ma ai shine abin kunyar, hhmmm da zai fahimci haka ya zai dauketa, maras tunani ko maras matunci? In kuwa hakane gara ta yiwa kanta rigafi ta danne zuciyarta zai fi mata alkhairi. Ba sauran barci a idanunta don haka ta fito daga dakinta ta nufi kicin inda ta taras da Uwale harta kama aikin hada breakfast, tana ganin Rahima ta durkusa ta gaisheta "Hajiya barka da fitowa." Ta amsa "Ina kwana Uwale ashe kin tashi tun dazun." Tayi dariya "Ai mun saba, a can kauye ina muka ga lokacin barcin safe, muna alla-allah bayan munyi sallah mun karya kummalo da dumammen turo mu zuba hatsi a turmi mu shiga neman na abincin rana mu da yara.. Rahima tace "Gaskiya kuna kokari,kuna wahala, shiyasa akace mutum ta rinka kallon na kasa da Kai, nan zaka gane ni'imar da Allah yai masa sai Kuma ka gode masa don wasu sun fi kane Kai Kuma kafi wasu, amma gaskiya idan kika duba rayuwar matan karkara sunada matukar tausayi, sai muce mu aljanna muke." Uwale ta nisa "Ina ma ki kasan haka Hajiya, sai Kinga macen kauye a ce miki sa'arki ce ki yita rantsuwar ba haka bane don ta kusa haihuwarki a fuska, ta tsofe ta komade saboda wahala, hakora sun zube, ba isashshen ingantaccen abinci, ba hutu, na kyakkyawar muhali balle wani sutura mai kyau ga rashin samun kulawa daga mazajenmu, yawanci mazanmu fa basu San darajar mace, iyakar ki dashi ki dafa abinci, wata har noman abincin ma da ita za ayi, kiyi surfe da daka, idan ya bukaceki ya sarrafaki kamar yadda yakewa jakarsa da yake kiwo,idan kin dauki ciki ki babu wani kulawa, wajen haihuwar ma wani a rabu kacar sabida yaushe ya barki Kika je wani asibiti don inganta lafiyarki balle na dan cikin ko jariririn da aka haifa, wasu kuwa don su doki mace ba wani aibu bane a garesu, to mazan nawa ne suka san hakkokin matan da ya rataya a kansu?" Dalili kenan koda mijina ya mutu zawarawa suka yo min caa!! Nace bada Uwale ba, anyi daya ba za a kara na biyu ba, da in zauna cikin jahilci da rashin sanin me auren ya kunsa da rashin sanin hakkokin juna gara in taho birni in nemi sana'a." Rahima ta nemi kujera ta zauna tace "Bari in tayaki aikin mu ci gaba da hirar sai mu karu da juna.. Uwale tace "Ai ke Hajiya Allah ta tarfawa garinki nono, da mata na dacen irin mijinki da ba za suyi kukan komi ba, ko su Mairo da suke 'yan aiki sun shaida balle ku, kin kuwa ji ance kyakkyawar safiya tun daga maraice ake fara ganewa, jumma'ar da zata yi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66