Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 1

Chapter 1

Rahima Book 1 Complete Hausa Novel 1,217 words 0 views Progress saved
Download Book

28/03/2020, 21:32 - Messages to this group are now secured with end-to-end encryption. Tap for more info. 03/09/2020, 10:52 - Anty saliha: *Asslamu Alaikum Wa Rahmatullah Wa BARAKATUHU.* 💕 *A dalilin yawan kira da neman tsoffin Littafaina da Masoyana keyi yasa na yanke shawarar kokartawa in rubuto muku su online don farin cikinku saboda dominku ake rubutun*💞 *Zamu fara da littafina mai suna RAHIMA saboda yawan tambayarsa da ake in Sha Allah. Littafin *RAHIMA* na *sayarwa ne*, don haka ga masu son karantawa za'ayi adding dinsu a group ne bayan sun biya *300* kacal ta daya daga cikin wadannan bankuna. A- *0598537268* GT Bank B- *6016142358* Keystone. Nagode. ....*RAHIMA*doc by Jami *ONE* Na *Saliha Abubakar Abdullahi Zaria* 1 *Bismillahir Rahmanir Raheem* Gaba daya yau cikin garin Kano an tashi cikin fatsakin rana ne duk da cewan an shiga watannin da ya kamata a rinka samun ruwan sama ko da yaushe. Al'amarin sai addu'a kenan domin wasu jihohin da kauyaku tuni sun sami ruwan sama, banda wannan ma sau da yawa hadari zai hadu a sararin samaniya tamkar ruwa zai sauko kafin kiftawar ido amma cikin hukuncin Allah sannu a hankali hadarin sai ya washe garin yayi haske , abu gwanin ban tsoro. A kalla a kan jera kwanaki ana hakan kafin Jalla sarkin sarauta Yai nasa hikimar a saukar da ruwan kamar da bakin kwarya, wani lokacin har a yini a kwana ana shekawa. Idan anyi dace da wannan baiwa, garin ya kanyi sanyi, duk inda mutum ya taka zai ji taushi da kamshin kasa wanda sansanyar iska ke yadawa ko'ina, alamun an samu ni'imar Allah kenan don zafi zai ragu matuka, daga nan kuma sai manoma su dukufa su koma gona, malamai da sauran jama'a kuwa mu ci gaba da adduar samun damina mai albarka don kasarmu ta Kara samun yalwar abinci da kyakkyawar ci gaba, Allah yasa mu dace, ameen. Duk da cewan ranar tayi yawa wacce ta haddasa zafin dake bugawa ta ko'ina bai hana jama'a bayin Allah zirga-zirga da kaiwa da komowar su wajen sana'oinsu ba, matan aure a gidajensu sun dukufa neman na kansu, halayen Kanawan Dabo dake burgeni kenan. Ba dai kaga suna zaman kashe wando ba mazansu da matansu, babba da yaro sun san hanyar da zasu maida taro sisi, sisi ya zama sule, sulen nan ya koma naira ba tareda girman Kai ko kyashin juna ba. A daya daga cikin wadannan gidajen dake unguwar Yakasai ne Hajiya Kaltume, dattijiya 'yar kimanin shekaru hamsin da biyar ke zaune cikin dakinta tana 'yan kulle-kullen kayan sana'arta, kamarsu kuka, kubewa busashahiya, maggi vedan da mai tauraro, tana sayarda omo, gishiri da suga, ga dakakken yaji da take masa hada-haden kayan kamshi, tafarnuwa dasu magi harda soyayyar gyada,kana ta durasu cikin robobi ko kwalabe tana saidawa. Sha biyu da rabi dai-dai babban danta Dr Haseeb yai sallama ya shigo gidan ya tarad da ita ta baje kayan a gabanta tana ta faman kulli, ganin haka ya kara tamke fuska ya murtuke babu alamun walwala ko kadan. Itama sanin halin likitan yasa ta daure nata fuskar, ko banza Dan fari ne,daman can ba sakin fuskar yake samu ba. Ya gaisheta ta amsa a ciki. Ya gyara zamansa tare da kurawa tafukan hannunsa idanu na 'yan dakikoki ya saki ajiyar zuciya. An ce tsakanin da da mahaifi sai Allah, ajiyar zuciyar da yayi yasa uwar ta dago Kai ta kallesa tace "Kai lafiya, wani abu na damunka ne?" Ya kada kau "Komi lafiya ba abinda ke damuna, sakon da kika bari a gida ne yasa na garzayo inji ko lafiya kike son ganina da hanzari?" Kafin ta bashi amsa Saida ta kulla kullin gishiru uku, hakan ya kara tunzura shi nan take ya kasa daurewa ya bara "Wai Hajiya don Allah me yasa kike son wahalar da kanki ne? Meye naki na zama kina wadannan kulle-kullen?" Ta kallesa ta kau da kai kana ta amsa " Tun shigowarka na lura ranka a bace yake, amma so nawa zan fada maka cewan ni rayuwata ta duniya iyayena basu yi min tarbiyyar zaman banza ba tunda kuruciyata, nasan muhimmancin dogaro da Kai ta hanyar neman na kaina, naga Kuma amfanin sana'a tun duniya na kwance kudin nada daraja ba yanzun da muke muna sana'a ba, muna buga-buga." 03/09/2020, 10:52 - Anty saliha: ....RAHIMA..doc by jami 3 Karfe biyar na wannan ranar yana kwance cikin dakin barcinsa, tunanin al'amarin 'yanuwansa kaf suka addabesa, ya juya can, ya juya nan.... Aka bude kofar dakin a hankali, ta shigo da dauke da cup data doro bisa faranti mai dauke da tatacciyar abarba ta tsaya gefensa ta mika masa, bai karba ba Saida ya tashi zaune, maimakon ya sha ya rinka karkada 'yan kololon kankarar da aka jefa cikin juice din don yai sanyi. Kafadarsa ta dafa tace "In tambayi Daktan wani abu?" Ya dago ya kalleta yana shafar goshinsa da yatsunsa biyu wanda alama ce ta nuni da yana cikin damuwa, ita tasan haka don ba banza kawai take takamar ta fahimci halin wannan murdadden mijin nata da suka kwashe shekaru shidda suna tare ba. Kafin ta bata amsa Saida ya kurbi juice din ya hadiye sannan Y Ya dago ya kalleta yace "Meye?" Ta amsa "Lafiya na ganka cikin wani yanayi tunda ka dawo?" "Ba wani abu ya bata amsa a taikaice kafin ya ci gaba batun auren Rabi'u ne ya taso, Ina ganin karshen watan nan za a daura auren ayi bukin kowa ya huta." Zuwaira ta bugi kirji "Wane Rabi'un, ba dai autan Hjy ba, karatunsa fa?" "Saurara! Ya fadi ba tareda kallonta ba, Hjy na ganin danta ya girma don haka gara ayi auren, idan da halin ci gaba da school to, but for now ayi auren dai... Ta so taji karin bayani daga bakin maigidan nata amma tsawon minti goma sha biyar ta fahimci iyakar abinda zata ji kenan daga bakinsa, taja jiki ta fita ta koma kicin. Karfe shidda kanninsa suka yi sallama gidan babban Yaya, ya fito falonsa suka zauna, Hayatu da Rabi'u suka zamo daga Kan kujeru domin su gaishe shi, ya amsa musu cikin fara'a har suka ji mamaki dalili da a zatonsu bom zai tashi! Ba bata lokaci ya fara magana "Ba wani abu yasa na nemeku ba sai don inji daga bakinka bayan na Hajiya dangane da batun aurenka." Rabi'u ya gyara zama ya fara kare kansa "Wallahi Yaya ban taba tsammanin abu ya zama haka ba, yes nasan mun fara sa mutunta juna tun shigowarta makarantarmu don shekara daya kacal na wuce ta, duk da ba course dinmu guda ba muna fahimtar fannin karatun junanmu da inda muka dosa. Da farko relationship dinmu tamkar yan uwa har a kan kiramu wa da kanwa, cikin ikon Allah myka shaku da juna fuye da zatonku, Kuma wallahi bamu taba furtawa juna batun soyayya ba sai watanni biyu da suka wuce har muke ganin zamu iya zama abokan rayuwa, sai dai ko da muka gasgata muka yanke shawarar bamu kawo batun aure kusa ba don gaskiya na fada mata sai na kare karatu ta amince saboda itama tana shaawar karatun sosai. Ashe muna namu ne Allah na nasa, kwatsam kakanta na wajen uba ya tada kayar baya cewa shi sam bai San da batun

Table of Contents

Chapters

66 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66