Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 43

Chapter 43

Rahima Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

ikon Rabbana? Da itace Zuwaira ba zata yi wani shirme da zai kawo raini tsakaninsu ba, idan ma kishin ne za tayi na 'yan birni irin kishin matan da suka san kansu. Ta zamo daga kan kujera ta rusuna "Aunty barka da kwana, ya kwanan su Khalifa?" Ta galla mata harara tace "Ke Kinga idan kina son kanki da arziki karki sake yi min magana saboda kin zama baka Mai bakar aniya, ki auri kani ki dawo ki aure was ko kunya ba kiji ba. Yanzun ke kinyi abinda ya dace kenan? Idan namiji bai san yakamata ba ke baki san ciwon kanki bane da kika amince masa kuna raba abin Fadi a gari?" Rahima ta dake "Aunty kina da damar fadin abinda kika ga dama don anyi miki laifi, Ni Kuma da kika gani na dauki kaddarar da bani na shiryowa kaina ba, tunda haka Allah ya tsara, haka yake son ganinmu, mun bi umurninsa, na rungumi mijina da hannu biyu, sai dai kiyi hakuri kema ki rungumi kaddarar." "Ba laifinki bane inji Zuwaira da take ta sakar mata harara, duk cin mutuncin da kika yi min sayo min aka yi aka zube cikin gidana, sai dai Ina gargadinki da abu days karki sake ki shiga harkata kota yarana, idan kika yi min shishshigin da kike yiwa danginsu Dakta ranki zai baci ki gwammace ba ki amince kinyi tarayyar miji dani Zuwaira ba." Haseeb ya gyara murya da yaga zata wuce gona da iri yace "Ba surutu ya kawo mu ba, idan keep n shirya ki taho mu tafi Yakasai." Ta kallesa a wulakance "Ban shirya ba, kaje na iskoka can." Ya fusata ya mike yace "Yanzun nan nayi niyyar mu tafi tare ko kin shirya ko baki shirya ba, karki maisheni mutumin banza, inace gudun haka yasa na kiraki a waya na shaida miki tun jiya?" Ta tashi fuu ta wuce cikin bedroom yai kamar ya kyale sai Kuma ya kalli Rahima yace "Excuse me." Ya bita ciki. Tsaye ya iskota tana wani jijjiga tana tsuma wai ita masifa na cinta, yai sallama ya shiga duk da bata amsa ba. Ya tsaya a bayanta cikin wata masifaffiyar sansanyar murya yace "Zuwaira kiyi hankali dani, duk abubuwan da kike yi ba za suyi komi dani ba, kin san Ni, kin San halina, idan Kika sake Kika kureni ke za kiyi dana sanin da baida amfani, na kawo yarinyar nan ki zauna ku gaisa ku fahimci juna abu ya gagara, Rahimar wata ce da baki sani ba? Kina ganin shirmenki zaisa ta ga kimarki ta girmamaki? ke ganinki wannan haukar da kike wace bata da maganin daya wuce hakuri ne mafita a gareki? To ki sani idan muka fita muka je gidan Hajiya, ko gidanku ko nasu Rahima kika kika ki kama kanki za kiyi mamakin matakin da zan dauka a kanki, and yanzun na baki only 5minutes ki shirya ki fito ko ranki ya baci." Yana gama maganganunsa ya fita. Ta tsaya tayi shiru na yan dakikoki kafin ta zabura ta fara Shirin dole domin tabbas tasan halinsa, zai iya Kyaleta tayi masa duk cin kashin da zata yi amma duk ranar data kai shi makura sai ya juye mata ta rasa gane kansa, duk iya kissa da dabarar ta bs zata ciwo kansa ba sai ya gaji ya sauka don kansa. Sannan wani abin takaici sannu cikin ruwan sanyi yake gasata, ita tunda take dashi bai taba daga muryarsa da sunan fada ba, sai dai ya kara zama cool. Tayi kwata, wallahi Haseeb green snake ne. Duk caba adon da tayi da wani jan material Mai sulbu yana shaking a jikinta bai burgesa ba, tana fitowa ya mike Rahima ta bi sahu, har zasu fita ya tsaya ya kalli Zuwairan "Su Khalifa school suka je ko Ina kika tura su?" Ta sassauta murya "Suna school, daga can zasu wuce gida." Yasa Kai suka bi shi. Hhmmm su Zuwaira ashe wargi wuri yaka samu. 14/09/2020, 22:44 - Anty saliha: ..ˆRAHIMA..doc by jami 34 Uwargida ta zauna gaba, amarya na baya, angon na tuki a sukuni, babu mai magana cikinsu duka har saida ya furta cewan akwai tsararbar da ya taho dasu a boot na Mahaifiyarsa da iyayensu kowanne da ledarsa. Rahima ta saurara taji Zuwaira tayi godiya bata yi ba, ta bude baki tace"Mun gode Allah ya Kara budi." Adduar ta yiwa maigidan dadi saboda bai taba yiwa matarsa ko iyayenta wani alkhairi tayi godiya ba, infact ita kullum gani take tunda yana aurenta wajibi ne yayin, idan yayi Kuma ba wani gwaninta ne a gareta ba balle har tayi godiya ta dora da addua irin yadda Rahima tayi masa ba, dadin da yaji yasa ya kallota ta mirror yace "Ameen nagode da addua. Cikin sakin fuska. Hakan ya Kara sa Zuwaira tsuke fuska. Suka Yakasai Hjy Kaltume ta tarbesu da murna da farin ciki, abin gwanin shaawa, suna gama gaisawa ta fara yi musu nasiha, ta fara da Uban gayyar cewan ya rike matansa da zuciya daya tsakani da Allah, yayi kokarin kwatanta adalci tsakaninsu, yaji tsoron Allah, ya tuna da mata da 'y'yansa amana ce a gareshi, yasan Allah ba zai barsa ba muddin yaci amana ko zaluntar wata. Ta juyo kansu tace "Ku Kuma kin zauna lafiya, ku rike mijinku fisabilillah, kuyi biyayyar aure yadda Allah ya umurceku dayi, ku sani aure ibada ne don haka ku tafiyar da rayuwarku da bin dokokinsa. Ke Zuwaira ki Kara hakuri, ki rike girmanki karki sake a rainaki, ki daure ki sanyawa zuciyarki salama, ci gaba bai samuwa sai inda aka yi hakuri.. idan ma an zalunceki ki kayi hakuri Allah zai saka miki .. "Dole a bani hakuri Mana tunda an riga sn zalunce ni, in gaskiya ne me yasa aka rasa wace za a hadashi da ita sai matar Rabiu?" Zuwaira ce ta katse maganar sarakuwarta... Hajiya da Rahima suka bude baki cikin mamaki.. Shi Kuma ya juya a hankali ya kalleta "Kinsan nayi warning dinki ko? Saboda nasan hakan zai faru, to wallahi idan Kika sake ce tak na nuna rashin mutuncin Mahaifiyata na gama aurenki tun a nan ba sai mun matsa ko Ina ba." "Innalillahi wa Inna ilaihirrajiun to ba a gabana ba, ba gidana ba, Kuma ban amince ka karya kadarin aurenku ba." A fusace yace "Hajiya zan yi mata hakurin komi a duniyar nan amma banda wulakanta min ke, sam ba zan taba yarda da wannan rainin wayon ba, idan ba rashin kunyar banza ba ta kalli kwarar idonki tana fada miki wadanan surutan, yau na Kara tabbatar da baki San mutunci ba, baki San darajar na gaba dake ba." Hjy Kaltume tace "Wallahi in don Ni na yafe kaima Kuma kayi hakuri, kasan bacin rai ne." "Bacin rai da akayi mata mene? Aure ne nayi duk abinda za kice kin dade, na auri matar kanina, aurene muke yi ba zaman banza ko?" Sai anan Rahima ta tanka "Don Allah kayi hakuri a bar mahanar." Ya gyara zama "Daga yau kowaccenku ta sani ban hada Mahaifiyata da kowa ba a duniya, haka ina kaunar 'yan uwana kaf fiye da zaton kowa saboda haka duk wace taga ba zata iya kaunarsu ko girmamasu ba zama dani ba dole bane.". Hjy Kaltume ta nisa

Table of Contents

Chapters

66 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66