Chapter 49
Chapter 49
take yasa hannayensa ya rungumota in a warm hug, cikin matukar kulawa yake son jin me ya tsorata ta, ta fada masa mafarkin da tayi, yayi shiru tukunna yaja numfashi ya saki kana yace "Ki daure ki sanyawa zuciyarki salama kan marigayi, nima Dan uwanane Rahima, amma ba zan so ace duk lokacin da muke tare zaki rinka kawo batunsa ba." Taf! A takaice yai misunderstanding dinta kenan, to a ganinsa da gangar take yi ko me yake nufi? Nan take ta cika, ta zare jikinta ta zuro kafafunta zata sauka daga kan gadon ya dago "Ina zaki?" Ta ci gaba da daure igiyar night dress dinta "I just want to be alone." Ta mayar. "Okay zo amshi key don na rufe kofar." Ta juyo da niyyar amsa, ya janyota ta fada jikinsa ya riketa gam ya lakace hancinta "A takaice ba kiji wa'azi ba kenan, don ke ba juya bayan ma za kiyi ba, guduwa za kiyi, Rahima baki da kirki. Ni bada wata manufa nayi miki nasiha ba, kiyi tunanin idan da bani Kika aura ba wane namiji ne zai yarda kuna tare kina maganar tsohon mijinki ko a mace ko a raye.?" Ta langabar da Kai "Ya kayi min muguwar fassara baka fahimceni bane in dai Kuma ba kishi ne ba." Ta karisa tana boye fuskarta. "Hhmmm kunyarki ai na karyane in har zaki iya min Zuciya daga na fada miki gaskiya, in Kuma kishin ne Ni ya dace ma inyi fushin dake Rahima amma sai kika bugeni kika hana min kuka." Ta saki sa sanyar ajiyar zuciya "Kayi hakuri danu Yaya ba zan sake bata maka rai ba, but you should understand me Nima tun farko kace min auren nan dole a gareka to ya za kayi expecting barin tunani bayan nasan banda wani matsayi a zuciyarka data wuce "yar amana?" Yayi shiruu! Lalle baki shi kan yanka wuya, yasan abinda zai fadi amma bai San illar da furucin zai haifar ba. Rahima ta iya ramuwar gayya, shi tun ranar daya Fadi kalmar ma ta manta bai yi tunanin kalmar *dole* zata ja masa problem ba, gashi magana zaran bunu ce data riga ta fito ba a maidata ciki.Ya muskuta yace "Yes na tuna na furta hakan but wallahi is a mistake, i was under pressure at the time ba hakane cikin zuciyata ba, kinsan duk muutum ajizi ne ki yafe min." Tace "Matsayin nawa kawai nike son sani saboda ina cikin duhu." Ya kada Kai " Wannan akwai ki da kure amma ba komi gidan kika taras tunda na lura halayyar mu daya." Tayi murmushi "Wace ni da irin halin manya?" "Hhmmm tsokanace ma abin? To tashi muyi wanka asubah ta karato tunda kin hanamu barci." Kinji namiji wai nice na hana masa barci, ta Fadi a zucci.. Bata yi aune ba taji an sureta an yi cikin toilet da ita, ya direta cikin bath, yai tsaye yace "to bismillah ki inyi miki ne?" Ta rufe ido "No nagode." "Dube ta da anyi magana kice kunya alhalin baki da dama." Bayan ya dawo masallaci ya zauna suka yi karatun quranin tare suka yi azkhar dinsu suka shafa adduoinsu.. Ya rinka mata wani irin kallo yana nazarinta, ya tabbatar wannan lallasausar jikin nata mai kama da jikin mage yai mata tsami ko'ina... Ta dago taga yanayin kallon da yake mata, suka hada ido tayi saurin saurin sauke nata kasa, ita dai wani bala'in nauyinsa take ji. Hhmmm har ga Allah ta gwammace yayi magana komin kankantarta da yin shurun nasa da Allah kadai yasan abinda wannan kwakwalwar tasa mai kamar computer take kirfa masa. Ta sake satar kallonsa har zuwa lokacin ita yake kallon, ya nutsar da idanunsa alamun cikin zurfin tunani yake, da yaga shi take kallon itama yai mata signal, idanunsa sun koma tamkar na mai jin barci, nata sukayi luuu ... Da za a tona zuciyar kowanen su tsantsan so da kaunar junansu ne suka mamaye ko'ina amma sun kasa furtawa juna, hhmmm zuciya na so baki yaki fada kenan inji Aunty Hadiza Bungudu. Da baki zai daure ya taimaki zuciya ta amayo cutar data addabeta da sun sami saukin kuna da tafarfasar da take musu a daidai lokacin. Amma tunda dukkansu kowa naji da kansa sai a rinka kallon-kallo a jira har zuciyoyin su cika su tumbatsa.... Tare suka sauke sansanyar ajiyar zuciya, kasancewarsa namiji yai ta maza ya danne tukukin hayakin soyayyar da ya nemi fitowa waje ya koma kirjinsa ya cika yaci gaba da radadi, ya Kira "Rahima?" Ta dago ido da kyar domin ita kadai tasan abinda take ji, jiransa kawai take ya furta wani Abu yaji sirrin zuciyarta amma tunda bai shirya ba ta dake, ko ba komi a matsayinta na mace ta rike martaba da darajarta har sai ranar da ya gaji ya bara. Ta kanne tace "Ka kirani kuma kayi shiru.. Ya sake yin shiru sannan yace "Kin San anjima zan koma gidan Zuwaira ko?" Bata yi tsammanin kalmar da zai fadi ba kenan, da taji ba warning kishi ya taso ya lullubeta ta shiga jan innalillahi wa Inna ilaihirrajiun domin kishi masifa ce, sannan ta amsa "Yes na san ka"idar ai." Ya kura mata ido don ya lakanci wani abu yace "Ni fa dadi na dake kenan iya zance.". "To me nace daban?" Ya naji a bar zancen, batun asibiti ki bari Saida azahar ki tafi sabida ki kwanta ki sami hutu, batun breakfast ma ba zan ci komi ba for now." Ta kallesa "Wai don me?" "You ve filled my apetite, na Kuma gode Allah ya saka miki yai miki albarka." Ta juya baya don kunyar jin kalamansa, yai murmushi, Nima kwanciyar zanje inyi amma in my bedroom muddin Ina son ki huta din." 16/09/2020, 23:42 - Anty saliha: ...RAHIMA..doc by jami 40 Bata farka ba saida akayi kiran sallar azahar cike da mamaki, rabonta da samun lafiyayyen barci haka ta manta. Saida ta gama kimtsawa tsaf ta nufo kicin wajen Uwale, bayan sun gaisa take tambayarta Yaya ya tafi asibiti ne ban ganshi ba." Uwale tace "Ya jima da fita ai Hajiya, shine ya ban umurnin Kar na sake na tasheki sai kin farka don kanki." "Ikon Allah ta Fadi, to ya batun abincin su Hjy Fatima?" Uwale tace "Tuni an gama aikin sabida tun jiya Alhaji yace in kwana da shirin hada musu abincin Karin kumallo, to har na ranar ma na gama an kai tun dazun, wannan zaman ma da kika ga nayi jiran fitowarki nike in damka miki sakonki in tabbatar da kin ci.".. Rahima ta kalleta "Ban gane ba, anyi yamma da kare,meye na wani tilastani cin abinci gaskiya ban jin yunwa." "Ai kuwa zaki daure kici ko dan kadan ne, na dau alkawarin tabbatar da hakan." "Abincin baida suna ne wai?" Inji Rahima cikin curiousity. Uwale ta duka ta duka ta bude oven ta fiddo sauran naman da suka ci tareda Dakta daten jiya ta aje mata a gaba, kana ta dauko warmer dauke da soyayyen dankali da plantain ta hada mata, ga flask cike da ruwan shayi, ta koma ta jingine." Ta dago "Wadannan abincin duk zan zubawa cikina? Tirkashi, to miko plate in zuba miki naman.". Ta wani zaro ido ta daki kirji tace "Wa Ni?
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66