Chapter 57
Chapter 57
Ni ban dauki Aunty Zuwaira kishiya ba, abinci kuwa ko taci ko Kar taci na sauke nauyin da Allah ya dora min matsayinta na makwabciyata." Ta rike haba "Makwabciya kuma Hajiya, ina makwabciyarki itace Hjy Shafa'atu mai shigowa wajenki din nan?" Rahima tace "Makwabta sun kasu kashi uku ne Uwale, akwai mai daraja ta daya, ana nufin musulmi danuwa da kuke da danganta da juna Makwabci Mai daraja ta biyu shine wadanda baku hada komi amma Allah ya hadaku zama unguwa daya, ka zo , na zo kamar ita Hjy Shafa da kike batu.. Mai daraja ta uku shine makwabcinka da ba musulmi ba. To Kinga zan iya Kiran Aunty Zuwaira makwabciyata Mai m daraja ta daya kasancewarta musulma, ga Zumuncin dake tsakanin yaranmu, ga shi muna auren miji daya, muna zaune karkashin mutum guda, ko da a ce ga dakina ga nata ne sunan mu Makwabta Uwale. Tunda hakan ne wajibi a garemu mu kyautatawa juna don gudun fushin Ubangiji mu Kuma tsira daga cikin mutanen da Allah ba zai karbu tuban su ba matukar sun mutu basu gaggawar gyarawa ba, shin kin san cewan an ce daidai da abinci mai kyau makwabci ya dafa ya ba makwabcinsa Kar ya cinye shi kadai?" Uwale ta gyara zama "Oh gaske naga baki damu da wulakancin da take miki ba kullum idan kin shiga gaisheta, har a zuciyata nace ko dai tsoronta kike ne? Kuma ga wannan kwaikwayon naki da take yi kullum.. "Abu Mai kyau mutum keyi har wani ya gani ya yaba ai, inda taga mummunar abu nikeyi ai ba zata yi ba komin gasar ta kuwa. Bayan haka sanin nauyin da Allah ya dora mana a Kan juna yasa nike share wulakancinta, inyi biris da shirmen ta sabida nasan abinda nike kwadayi, itama rashin sanin ko biris da sanin yasa tayi sakaci shaidan yai rinjaye a kanta amma Ina adduar Allah ya ganar da ita, muma ya Kara mana fahimtar. 19/09/2020, 18:21 - Anty saliha: ..ˆRAHIMA..doc by jami 47 Uwale tayi ajiyar zuciya "Ameen Hajiya, gaskiya zama da mai ilmi babban nasara ce a rayuwa saboda karuwar da mutum zai yi, yanzun gashi na karu da sanin abubuwan da tunda nazo duniya ban sani ba, dole in kara himma a makarantar islamiyyar da na shig, amma Hajiya taimaka ki fada min su wanene Allah ba zai amshi tubansu ba idan suka rasu suna aikata sabon da suke yi basu bari ba?" "Uwale nima ilmin nawa cikin cokali ne, amma yanada kyau komin kankantar ilmin mutum ya sanar da wadanda basu sanin ba suma su amfana sai Allah ya baki lada ya kuma kara bude miki kwakwalwar ki kara ilmantuwa don kiji dadin yadawa jama'ar musulmi. Wadannan mutane bakwai da malamai suka yi mana bayani sune na daya shine Mai bata hakkin makwabtaka, na biyu masu yin luwadi, na uku wadanda suke matse al'aurarsu har sai maniyi ya fito musu, na hudu masu saduwa da dabbobi, na biyar namijin dake saduwa da matarsa ta duburarta, na shidda Wanda ya hada diya da uwa yana saduwa dasu, (irin bala'in da yai yawa yanzun cikin al'umma, uba ya rinka neman diyat da ya haifa) na bakwai mai yin zina da matar makwabcinsa." Uwale ta jinjina "Ashe aiki na gaban rago bai zo ba balle ya wuce, wallahi duk ilahirin jikina ya mutu likis, Lalle muna da sauran aiki jawur, in hakane kuwa Allah kadai yasan ladan da kike kwasa kin barmu baki sake sai dai mu take ciki da abinci mu koshi, kwanya ta toshe da miyar kuka da ruwan goro." Rahima ta kyalkyace da dariya "In don wannan karki samu damuwa tunda muna da likitan kwakwalwa, ya bude ya kwashe miyar." Ta kwalo ido "Rufan asiri Hajiya na koya a hankali." Ta mike "Naga idan na biye miki ba zani gidan Shafa'atun da nayi niyya ba, bari in hanzarta kafin maigidan ya dawo yace ya fasa barin fitar." "To a dawo lafiya Hajjaju." Ta saka hijab dinta har kasa ta nufi sashen Zuwaira tukunna, ta tsaya ta rinka sallama shiru Kuma tasan tana ciki tunda ga motar ta nan. Al'adar ta kenan da duk zata fita zata shaidawa Makwabciya, kazalika idan ta dawo don gudun faruwan wani abu ga Kuma sauke hakkin zama tare, ta juya ta tafi abinta. Ko awa guda bata yi ba ta dawo gida saboda sam Daktan bai so ya dawo gida bata nan duk runtsi, tana matukar gudun zuciyarsa. Bata yi fushi ba data dawo gida ma ta sake shiga wajen Zuwairan shima tayi sallamar shiru har ta juya taji an bude kofar falon, ta dawo ta tsaya "Sannu da Aunty, daman fita zanyi na leko mu gaisa in fada miki but har naje na dawo ma." "Oho ai banji knocking ko sallamar naki ba ina cikin toilet ina wanka." Sai a lokacin Rahima ta bita da kallon yadda ta fito ba riga a jikinta sai towel data ratayo a wuyanta, ta jike gashin kanta sharkaf da ruwa har tana wani girgizashi ruwan na fantsamawa Rahima a fuska. Tace "Ayya tunanina bai kawo hakan ba ai.. "To ya na iya ai nima wankan dole ce ta kamani yanzun, ni wannan hidima na Dakta ta fara isata." Rahima ta wani kalleta ta sakar mata matsiyacin murmushinta tace "Ashe daman ke kika koya masa haka Aunty, da na sani ai da tuni na kawo kararsa wajenki don ni din raguwa ce.". Zuwaira ta zuba mata wata uwar harara tare da tsuki gaba daya ta juya ta rufe kofarta garam, ita kuma ta karisa sashenta tana dariyar wautar Zuwaira, a tunaninta don ta nuna tana tare da miji zai daga mata hankali ko da ace gaskiya ce balle tasan ba hakan bane, ko ce mata akayi jima'i kadai ne jigon rayuwar aure oho. Ba wani dadewa Daktan ya dawo, bayan sun dan taba hira take tambayarsa ko ya leka Hajiyarsa? Ya amsa "Sai zuwa dare in Sha Allahu." Tace "Dazun dana kirata a waya naji alamar bata jin dadi ko ta gaya maka?" "No kin san ba zata fadi ba sai dai mutum ya fahimci akwai damuwar." Ta kallesa, fuskar nan a murtuke, maganar da yake yi dai kace tilas sai kawai tayi dif itama, to ta riga ta lakance sa da zaran miskillancin nasa ya taso ko yana cikin bacin rai ta lura mood dinsa ya canza ta kan ja jikinta sai ya nemeta. Shirun da tayi kuma bai masa dadi ba ya kalleta ya kau da kai, ya sake juyowa ya jefo mata tambayar "Rahima me ya faru tsakaninki da Zuwaira take fada min surutun wofi?" Kunji kuma wani daukakkiyar, ba dai mganar da suka yi ne dazun ta zama abin korafi ba.... Da yaji bata tanka ba, ya cire glass dinsa, ta dago ta kasa kallonsa cikin kwarar idanu, ta juyar da Kai gefe yace "Ba ki ce komi ba." Tace "Saboda ban san amsar bane tunda a sanina ba muyi fada ba just magana ce tayi na bata amsa ko ance wani Abu ya faru beside hakan?" "Look Rahima shirmen nan na guda tunda kuka dage zaku zauna tare na amince dole and you know how much I hate the idea amma Kika nace gashi nan yanzun kusan 6 months kuna tare ba zaman
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66