Chapter 44
Chapter 44
"Ka cika mita, batun ya wuce ai, ina Kara horonka da kayi hakuri a matsayin Wanda ya tara, muna tayaku addua kullum Allah ya albarkaci rayuwarku." Har zuwa lokacin Zuwaira bata ce ayi hakuri ba, to bashi cikin policy dinta sam sabida a ganinta laifin me tayi? Daga fadar gaskiya kawai a dake ka a hana maka kuka a kan me? Sun baiwa Hajiyar tsarabarta wadanda suka kunshi duk abubuwan da yasan tana so ne ya karo mata kasancewar daman bata rasa komi ba. Daga nan gidansu Rahima suka nufa, Umma ta kasa rufe baki don murna, nau'ikan abinci ne aka jera musu na tarbonsu, gefe kayan sanyi ne da ababen motsa Baki, Umma akwai iya tarbon baki... Alh. Mamman na gida don haka bayan ya tsaya sun gaisa dasu Zuwaira yaja Haseeb suka koma soro suka shimfida tabarma ana gaisawa. Suna Nan har aka dauko Abdul daga makaranta yaga babansa ya daka tsalle ya haye jikinsa yana murna. A cikin gida Zuwaira tayi kasake tana kallon yadda ake nunawa Rahima so da kauna irinta tsakanin da da iyaye, ita Kuma tana basu girmansu, ta kanta domin da ita gani take ai 'gata ce a gidansu ashe gatancin Rahima shine gata Kuma ya dama nata ya shanye don ko ba komi gatan bai zamar mata wauta ba balle cuta. Tun tana daure fuska har ta gaji ta saki, to Umma macece mai harka ga iya zama da mutane, ta nunawa Zuwaira su basu iya hauka ba. Suma sunyi murna da tsarabar bakin sunyi godiya sosai. A rijiyar Lemu aininhin Mahaifin Rahima ya nuna Haseeb ba surukinsa bane, Lauratu ce tace ita kam surukutat za tayi da likitan, daga karshe duk da kunyar Rahima da yake ji bai hanata kebewa yai mata nasihohi ba kana ya hadasu yai musu addua, da kyar suka amshi tasu tsarabar suna sa albarka A gidansu Zuwaira kuwa sai ta canza, basu dade da shiga gidan ba ta nunawa Rahima cewan gidan ubanta ne ta wuce gaba ta barta, Rahima ta saki fuska tamkar ta taba zuwa, suma iyayen Zuwaira da 'yanuwanta sun mata kyakkyawar tarbo, suka karramata.Tayi mamakin ganin ingantattar tarbiyyar sauran yaran gidan, kenan kan Zuwaira aka samu zakka. Ganin irin yadda iyayenta suka amsheta da hannu biyu yasa tayi kudurin zama lafiya da diyarsu duk iya fitinar da zata tayar don sunyi mata halacci, sunyi musu nasihohi da adduoin suma.Abdul ya lakewa yan uwansa da suke gidan, suma din kakansu yace su bi iyayensu gida. Zuwaira tayi kwatakyas data ga irun tsarabar da mijinta ya jibgowwa nata family din, duk inda suka fito nasu bai Kai na gidansu yawa ba, yayi hakan ne sabida yawan da suke dashi amma ba dominta ba... Sai karfe goma na dare suka koma gidansa na Galadanci inda ya mikawa kowa nata tsarabar dana Yara. Sun tashi tafiya Uwargida ta hade rai, Rahima tayi mata sallama ta amsa a ciki bata kula ba ta rike hannun Abdul su tafu yaron ya cije shi wajen su Khalifa zai kwana, suma suka ce ki dai a barsa wurinsu, ko su bishi dorayi su kwana can, Rahima tace a tarkato mata su tafi can gaba daya. Zuwaira najin haka tace "Gaskiya ba inda zasu." Yaran suka sa kuka, uban ya wuce cikin bedroom dinsu ya kwaso kayansu ya tasa su a gaba su ukun ya saka a mota kana ya cewa "Rahima ki tafi ku shiga mota Ina zuwa. Taja hannayensu suka fita waje. Tana fita ta fara yarfa ruwan bala',in don me za'a kwashe mata yara ya kai gidan wata, Kuma ba'a tambayeta izni ba. Ya kalleta " "Gidan watan da kike ikrari gidana ne, yarana ne akwai wanda ya isa ya hanani daukarsu ne tunda can naso su kwana?" Ya barta baki bude yai gaba, su kuwa Yara sai murna suke. 15/09/2020, 12:01 - Anty saliha: ..RAHIMA...doc by jami 35 Suna shiga gida Uwale ta taimaka mata suka yiwa yaran wanka tayi musu Shirin kwanciya sannan ta kaisu dakin da aka kebewa Abdul ta shafe kowannansu da azkhar din kwanciyar barci, suka kwanta, ta sakayo musu kofa ta koma dakinta ta fada wanka itama. Tana gama wanka ta dauro alwala, Rahima ko yaushe cikin alwala take dare da rana, ko ya karye zata sake wata saboda malaminsu ya fada musu muhimmancin yin hakan, Wanda ke kwana da alwala mala'ikun rahama Kan bi kowacce kafar gashinsa suna yi mada addua da neman gafara, sannan duk wani shaidanin maridin aljani ba zai kusance shi ba, haka shaidan la'ananne zai nisance shi. Tsaye take a tsakiyar dakinta daure da katon towel bayan ta fito daga toilet, ta dauko man shafawarta data hade da turaren miski ta fara shafawa tana maming wakar nan ta back street boys *I don't care who you're , where you're from, what you do, as long as you love meee* Kamshin dake fitowa daga cikin dakin ya fa fara dukan hancinsa, Yana isa daf da kofar yaji 'yar karamar muryarta na maming wakar da yake son shima, ya kara kutsa kai Yana sallama amma bata ji ba sabida ta shafa'a tunanin maigidan fa na iya shigowa ya ganta ba sutura a jikinta, idan ya ganki fa, ba mijinki bane wata zuciyar ta bata amsa.. Bata ankara ba kawai taga mutum a gabanta, taja da baya a firgice ta bude baki zata buga ihu.. Tafin hannunsa yai saurin sawa ya rufe bakinta tareda yi mata magana a hankali"Me yasa kika cika tsoron tsiya ne?" Ta saki numfashi jikinta ba inda bai rawa, ganin haka yasa ya janyota garesa ta langabar da Kai, kafafunta sunyi sanyi da ace bai riketa ba zata iya kaiwa kasa. Haseeb ya kara mannata a jikinsa har tana jin bugun zuciyarsa, ta dago a hankali tana kokarin kubcewa Amma baiyi niyyar rabuwa da ita ba, wani abu take ji Wanda bata taba experiencing ba... Ya tallabo gemunta don ta kallesa, hasken da taga kwarar idanunsa na fitarwa yasa tayi saurin rufe nata idanun, yayi mumushi "Wai wace irin kunya ce haka da taki karewa?" Tayi shiru ta Kara rumtse idanun. "Rahima bude idanunki ki kalleni." Ta girgiza Kai ta Kara cusa kan nata cikin jikinsa tana shakar kamshinsa. Ya sumbaci tsakiyar kanta, warm lips dinsa suka haifar mata da kasala, ya sassauta rikon da yai mata da niyyar kissing dinta... Wayarsa dake cikin aljihunsa ta fara sound na alamun an kirasa, ya share bai daga ba harta tsinke, aka sake kira, kamar ba zai daga ba again, ya tuna matsayinsa da irin aikinsa na ceton rayukan al'umma, nan da nan ya fiddo wayar ya daga yana sauraren mai kiran, kusan minti biyar kana ya aje ya tsaya yana kallon Rahima data koma gefen gado ta zauna, ya matso ya tsugunna a gabanta.. "Ina fatan lafiya.'. Ta furta da taga yanayin damuwarsa. Ya dafa gwiwarta "Dr Kabir ne ya Kira cewan mun Sami wata patient daga Maiduguri tun dazun Kuma yayi iya nasa kokarin babu canji so zanje mu gani may be sai anyi mata surgery don jini ne ya shiga kwanyarta sanadiyyar accident da tayi." "Subhanallah Ubangiji ya bata lafiya, me zan taimaka maka yanzun don ka hanzarta shiryawa ka tafi?" Rahima ta Fadi cike da tausayin matar da bata sani ba Ya mike tsaye
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66