Chapter 3
Chapter 3
da kuke uba daya nawa suka yi aure? Gaba dayansu babu Wanda ya haura shekaru ashirin a cikinsu, me yasa baka hanasu ba, wane irin gudumuwa ce baka basu ba, sai yanzun yaro ya Kai shekaru da biyar a duniya ya isa aure kace zaka tauye masa hakkinsa?" Yace Yi hakuri ban tari numfashinki ba, wadanda kike magana na amince musu ne saboda kowannansu nada shago a kasuwa, sunada abinyi,tunda sun nuna su kasuwancin suke so fiye da karatun, na tabbatar Kuma zasu iya daukar takalihun matansu, amma Kya hada da wannan ahi ba karatun ba, shi ba aiki ko wata katamammiyar sana'a ba? Idan Kuma kina ganin banyi magana Kan auren su Hamisu ba na Hayatu shima na hana shi ai amma shima don rashin sanin ciwon Kai matar shekararta biyu ya sake auro wata, gasu nan banda tashin hankali me suke yi?" Ta juyo a fusace "Ka rufa min bakinka kaji, ai fa tunda ba Kai ya shafa ba yanzun zaka rinka kawo min kabli da ba'di, to shima da ya auri mata biyun ai ance matar mutum kabarinsa da yaje yana neman na banza a waje ai gara ya tara cikin gidansa. Kai wai ya za ayi daman ra'ayin rikau dinka ya zama irin na kowa? Naji ta bakinka, tashi jeka, kaga kyaun sana'ar da kake mita, ni zan tsaya, Allah kuma zai taimakemu ayi wannan auren da yardar Allah autana ba zai kunyata ba, idan ba zaka jagoranci harkar auren ba ai ba Kai kadai bane, kaninka na Nan, Allah dai na gani na baka hakkinka na kasancewa babba." Da ya tabbatar da al'amarin yai nisa gashi bai son bacin ranta ko kadan har dai in ya tuna can inda aka fito da can dole ya fara lallashi yana bata hakuri yace "Tunda abin ya zama haka ba komi Hajiya, daman ni naso ace ya kara sanin ciwon kansa ne yasan wahalar ya nemi na sa yadda idan yai auren zai fi rike matar da daraja da mutunci amma tunda an matsa insha Allahu ba damuwa za ayi yadda kika ce cikin yardar Allah. Zan nemi Hayatu mu tafi gidan iyayen yarinyar cikin satin nan in yaso duk yadda muka yi dasu Kya ji, anjima ki turo min Rabi'un yai min bayanin unguwar, Allah yasa mana hannu." Dadi ya rufeta cikin murna tace "Insha Allah yau dinnan zaka ganshi yana dawowa gida zan turo maka shi, Allah yai maka albarka." "Ameen nagode, idan babu wani abu Ina son komawa asibiti amma shi Rabi'un ya sameni a gida." Ya ciro kudi cikin aljihunsa ya ajiye a gabanta bisa tabarma, ya mike kana yai mata sallama ya fita tana sanya masa albarka. 03/09/2020, 10:52 - Anty saliha: ...RAHIMA..doc by jami 4 Rabi'u yace "Yaya Haseeb, Rahima da iyayenta 'yan usulin jihar nan ne, gidansu na unguwar rijiyar lemu, muna iya kiranta marainiya don ta rasa mahaifiyata tun lokacin haihuwarta. Bayan Allah ya amshi ran mahaifiyarta ne kanwar uwar dake shayar da nata jaririyar 'yar kimanin watanni uku ta dauketa taci gaba da shayar dasu gaba daya. Kasancewa mahaifinta daman matansa biyu sai abin yazo masa da sauki domin ta samu saukin maraicin diyarsa da aka mutu aka barin masa, ko sa yake ita ce diya kwara daya tilo da mahaifiyarta ta bari su bakwai ne cif wajen mahaifinsu, sunan mahaifiyar nata aka mayar mata don tunawa da marigayiyar. Sunan mahaifinta Aliyu ana kiransa Ali mai goro, data girma ta isa shiga makaranta saita shiga da suna Rahima Mamman Mai yadi, sunanta marikinta kenan, kowa dai ya san Mamman Mai yadi na Yakasai, tsakanin gidansa dana Hajiya bai wuce loko biyar zuwa shidda ba, bayan wannan Rahima yarinya ce mai hankali da zurfin tunani Ya Haseeb. Hayatu ya kallesa "To ai ka bari har mu bincika muji wa kunuwanmu tukunna kana mu zartas da hukunci, Kai daman ya za ayi ka Fadi wasu aibunta tunda kana sonta." Rabi'u yace "Balle ma bata dasu, yarinya ce mai da'a wace ta samu dimbin kyawawan tarbiyya nagari Kuma nagartacce." A nan dole Haseeb yai murmushin da bai shirya ba yace "A nan kan Ina bayan Hayatu Rabi'u, idan har mun bincika mun tabbatar da yarinyar da halayen daka fadi babu shakka kayi sa'ar Mata, idan kuma munji sabanin haka sai dai kayi hakuri. Yanzun sai ku koma gida, idan Allah ya kaimu gobe zanyi abinda ya dace sai kaje kaci gaba da adduar Allah ya tabbatar mana da alkhairi. Duk yadda muka yi goben za kuji insha Allah." Sunyi sallama cikin farin cika da murna. Kamar yadda ya dauki alkawari, ya binciko dukkan abubuwan da suka dace ya sani ya Kuma ji ta gamsu saboda aure tsakanin Rabi'u da Rahima tabbas ba makawa. Baiyi sanya a gwiwa ba nan da Nan ya nemi Baffansu Rabi'u da kanin Hajiyarsul watau kawunsu yai musu bayanin halinda ake ciki. Suma basu bata lokaci ba suka amince, suka hadu su hudu suka nufi gidan Mamman Mai yadi a matsayin mabidan auren wa dansu diyarsa. Ba wai ta fannin saye da sayar da yadiddika kadau yasa sunan Alh. Mamman yayi fice ba, ah ah duk wani Mai hulda dashi ta cinikayya ko harkokin yau da kullum ya shaidi mutym ne Mai son jama'a da mutunta su, ya iya hulda da mutane kwarai da gaske. Ta fannin iyalinsa kuwa matarsa uwar 'ya'yansa Habiba ita kadai ya mallaka, tunda ya aureta suke zaune lafiya, zaman so da kauna da mutunta juna sai bai taba sha'awa ko tunanin karo wata matar ba, gashu sun hayayyafa, Allah ya azurtasu da diya takwas, biyar maza uku mata. A zahiri diyanta bakwai ne amma tunda matarsa ta amshi marainiya Rahima ta shayar da ita yarinyar ta shiga zuciyarsa, yaji yana tsananin sonta, irin son da da mahaifi har bai son yaji wasu su furta bashi ya haifeta ba, itama kanta Rahimar Saida tayi wayo ta fara sanin ciwon kanta ne ta fahimci cewan ba sune mahaifanta ba, ta Kara tabbatar da hakan yanzun da aka ce mahaifinta na wajen Uba ne yai ruwa sa tsaki wajen hanata ci gaba da karatunta. Hausawa kance wani ma yai rawa ballantana dan makadi, su Alh. Mamman kan shiga su fita suyi wakilcin aurarraki da dama har sau sunga an kulla sunnar Manzon Allah SAW suke numfasawa to Ina ga Kuma ana batun auren diyarsu aka zi yi, 'yar lelensa wace yake ji da ita? 'Yanuwan Rabiu da sukayi tattaki zuwa wajen neman auren sunsha mamakin irin karamcin da akayi musu bayan an karbesu hannu bibbiyu. Sun rabu kan cewan an basu yarinya saura batun sa ranar daurin aure sai abinda 'Yanuwa suka tattauna zasu nemi dangin angon. Mutunta su day aka yi ya karawa Hasseb kwarin gwiwar aiwatar da abubuwan da suka kamata dangane da auren. Kudi ya ware masu yawan gaske ya baiwa matarsa ta hado kayan lefe setin akwatuna uku dankare da tufafi, kayan shafa, jakunna, takalma da sauran tarkacen da ake hadawa budurwar data hadu Kuma ta dace da Mai yin. Shi kansa Rabi'u akwati guda ya cika masa da tsadaddun shaddodi na shigar angonci kana ya samar masa Dan madaidaicin gidan da zasu zauna amma mahaifiyarsu taki amincewa da hakan, tace tafi son ta zauna tare dasu tunda daga amaryar har angon
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66