Chapter 47
Chapter 47
da laifin karatu ba amfani cikin marubutanmu naji sai gaba yake yi, nagode 'yaruwa, zanyi iya kokarina da taimakon Allah." "Oho na dai fita hakkinki, ni yanzun ma Dakta nafi baiwa laifi.' Ta bude baki "Wane laifi Kuma?" Ta muskuta "Ah to ba namiji yake ba sai yace kule ace masa cas! Ko sai zuciyoyinku sunyi bursting?" Rahima ta jinjina "Wane irin bursting Kuma?" "To in baku ba ya za ayi ina so Ina kaiwa kasuwa?" "Allah ya shiryeki a bar batun Ni dai." A nan suka hadu suka dafa abincin da zasu Kai asibiti, Maryam ma tace tana neman ladan. Karfe takwas na dare suka koma asibiti harda Alh. Abbas inda suka taras da 'yanuwan Haj.Fatima sun iso lafiya. Matafiyan uncles dinta ne su biyu da kanwarta Falmata wace zata zauna tareda ita har ayi sallama. Lokaci kankani matan suka zama tamkar 'yanuwa, Falmata sun sarke da Maryam, ita din zawarci take kuma bata taba haihuwa ba a inda ta fiton, Hjy Fatima kuwa yaranta hudu, maza uku mace guda, bata da kishiya, sai ma dalilin wannan hadarin ne da yaso ya zama kamar ta samu tabuwar kwakwalwa dangin miji suka fara batun ya nemi wata matar, bai dai saurari kowa ba a lokacin hankalinsa tashe yake yana neman wa matarsa uwar 'ya'yansa hanyar da zata samu waraka, bisa dukkan alamu Kuma an dace. Sai karfe goma saura Alh Abbas da Ahmad Shariff suka shiga cikin ward din, Abbas yacevwa Maryam ta taso su tafu gida akwai alamun hadari ana walkiyya. Da jin hakan Rahima ta mike itama tace zata bisu su ajeta kawai tunda har zuwa lokacin Daktan bai dawo ba. Koda suka ajeta basu tsaya ba saboda hadari na shirin tasowa, Maryam ta leko kai ta windo tace "Ya za kiyi yanzun na sanki da tsoron ruwan sama." Rahima tace "Kin cika tonon silili saida safenku." Ta shige gida Kai tsaye dakin Uwale ta wuce ta sameta har ta kwanta, ta tashi zaune "Oh a gaisheki Hajiya sai yanzun?" Tace "Ke dai bari, yau ma zirga-zirgan muka sha duk na gaji, wanka kawai zanyi in kwanta." Uwale tace "Ga garin ma da alamar ruwa za ai Mana." Ta wuce tana fadin "Allah ya bamu Mai albarka, mu kwana lafiya." Kasancewar ta gabatar da sallolinta cire kayan jikinta kawai tayi ta fada wanka, inda Saida ta cika bath din taf da ruwan dumi, ta zazzaga bath salt a ciki, ruwan ya dau kamshi da kumfa Mai sulbu, ta shige ciki tayi wanka ta fito ta gabatar da alwala ta fito. Ta goge jikin da yayi smooth, bata shafa mai ba balle wani make up, just turare ta mutstsuka a jikinta ta saka cotton night dress tana tunanin may be weather din yai sanyi a dalilin ruwan saman da taji yana shirin saukowa. Tayi adduointa ta kwanta, ta dauki wani novel ta bude ta fara karanta shafi guda ta rufe, hirarsu da Maryam ne ke mata yawo a kai. Ba shakka gaskiya ta fada mata hakika son mijinta ya mamaye zuciyarta ba karya, yanzun ne ta Kara fahimtar maanar so da kaunar wani, watau da shirme take, to Allah yasa ba tana abin nan da hausawa ke Kira *son ma so wani ne* ba. Ai da kuwa wahala ta ganta, oh oh Allah Mai yin yadda ya so, ya dauke kani ya hadata da wa to Amma a wane babi take cikin zuciyarsa? Ta zabura ta tashi, tunda ba amsar zata samu ba is better ta tashi ta gabatar da sallah ta Kara addua. Ta shafa kenan taji dawowar Haseeb. 16/09/2020, 06:08 - Anty saliha: RAHIMA...doc by jami 38 Ya shigo ya sameta kan sallaya, mamaki ya nuna a fuskarsa amma yace "Kin ganni sai yanzun ko? Kiyi hakuri." Ta kada Kai "Ya Mai jikin?" Ya amsa "Da sauki malaria ce ke damunta." "Allah ya saukaka, ba wani abinda kake so don kwanciya zanyi?" Yace "Akwai, but kiyi min hakuri inyi wanka please.". Ya fita yana tunanin why ta daure fuskarta tamau haka, ba dai kishi ke damunta ba itama, idan hakane zaiyi farn ciki don alama kenan na kamu da son sa kamar yadda yake jinta a zuciyarsa. Bayan fitarsa tayi kasake! Lalle ma namiji sai a barsa kawai, ji yadda ya shigo yana mata wani shan kamshi sai kace in laifinne bashi yayi mata ba ya dawo Yana tabarmar kunya. . That's why fa Ubangiji yace ba zasu iya adalci ba sai dai su kwatanta. Hhmmm Kar shaidan ta xugata tana zargin abinda bata gani ba ance ko zato zunubi. Tausayin Zuwaira ma ya tsirga mata dole fa ne baiwar Allah Nan tayi kishin mijinta... Ya sake dawowa ya ganta zaune inda ya barta "Har yanzun adduar ake ne?" "Ah ah". Ta amsa a takaice. Yace "Allah ya karba mana amma da kin matso nan ko haka zan rinka maganar kina can Ina Nan?" Ta mike cikin rashin karsashi ta dawo dab da gadon da yake zaune a kai ta zauna. 16/09/2020, 22:25 - Anty saliha: ...RAHIMA..doc by jami 39 Ya kalli yadda ta wani takure a gefensa ya girgiza kai yace "Rahima ya dace ki fahimci matsayinmu na ma'aurata, meye kike dari-dari?" Tayi shiru bata amsa ba, yaja numfashi yace "Gobe idan Allah ya kaimu kwanaki ukun da aka tanadar mana zasu kare sabanin kwanaki bakwai na auren budurwa. Wadannan kwanaki Kuma ba an kebe sune kawai don ango da amarya su hole ba kadai, ah ah ana son miji ya koyar da matansa abubuwan da ya lura bata sani ba dangane da addini ko zamantakewar auren ma gaba daya. To alhamdulillah! a 'yan kwanakin da muka yi tare nasa ido kan yanayin ibadarki abinda na gani abin yabo ne sosai, sai dai duk da haka wajibi ne gareni in miki wasu tambayoyin kan addinin don sauke nauyin dake kaina, kin fahimce ni?" Ta dago kai ta amsa "Na fahimta, me kake son sani?" Ya gyara zama "Ki karanta min suratul fatihatul kitaab, ki fada min farillan alwala, sallah da sunnonin su." Ta nisa tukunna kafin ta da basmalla ta kare karatun kana taci gaba da jero wadanda ya bukaci sanin." " Masha Allah Rahima, na godewa Allah da ya nufeni da aurenki, Allah yasa diyanmu su amfana da ilmin da ya bamu." Ta amsa "Amin ya Hayyu ya Qayyum, nagode da yabawa." Daktan yayi dan murmushinsa kafin yaci gaba "To bayan wadannan akwai 'yan abubuwan da nike son in Kara miki kwarin gwiwar ci gaba da aikatawa, alal misali na lura kina yawaita alwala ko yaushe, yana da kyau matuka, ko kina cikin tsarki ko jinin haila domin Manzon Allah SAW yai Mana nuni cewan duk Wanda ya kwanta da alwala ya gabatar da azkhar din kwanciyar barci akwai mala'ikan dake bin kafofin gashinsa jiki yana kwance a karkashi da duk ka motsa ya roka maka gafarar Allah, abu na biyu ki kiyaye salar kiyamul lail, ki rinka raya dare da ibada sabida mafi yawanci jahilai masu sihiri cikin duhun dare suke aikata surkullensu, to su can suna shirmensu ke kuma kina bautar Ubangijinki. Na lura ke mai yawan addua ce, to idan zaki roki Allah ki rinka masa fadanci kina masa kirari da tsarkakakkun sunayensu mafi soyuwa a garesa, wadanda idan aka kirayesa dasu
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66