Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 52

Chapter 52

Rahima Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

kaina ya dau zafi already." Ta sadda kanta kasa "Zuwa nayi in baka hakuri, don Allah da Annabinsa ka yafe min." Yace "Idan nayi hakurin na yau, sai kuma na yaushe, anjima, gobe ko jibi? Kuma ma hakurin me kike bani, mun riga mun saba, zaman auren kawai muke tamkar wasu jahilai." Ta muskutta "Ni dai nace ka yafe min ba don halina ba." "Me Kika yi da kike neman yafiyata, Ni a was Nike a rayuwarki don ban san matsayin da kika ajeni ba." Ta dago cikin hanzari "Ya zaka ce haka, matsayin mijina mana." Yace "To su Kuma abokan da kike dasu na waje matsayin me suke a gareki?" Ta fara kuka" Ni fa wallahi tallahi ban taba tarayya da kowanne namiji ba, wadanda muke huldar business dinmu kadai ne muke communicating dasu." "Ni ban tambayeki kuka ba, to su din kuma muharramanki ne? Zuwaira ki ji tsoron Allah, ki sani komin dadewarki a duniya Zaki tafi lahira, Allah zai tuhumeki abubuwan da kika aikata a duniya. To wai tsaya ma tun farkon aurenmu nasan ke din mace harija, duk kokarin sauke hakkinki ki kan nuna ke ba a gamsar dake ba, tun a nan na fara tausayinki, bayan wannan ke din nan fa ban aureki cikakkiyar mace ba, for whatever reason hakan ya kasance gareki ban sani ba, that's why ganin yadda kike huladarki da abokan naki yasa ni zargin. A wancan lokacin mutuncin dake tsakanina da mahaifinki yasa na share, na danne zuciyata har addua na rinka yi kar Allah yasa in rinka ganin bakinki ko rashin martabarki, ba don haka ba da tuni mutuncinki ya gama zubewa a idona, ke kinsan *virginity* darajar diya mace ce amma na ci gaba da zama dake da halayenki na rashin da'a amma kawaicina da hakuri bai sa kin gyara ba, sai kika kara shiga harkar kawaye masu zugaki kina shiririta, kina zaton ba don su Khalifa sunyi kama dani ba Zan karbesu ne a matsayin 'ya'yana? Nace idan ma halink ne yau da gobe bata bar komi ba ai. Daga nan saboda daurewa yawon gindi kika je kika daure mahaifa wai ke karki haihu ki tsufa da wuri, kika kara samun lasisin yawon. Kullum cikin nasiha nike a gareki amma ko a jikinki, Zuwaira ban rageki da komi ba, ba rashin abinci ba sutura, ba rashin kudin kashewa, iyayenki na kokarinsu a kanki to ashe duk ba muyi miki gwaninta ba, kince kina son ki nemi na kanki na mara miki baya don nima ban son tauye hakkinki, kuma no matter how much muke baki, is good ki nemi na kanki din saboda halin yau da gobe, but sai kika zake in the process, ke kinsan wanene ni, ni ba mazinaci ba ne, Allah ya kaddaro min auren Rahima kin kasa kwantar da hankalinki sai shirme da hauka kike wadanda ba zasu hanani komi ba balle su sani illa ma ki Kara zubda mutuncinki a idona. But ki sani kin kaini makura, saura kiris in dau matakin da zai baki mamaki." Tayi kasake tana saurarensa, to me ya fadi Wanda ba gaskiya ba? Babu, tayi tsumi ta muzanta, to ai shi daman komi kake aikatawa Allah na ganinka da lokacin da zai kama ka a hannu... Amma Allah ya sani da zuciya daya ta auri mijinta don tana matukar son abinta, amma ba a a nan gizo ke sakar ba, tun kafin ta auri Haseeb kawarta a boarding school ta fara bata ta in the process of lesbianism, ta saba a haka har suka gama school, sai kuma wani tsinannan saurayinta ya nemeta ba tare da sanin kowa ba, har iyayenta, tun kafin taga Haseeb. A gaskiya tafi danganta lalacewarta da wadannan mutum biyun da suka taka rawa wajen gurbacewar tarbiyyarta duk ta taso da shagwabar nata, iyayenta sunyi kokarin gyara tarbiyyarta ta fandare ita ala dole yar gata, kuma yan uwanta kaf ba haka suke ba.. Ta kalli mijinta da wutsiyar ido taga latsar wayarsa kawai tunda ya gama mata magana, in banda sharrin shaidan wace mace ce zata sami miji irinsa tayi mishi rikon sakainar kashi? Wallahi ko personality dinsa kadai ya ishi mace jin sha'awarsa balle a Kai ga kyawawan halayensa, ba domin shawarwarin da Husaina ke bata ba da tuni ta daina abubuwan da take yi ta rungumi mijinta, to amma ko yanzun lokaci bai kure ba, but Kashi! Inda zata sami cikas dayane, wannan auren da dauko. Sai dai kuwa ta kadata tayi gaba ta bar mata mijinta idan kuma taking fita za taga sharri kala-kala, ba zuwa wajen boka balle Malam, Zuwaira bata bin malamai duk iya shegenta, wannan sai Husaina. Tasa hanni ta shafi lallausar suman kansa "Kayi barci ne?" Ya wani dago kamar wace ta cije shi, "Menene Kuma?" "Na rokeka gafara ne banji kace ka yafe min ba ." Na yafe miki Zuwaira Allah ya yafe mana gaba daya amma ki roki gafarar Ubanginki kan zunuban da kika dauka da niyyar ba zaki sake aikata kwatankwacin su ba, idan kuwa kinsan ba zaki bari ba, no need ma kiyi istigfarin don Allah ba abokin wasan kowa bane, ai kin gane?" Tace "Wallahi har ga Allah ba zan sake ba, don Allah ka tayani addu'a. Yace "Kullum cikinta muke, muma ajizai ne Allah ya yafe mana dukkan kurakurenmu." Tace "Ameen.' Ya juya baya domin turaren data fesa hawa kansa yake, karfinsa yai yawa har ji yake kamat zaiyi amai." Ba da son ransa ba ya rinka tuna sansanyar kamshin turaren Rahima Wanda ya kama jikinta radam, turarenta har wani kashe jiki yake...bai gajiya da shakarsa.. Ta matsa kusa dashi ta shafa bayansa ta kira sunansa "Dakta? Ya amsa "Ni kuwa haihuwa nike so." Wata sabuwa inji yan caca! Ba tareda ya waigo ba yace ",To Ni ke bada haihuwar, da can Kuma nina hanaki? Ai kin fini sanin abinyi sai ki hada da addua.". Ta kwantar da kanta a jikinsa ta sassauta murya "Ka taba ganin mace ta haihu ita kadai, yaushe rabon daka kusance Ni?" Haseeb ya dafe Kai! Allah wadaran naka ya lalace, shi bai taba ganin mace maras kunya irin zuwaira ba, duk da ya saba da halinta na rashin iya danne maitarta, yau abin yai masa wani iri, ko don 'yan kwanakin da yayi da Rahima ne, yana son mace mai kunya, yana jin dadin yadda take jin nauyinsa, mace mace mai kunya abin so ce, duk yadda taso da bukata sai an kai ga rarrashinta ta bar mijin da rawar jikin, Kai Allah ya shiryi Zuwaira, abinda akace kunya na daga cikin yankin imani. Da taji ya Kyaleta ta kuma Kara rungumarsa tace "Kasan dai hakkina na kanka ba mai sauke min shi sai kai, kuma zaka rantse da Allah kwanaki ukun da kayi a wancan gidan haka kayi salin alin ba abinda ya wakana tsakaninku sai Ni don na nemi hakkina ka ja min rai?" Cikin deadly voice yace "Nayi warning dinki daga yau idan zaki magana karki sake kawo min batun Rahima.. Ta marairaice ta narke a jikinsa "Afwaan ba zan sake ba. " Ya dago ya kalleta tun daga sama har kasa yaji shi kansa kyamar kansa yake ji but wajibi sauke nauyinta da Allah ya dora a kansa, ya tashi zaune

Table of Contents

Chapters

66 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66