Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 65

Chapter 65

Rahima Book 1 Complete Hausa Novel 1,212 words 0 views Progress saved
Download Book

ake bukata tunda shima ya zama business man, sosai suke samun nasibi baya ga business dinsu da Maryam Kuma, sun Kara da saro designers perfumes, shoes and bags latest designs. Rahima ta biyawa Umma da Baffa kujerar Hajj, ranar Umma Saida ta zuba ruwa a kasa tasha domin murna tare da godiyar Allah da ya rayasu ya shirya musu zuriyyar ya daukaka su har an fara dawainiyya dasu da wasu ma duk ana cin gajiyarsu. Ka'idane duk shekara Haseeb na fitar da zakka ya rabawa marasu galihu, ya kuma biyawa wadanda Allah ya tsaga rabonsu zuwa sauke farali ko Umrah, wannan karon kuri'ar kan Lauratu goggon Rahima, Malaminsa Mal. Nuhu da amintaccen maigadinsa Mal Hassan ta fada.. Rahima tace itama zata biyawa Uwale da fatar Allah ya kai ladar kabarin mahaifiyarta da Rabi'u Duk karshen wata suke haduwa family ana sauke qur'ani a gidan Daktan, in an kare ayi adduoi ga dukkan mamata da masu rayuwar, iyaye, 'ya'ya, 'yanuwa da abokan arziki, jiharsu da kasarsu baki daya. Duk ranar jumma'a za a dafa abinci a rinka rabawa mabukata sadaka duk don neman yardar Ubangiji da neman karin yalwarsa cikin dukkan al'amurran ratuwarsu. Aikin Dr Haseeb sai dada bunkasa yake, sunansa na dada yaduwa yayinda yaci gaba da bude rassuna jiha-jiha Yana samo kwararrun likitoci Yana zubawa Gwamnatin tarayya ta yaba da kwazonea kwarai suka bashi mukamin *Minister for health* Yace bai so hidimomi sunyi masa yawa... Mata da 'yanuwa suka yi masa ca! Bai amince ba saida Hajiyarsa tasa baki tace "Ya Allah zai maka daukaka ka butulce? Hidimomi ba Allah ke taimakonka tafiyar da komi ba ko da karfinka kake?" Ya amsa da zuciya guda ya fara aiki. Kamar ba za a sake haihuwa gidan ministan ba domin Saida Ummi ta shekara uku aka samar mata kani, wannan karon sai ga kyakkyawar yaro, ga tsawo ga kiba, babansa zahiri.. Ranar suna Saida kowa yai kwalla da yaji sunansa *Rabiu* Nauyi kam ya karu kan Daktan, ga na iyalinsa, ga na Mahaifiyarsa, 'yanuwa dana yanuwan Zuwaira ga na jama'an Annabi da suke cin arzikinsa banda na aikinsa, ya zama bai da lokacin kansa. A ka zo batun komawa Abuja Zuwaira tace sai dai Rahima ta tafi domin ta sakankance ita dince ce *star* din Haseeb, ta kuma hakura da haka duk da cewa ba nuna banbanci yake tsakaninsu a zahiri ba, Rahimar taki yarda da shawarar Aunyn ta domin tsakaninta da ita girmamawa ce. Da kansa takobin dagan ya raba gardama cewan kowacce zata rinka zuwa wata uku ta dawo dayan ta tafi Kuma, wace lokacin hutu ya shigo cikin turn dinta ta tafi da yara. Zuwaira ta sake samun 'yar bebinta 'yar caraf kyakkyawa, da ganinta tace wannan ai Rahima ce,kamar yana jiran ta furta, ministan ya rada mata suna *Rahima* suna kiranta Amira. Zuwaira na murna ita kuwa wace akayi dominta ta korafin me yasa ba a fara sanya sunan Zuwaira ba? Ya kalleta yace "Banyi gwaninta ba kenan?" Ta amsa "Wallahi kayi sosai na kuma ji dadi nagode amma kayi min alkawarin idan muddin na haifi mace Zuwaira ce." Yace "Allah ya kawo cikin, shin ko har an samu?" To Allah yayi an haihun amma namiji aka samu sai yaya kenan? Ya rada masa suna Habibullah. Shekaru sun mika kwarai, tuni Dr Abdul Haseeb Junaid ya ajiye aikin gwamnati bayan shekaru takkwas yana bautawa kasarsa a matsayin ministan lafiya. 'Ya'yansu maza sun kare univertsity. Junaid (Khalifa) Engineer ne, Mohammad(Abba) Architect, Abdul Haseeb karami ya bi sahun babansa ya zama likitan kwakwalwa, yana kasar Bulgeria karo ilmi. 'Yan matan Kuma Muhibba ta dage saita zama irin Dr Kausar ta cikin littafin Anti Saliha Zumuncin Zamani, ita din Gynaecologist ce, Ummul Salama Lawyer ce don ita Bartister Tahir ne gwaninta(Son Zuciya) Ummi Habiba sha'awar Boutique din Sufab ya tunzuro ta da yadda ita kanta Surayuar ke tafiyar da business dinta da son taimakon iyayenta yasa ta karanta Business Administration yayinda Amira Rahima ke son zama cikakkiyar malamar makatanta mai zaman kanta irin na Sa'adatun Sagir haka dan autan gidan Daktan yace shi malamin lissafi zai zama, so Habibullah mathematician ne. Wata rana Daktan ta tara manyan 'ya'yansa lokacin Abdul karami ya kare karatunsa yace lokaci yayi da kowannansu zai fitar da abokiyar rayuwarsa. Ba bata lokaci Junaid ya nuna Walida diyar Maryam yake so wace ke zuwa hutu wajen Innarta Rahima, Muhammad yace Nabila diyar Uncle Hayatu. Wadannan 'yan Mata duk karatu suke a B.U.K. ne, Walida na karanta Mass Communications tunda a rayuwarta Laila Tahir Mutallib ce role model dinta, Nabils na karanta Economics. Idan ta bi daga-daga na kurya kan Sha Kashi, Abdul Haseeb junior yayi shiru bai ce komi ba, to shima miskilin ne irin uwarsa da wan uban, to Barewa tayi gudu ne danta yai rarrafe? Baban nasa yaxe ya rubuto sunan wace yake so tunda ba zai furta ba, ya rubuta ya ajiye, yana fita ya dauki takardar ya warware, abinda ya gani yai matukar faranta ransa, ba domin namiji yake ba da yai guda Amma yayi abinda yafi dacewa yayi a irin yanayin, ya daga hannuwansa sama yace "Tsarki ya tabbata gareka ya Allah Ubangijin Al'Arshi mai girma!!! Ya sake duban takardar da Abdul ya rubuta *Daddy Rahima Amira ce mata ta Insha Allahu* Ya juya takardar yana mamakin ko ya aka yi yaran suka yi tunanin hada auren zumunci gaba dayansu oho? 23/09/2020, 12:31 - Anty saliha: ...RAHIMA...doc by jami 54 Iyaye, 'yanuwa da kakanni kama da abokan arziki da sauran jama'ar da suka ji labarin hada wadannan igiyoyin aure sai sha'awa da murna suke. Kasa-kasa ba inda Daktan bai aika da katin gayyata ba, duk wasu masu hulda da asibitocinsa, abokai da tawagar shugaban kasa da kusoshin gwamnatocin jihohin Arewa sun halarci wannan gayarumin dauren aurarraki. Da yake al'amarun tuwona Mai na ne shi kansa Daktan ya rasa inda zai fi maida hankali a sha'anin, to kusan shine uban angwaye da amaren baki daya, haka ya wakilta kanninsa da abokan arziki aka taru aka yi komi cikin tsari gwanin sha'awa. A wajen bukin ne su Ummul Salama suka hadu da masoyansu ita ta hadu da abokin Khalifa, Muhibba dan abokin babanta balarabe nan na Riyadh ke sonta, har sun amincewa juna, sai adduar Allah ya nunawa iyaye lokacin nasu bukin. Bayan an gama shagalin da wata guda, kura ta lafa, Zuwaira ce da Rahima ke zaune a main parlour suna hira, sai kallon Rahimar take cike da sha'awa tana yaba yadda take tafiyar da al'amurran rayuwarta ta yau da kullum, me zata ce da wannan baiwar Allah? Gaskiya sai godiya da adduar Allah ya saka mata da khairan domin a dalilinta ita kanta da 'ya'yanta sun samu nagartacciyar rayuwa, ta sami kan maigidanta yanzun girmamata yake sabanin da can inda aka fito..... Karar waya ta dawo da ita daga duniyar tunani, tayi firgigit daidai Rahima ta dauka ta sallama, can taji ta rafka salati ta kalli Zuwaira, ita Kuma a firgice tace "Me ya faru wa Kuma muka rasa?" Rahima tace "Allah yaiwa Husaina rasuwa sanadiyyar accident.....Zuwaira tayi kasake tsoron Allah ya Kara kamata, duniyar kenan mai halin dan mangwaro, sai ta bari ka saki jiki kana tsotso kana jin zakinta ta subuce maka. Ita yaushe rabonta da ita tun ranar

Table of Contents

Chapters

66 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66