Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 40

Chapter 40

Rahima Book 1 Complete Hausa Novel 1,209 words 0 views Progress saved
Download Book

suma suka bi suka kwanta ya gama shirunsa tsaf ya juya ya kalli Zuwaira dake zaune gefen gado yace "Ni zan tafi ba wani abu?" Ta kallesa ta watsar bata tanka ba. Yai ajiyar zuciya ya mike tsam ya nufi kofa kafin ya isa ta rigashi ta taresa "Kana nufin can Dorayi zaka tafi yanzun ka kwana can?" Ya kura mata ido ta cikin glass dinsa yace "Me kike so inyi miki ne Zuwaira,tunda na shigo gidan nan kike neman ffitina, me kike so?" Ta Kara tare kofa "Me nake so? Ya za kayi min wannan shegiyar tambayar bayan wani gida kayi niyyar tafiya ka kwana, bani da right da zan tuhumeka?" Ya girgiza Kai "Ki tuhumeni for what reason? Look Zuwaira ki gane addini yaba magidanci damar sauka duk inda yaso in ya dawo daga tafiya in har ya mallaki mace fiye da daya, amma ga mai son kyautatawa sai ya sauka wajen uwargidansa ko wace take da girki a ranar, a al'adance. To ke na kyautata miki, na dawo na sauka a nan,tsawon lokacin dana dauka tare dake kika nuna tamkar baki san daga inda na fito ba, babu maraban arziki balle nuna jin dadi da hamdallah ga Allah cewan naje na dawo lafiya, banyi fushi ba na zauna tare dake har zuwa yanzun duba time karfe nawa ne, sai kuma zan fita ki taso ki dasa min wasu tambayoyin da basu dace ba? Me ma kike nufin da wai can zan kwana? To yes can zan kwana, idan kin manta ne in tuna miki yanzu ku biyu na mallaka matsayin mata ne, hakkin Rahima ma ya rayata a kaina yadda naki hakkin yake a kaina, wajibi ne in sauke nauyin da Allsh ya dora min nata, tunda an daura ba na Nan, kwana uku zanyi a gidanta, kana in dawo ku ci gaba da raba kwana yadda kuke so wace ban kwana gidanta ba wajibi in lekata da safe don ganin lafiyarta, Ina fatar kin fahimceni, bani hanya in wuce." Wai saita saka kukan kissa ta kama shi gam ta rike "Sabida Allah nu kadai zaka barni in kwana cikin katon gidan nan?" Ya girgiza Kai "Yau aka fara hakan? Idan ban barki kin kwana ke kadai ba ai ke kya barni ki tafi balaguronki ko, to meye na damuwa yau keda kike alla-alla ki samu kafar yawo?" Taci gaba da kuka wanda a zahiri tana yine don bata masa lokaci, ya dago manufarta, ya yakiceta ya raba daga gefenta ya fita, ta bisa har waje yayinda direbansa ya taso ya bude masa mota, yace Mata "Saida safe." Ya shige mota abinsa suka tafi. 13/09/2020, 23:21 - Anty saliha: ...ˆRAHIMA..doc by jami 31 Mal. Hassan ya dagewa direba murfin gate ya wuce harabar da aka tanada domin aje motocin. Uwale ce ta fara hango Maigidan ta tagar kicin yana gaisawa dasu Mal. Hassan bayan fitowarsa daga mota, direban ya bude boot yana fito da kayan dake ciki suka fara shiga dasu cikin gida. Rahima na can cikin bedroom dinta bata San bidirin da ake yi ba, kwance take rigingine ta kifa littafin da tsananin tunani ya hana mata karantawa a fuskarta kamar tana barci, zurfin tunanin da take yi ya hana jin sallamar da Dr Haseeb yayi. Ya dauka barci take ya Kara sallama har sau uku bata motsa ba, ya matsa ya shiga cikin dakin, taushin rug din ya hana mata jin takunsa, saida ya kai daf da gadon da take kwance, yaji sautin wata waka dake fita a wayarta, ta wasu samari da su Kai masa suna *I don't care who you're* Ya tsaya bisa kanta yai mata kallon tsaf cikin dakikoki...... Jikinta ya bata lalle ana kallonta, daidai lokacin ya duka ya kai hannunsa ya cire book din data kare fuskarta, daidai lokacin suka shaki kamshin juna, Rahima ta kai hannunta zata cire book din, already nasa hannun ya sauka a kafadarta. Ganin wanda yake tsaye kanta ta yunkuro ta tashi zaune a tsorace. Ba tareda yayi magana ba ya maidata kwance ganin yadda ta razana, tana ta kokarin fahimtar what's happening is real ba mafarki ne ba, tayi kokarin magana but shock ya hanata, shima a kidime yake don da za a auna jininsa a lokacin za a ga ya hau saboda bugun da zuciyarsa keyi very fast. Ya gyara muryar da zama very low yace "Sorry I didn't mean to scare you.' Ta saki ajiyar zuciya yayinda ta sake yunkurin tashi ta zamo kafafunta yaja da baya kadan still yana kallonta, ta cije tace "Sannu da zuwa, afwaan ban ji shigowarka ba, ya hanya?" Ya amsa "Alhamdulillah ya gida? Idanuwansa na kanta ya lura da kananan kitson da aka tsarawa sumanta da suka sauka har bayan keyarta kafin ta lalubi dankwalinta ta rufe kanta. Yana tsaye yana ci gaba da yi mata kallon kurilla harta mike ta gyara rigarta ta lalubi mayafi ta rufa kana ta fara kame-kame tace "Abinci na can dining ko sai kayi Sallah ka huta tukunna?" Ya bi da kallo ya share tambayar bai amsa ba saboda ya fahimci so tayi ya juya ya bar badroom din shi Kuma kamshin dake fita a hankali ya haifar masa da wani irin natsuwar da yasa yaji yana son zama cikinsa. Amma tunda yaga a rude take, bari ya hakura har ta samu natsuwa. Ya kalleta "Zan shiga dakina for now inada wasu calls before magrib." Rahima ta nufi kicin ta taradda Uwale da Haladu nata shirya kayayakin da ya taho dasu, sun aje komi a mazaunin da ya dace, suna gamawa Uwalen tace "Hajiya zamu sake dafa wani abincin ne?" Ta kada Kai "Ah wadanda muka yi suna cikin warmers ai ba abinda suka yi." "To ke fa? Naga kina son tuwo har na dora ruwan zafi?" Ta girgiza Kai "Ba Zan ci ba gaskiya sai dai ko ke, amma nagode da kokari." Uwale ta dafa cikinta "Ai nima din a koshen nike alhamdulillah." Rahima tace Shikenan "Zan shiga inyi sallar magrib sai anjima kenan." Ta bude baki "Saida safe dai Hajiya, maigida ya dawo wane hira za muyi yau?" Ta girgiza Kai "Uwale kina son shige mun hanci amma zan fyato ki." Tayi saurin durkusawa "Wace Ni uwar dakina, yafe min, amma kinsan gaskiya na Fadi." Ta shiga tana dariya "Hhhmm naso in ganki da kuriyarki Uwale, kin cika ban dariya. Wasu masu shigowa gidan Rahima suna korafin wai tana sakewa da 'yar aikinta da yawa, ita kuwa mace ce mai ba kowanne irin mutum darajarsa, ta Kan dauki kanta ita ba wata tsiya bace, bata wulakanta na kasa da ita saboda sanin kowacce halitta da irin darajar da Allah yai Mata, tsakaninta da masu aikin gidanta,, mutunci ne da girmama juna. Ta dade da idar da sallar isha'i amma ta kasa tashi daga sallayarta. Kamar yadda yaji kamshin dakinta hakan ya cika nashi dakin tun daga falonsa zuwa bedroom, komi ya Burgesa, tsarin yai masa daidai. Hhhmmm ya kasa zama sai tunani, shi bai ma san yadda zai bullowa wannan auren nasu ba duk da ya rungumi auren nan da hannu biyu. To ai ba nan gizo ke sakar ba, ganin irin dari-darin da ta fara yi dashi, to ai shi din ma bai saki jiki da ita

Table of Contents

Chapters

66 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66