Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 55

Chapter 55

Rahima Book 1 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
Download Book

batun kyauta ta." Maganganunsa sun sa kunyarsa ta dawo mata sabuwa ta rufe idanunta, ya banbare da kyar. Cikin shagaba tace "Don Allah ka rabu dani.". Yace "Ai kuwa baki isa ba, alkawari ki kai min wajibi ki cika sa." Tace "To me kake so?" Ya amsa "Sai kin kalleni zan fada miki." Tana kallonsa yace *Yourself* Hhhmmm wai don Allah da gaske ne da mutane ke cewa yawancin Doctors maza basa jin kunyar fadar magana? Saboda ita ga nata likitan nan Yana ta rikita mata kwanya da surutan da ko a mafarki bata yi zaton zai iya Fadi ba. Dr Haseeb da Rahima sun ci gaba da gudanar da rayuwar aurensu gwanin sha'awa, aka bar masu fadin ya za ayi wa ya auri matar kaninsa baki ya mutu sai sha'awar su suke. Sati biyu cif Dakta ya tabbatar da warkewar patient dinsa Hjy Fatima don haka ya rubuta musu sallama. Da kansa ya daukesu zuwa gidansa suka kwana guda sannan suka koma Maiduguri. Ba su tafi ba Saida suka tabbatar zumunci Mai karfi ya kullu tsakaninsu tareda da alkawarin ziyarar su day zaran ya samu sarari inji likitan, sun rabu suna begen junan Hutun da Rahima ta dauka ya kare sai batun komawa aiki, Daktan ya daka tsalle waje guda yace ba zata sabu ba Wai bindiga a ruwa, yadda ta shagwaba shi yana bukatar attention dinta sosai amma yace ta nemi sana'ar da zata yi don bai son ta zauna hannu sake tana jiran kullum sai anyi Mata. Ta nemi shawarar iyayenta suka amince, ita da 'yaruwarta Maryam suka hada jari suka aikawa Hjy Fatima ta fara turo musu turarukan wuta, na jiki, dana tufafi, har dasu lapayya. A sannu Ubangiji yasa musu albarka, kasuwanci ya habaka ya karbu wajen matan manya sai hamdala. Kwatsam Zuwaira ta tada fitinar sai dai a hade su gida daya saboda kullum cikin zargin mijinsu na mata rashin adalci take, kuma wai ma Rahimar bin malamai take a nata tunanin ba haka kawai miji ke rawar jiki da ita ba. 18/09/2020, 19:13 - Anty saliha: ...RAHIMA..doc by jami 45 Tun daga Kan Hjy Kaltume, Maryam da Iyayenta babu wanda ya bata goyon bayan ta amince da bukatar Zuwaira ba balle shi kansa uban gayyar da yace duk abinda zata ce taje ta dade bata ba amma bai yarda tsarin ba sam. Rahima tace a bata kwana bakwai tayi istikhara ta roki Allah zabi tukunna. Sarai yasan halin gimbiyar tasa don haka yace Kar ma ta san ran zai canza ra'ayinsa ya riga ya yanke shawara. Ba Rahima bata amince da shawarwarin da aka bata bane, no bata san abinda gaba zata haifar ba, zaman nasu khairi ne ko sharri Allah kadai yasan gaibu, dalilinta kenan na dagewa tayi adduar saboda zuciyarta ta kasa tsayuwa waje guda. Bayan satin taji ta natsu ta amince da batun hadasu din sai dai ta dage da adduar neman tsari daga dukkan sharri da fitinar dare da rana. Tana tunkarar maigidan da maganar yai tsalle yace ba zai taba hadasu ba, ta kafe kan ra'ayinta ya kafe kan nasa taron taurin kai. Ranar tana zaune taji sallamar su Umma da Hjy Kaltume Daktan na biye dasu ta girgiza Kai ta tabbatar shi ya dauko su kan batun nan da yaki ci yaki cinyewa. Bayan ta gaishesu ta kawo musu abin motsa baki, bata bari sun fara magana ta tambayesu "Yaya karata ya kai ko?" Hajiya Kaltume ta gyada kai "Har yanzun kaina a daure yake Rahima, na rasa dalilin da yasa kike son dauko fitina da hannunki ki kawi cikin gidanki, me ye zafi haka? Ta sunkuyar da kai "Hajiya baku fahimce nu bane shiyasa kuke tunanin hakan." "Ina fa zamu fahimceki tunda ba muyi wayo da hankalinki ba." Ummanta ta fadi a fusace. Ta kalleta a raunane "Afwaan Umma haka nike nufi ba." Hajiya ta kalli Umma "Saurara mata tayi Mana bayani watakila ta fi mu gaskiya.". Sai a nan Haseeb ya tanka yace "In dai itace yanzun zata kashe miki jiki da lafuzanta ki amince da manufarta ko banza ba Kya ganin laifinta." Rahima ta kallesa "Shikenan Yaya bari in musu bayani idan basu amince ba wallahi na hakura, amma kafin nan ka fadu hujjojinka na rashin son hadamu din." Ya gyara zama "Hujjoji?, Halayyen Zuwaira ai ba boye suke ba, kuna nesa da juna ma ban tsira da korafinta na Ina rashin adalci tsakaninku ba, fitinar yau daban ta gobe daban Wanda da ina biye mata da tuni mun rabu." Rahima tace " Kuna jinsa ko? To ai ni abinda ban son ya faru kenan, da can din ai da halinta baka rabu da ita ba sai bayan aurena? Ko Ni ce zanyi zargin dalilin wata ka rabu dani, daga nan Kuma kulalliyar gaba ta kullu tsakanina da yaranka har abada saboda mai zurfin tunani ne zai gane cewan gajiya kayi da halinta ka Kai makura ne silar rabuwarku, batun danne hakkinta da take yi ma zaman mu a tare zai sa ta gani idan ana zaluntarta din, Kai kuma za a rage maka yawan zirga-zirga tunda iyakinka na natse waje daya hankalinka zai fi kwanciya." Umma ta daka mata harara "Ai ba dai iya magana ba 'yar ka iya, shi ba wadannan matsalolin suka dame sa ba." Yace "Ta fa san duk abinda nike gudu Umma." Hajiya tace "Rahima zaki iya zama da Zuwaira da halayyenta?" Ta gyara zama tace "Sai maganar halayye muke Hajiya amma bamu tsaya munyi nazarin shin wane irin hali Aunty Zuwaira ke dashi ba kamar yadda masu ilmin sanin halayyan dan Adam suka kasa halayyen mutum har kashi uku. Na farko akwai halayyen da basu gyaruwa kwata-kwata, misali irin halayyen da mutum ya gada daga iyaye ko aka haifesa dasu, to kowa yasan halayen Aunty Zuwaira ba gado ba ne don kowa ya shaidi martabatar iyayenta da sauran zuriyyarsu, ba kuma wadanda aka haifeta dasu bane. Na biyu shine halayyen mutum da ake iya gyarawa Amma sai an Sha wahala sosai wajen yin gyaran, irin wadannan halayyen mutum kan tsiri yinsu ne a kan da dole ma'ana wani dalili ya tilasta wajen adopting canza original halinda aka san mutum dashi. Misali irin yanzun da yawancin maza kan bar wa mace takakihun hidimar gida, yau da gobe darajar sa na iya zubewa a idonta, ta daina ganin girmansa sabanin yadda take mutuntashi da can. Na uku mutum Kan dauki halayyan da ba nasa ba da rana tsaka ko dalilin hulda da abokan banza, ko haka kawai ya halin wani ya rinka burgesa, irin wadannan gyara kawai suke bukata ba kuma za a wahala wajen gyarawan ba. Ya kada kai yace "To munji mai falsafa cikin wadannan kashin da kika zano da wanne kika danganta Zuwaira dashi har kike shaawar zamanku tare? Kenan kina ganin zaki iya gyara halayyenta? Rahima ta nisa "Sanin gaibu sai Lillahi, Ina adduar sanadiyyar zaman tare ta canza halayen nata." Hjy Kaltume tace "Da kyau Rahima haka ake son musulmin kwarai ya sowa kansa abinda yake so wa kansa, kin burgeni." Umma tace "Hakane Hajiya nima banki naki ba, tashin hankaline nike gudu." Rahima tayi murmushi "Kamar kin manta da halin diyar taki Umma, fitina ta kan kare ne Kan Wanda ya jawota, Ni dai

Table of Contents

Chapters

66 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66