Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 30

Chapter 30

Rahima Book 1 Complete Hausa Novel 1,208 words 0 views Progress saved
Download Book

Yana zuwa ya durkusa gaida Alhajin amma ya mika masa hannu su gaisa, ya dan tsaya saboda jin nauyi, Alh. Muhammad ya riko hannunsa Yana dariya, ya tambayi sunansa ya fada masa, ya sake tambayar dalilinsa na yawo da littafai Yana aiki ya bashi amsa da "Ina neman na kaina ne." Ya sake tambayarsa wanene mahaifinsa ya fada, nan da Nan ya gane don shi din sanannan mutum ne, Alh Muhd yai mamakin jin sunan mahaifinsa da yadda ya bar dansa na kwadigo bayan Allah yai masa rufun asirin da zai taimaki wani ma ba dansa kadai ba. Yana son jun ainihin tarihin yaron nan don haka ya mika masa katinsa yace ta samesa a gidansa a ranar, ya karba yana mamakinsa dalilin da yasa yake son ganinsa tareda alkawarin zuwa da dare. Karfe takwas na dareya isa gidan Alh Muhammad, da alamun an bada labarin zuwansa domin yadda maigadi ya tarbesa yai masa jagora har falon maigidan. Alh. Ya mike ya sake Mika masa hannu suka gaisa kana ya bashi umurnin ya zauna ya zabi abinda zai ci cikin nau'ikan abincin da aka baza a tsakiyar falon. Yasha lemu kawai yace ya koshi, Alh ya jima yana kallon yaron da ya shiga zuciyarsa farad daya ki domin baida da namijine ohom. Yaso yaji dukkan labarinsa but Abdul Haseeb ba haka yake ba, bayan miskillanci yanada rike sirrinsa domin ba ayi ciki don tuwo kadai ba, to ma haka kawai ne daga haduwa da mutum bai San kowanne irine bane zai zayyane masa sirrinsa, no bai san abinda zaije ya komo ba, bai san me mutumin ke nufi dashi ba. Alh Muhd ya tabbatar da ba zai Kara jin komi daga bakin bakonsa ba ya hakura ba don ya gamsu ba sabida har zuwa lokacin Yana mamakin uban da zai samu hazikin yaro kamilalle irin Haseeb yai biris da al'amarin neman ilminsa, da daure kai sosai amma tunda yaron ya dage kan cewan Yana kwadagon don ya taimaki kansa ne ya kyalesa a haka yai masa taimakon da zai iya yi masa. 09/09/2020, 23:56 - Anty saliha: ..ˆRAHIMA ...doc by jami 22 A ranar yaiwa Haseeb albishir din cewan saboda ya yaba dashi matuka gaya zai taimaka masa Kan harkar neman ilminsa tun daga kasarmu zuwa kasashen ketare har ya cimma burinsa. Yace Yana son ya dau masa alkawarin zai amince ya zama dansa saboda shi bai taba haihuwar da namiji ba, 'ya'yansa takwas duk matane. Bai yi saurin amincewan ba ya nemi ya bashi kwanaki uku yaje yai shawara tukunna, Alh.Muhd ya amince ya kawo kudi ya bashi yace yai kudin mota. Ya amsa yai godiya ya tafi. A ranar ya sallama gidan mijin mahaifiyarsa Yana kiransa Baffa, ya shaida musu duk abinda ya faru, Kaltume ta tsaya shiru ta rasa ta cewa, maigidanta yace mishi "Kaje ka amshi taimakon nan da hannu biyu ka rikesa da zuciya guda bisa amana tareda adduar Allah ya taimakeka bukatarka ta biya." Kaltume ta nisa "Anya? Ina jinjina batun mutumin nan Malam, kana ganin za'a kwashe lafiya, ka fa san halin mutanen zamanin nan na mu." Mal. Sunusi yace "Insha Allah na komi, Ubangiji fa ba yadda bai iya tsara al'amarinsa ba, idan cikin hikima da basirarsa ya kaddaro Alh. Muhammadu ya taimaki yaron nan ba makawa, ai shine kaddarar, zaki ga wani mutumin ba ko a mafarki tunani bai taba kaika cewan zaku hadu ba sai kwatsam Allah ya hadaku a shiga cin gajiyar juna. Kai dai har kullum gargadina gareku shine Wanda duk Allah ya hadaku dasu ku zauna dasu tsakani da Allah da zuciya daya, banda hassada ko kyashi, Banda biyewa zuciya ko mutanen duniya 'yan Kai kawo su shiga tsakaninku, banda daukar jita-jita. Ka sani daukaka Allah ke yiwa mutum ba kowa ba, idan ya so ka daukaka iya hassadar makiya basu isa su hana ba, kazalika in baiyi nufu ba ba Wanda ya isa ya kaika inda Allah bai Kai ka ba. Banda wulakanta mutum da kowacce irin halitta, banda kwadayi don yana janyowa mutum wulakanci da kaskanci, kayi imanin komi ya same ka cikin rayuwarka rubutacce ne daga Allah, wani ko wata, mutum da aljan basu isa suyi maka abinda ba Allah ya rubuto zai faru dakai cikin *Lauhul Mahfuz* ba. Ka riki gaskiya duk inda ka tsinci kanka cikin kowanne yanayi, Ina gargadinka daka rike addininka hannu biyu, ko da Allah zai daukaka nan gaba ta azurtaka karka butulce masa son duniya ya shagaltar dakai bauta masa gwargwadon iyawarka... Ka rike mutumin daya taimakeka da hannu biyu, ko da ace baiyi maka komi ba kaunar daya nuna maka ta isa domin duk Wanda ya kaunaceka irin haka, ba don wani Abu naka ba sai domin Allah ya gama maka komi, karka sake samun duniya ma'ana dukiya ta hadaka dashi, Kar ka zame masa mutum mugun icce. Da wadannan nasihohi masu mugun shiga jiki Abdul-Haseeb da mahaifiyarsa suka yi na'am da Alh. Muhd. Shi kuma can ya kosa yaron ya dawo yaji ta bakinsa domin har ya nemi alfarmar gwamna cewan yana da d'a idan mai girma gwamna zai tura hazikan dalibai karatu kasashen waje a saka sunansa. Gwamna ya amsa da alkawarin idan lokaci yayi nan da watanni uku zai sanar dashi. Lokacin da Abdul Haseeb ya koma gidan Alh Haseeb kansa ya daure, an nuna masa ya riga ya zama dan gida, kowa sai ji dashi yake kamar daman a gidan yake tafiya yayi ya dawo, hidimomi salamu Alaikum. Kaltume da maigidanta musamman Abdul Haseeb ya kaisu yi masa godiya shi da iyalinsa. Kafin watanni ukun Alh Muhd yaja Haseeb a jikinsa sosai ya Kuma bashi labarinsa tas, shima yace ya taso cikin wahala sakamakon iyayensa sun rasu tun Yana karami amma daga dangin uwa har na uba aka rasa Mai daukar nauyin karatunsa, nan ya shiga neman abinda zai hucewa kansa takaici, ya fara da yiwa wani attajiri kiwon doki, ya kanje ya yanko ciyawa ya share turkensa ya kula da dawakin ana biyansa, daga nan ya koma sayar da sigari, da goro, minti ashana da sauran tarkacce a tire a tashar mota, daga nan Allsh ta tarfawa garinsa nono,ya kafa dan tebur daga nan sai shagon kayan masarufi, daga nan Allah ya daga shi sannu-sannu ya fara kwangila tareda taimakon Allah, Ubangiji ya daga har ya Kai matsayin da yake ciki yanzun. Ya auri mata uku bai Sami haihuwa da wuri ba, da ya samun sai Allah ya azurta shi da diya Mata. Alkawarin da yayi suna gama sakandire zai aurad dasu, Amma duk ranar da Allah ya bashi d'a namiji sai inda karfinsa ya kare.. Zuwaira ce diyarsa ta biyu, Mai bala'in kama dashi saboda hakane yake sonta kwarai da gaske, irin son da ya janyo mata sangarcewar. A lokacin da ya hadu da Haseeb duk suna makaranta, Zuwaira na aji uku kacal. Duk wani takalihunsa ya koma hannun Alh Muhd, duk da haka bai saki jiki ya daina buga-bugan sa ba. A hankali ya fara koyon hanyoyin kasuwanci ya rinka aiwatar da abinda ya saukaka a garesa. Yayin da gwamnatin jihar Kanota dauki nauyin fitarsu zuwa kasar *Neatherlands* domin zama kwararren likita. Abdul Haseeb ya zama *Neurologist* ya zamewa uwa da uba dashi kansa Alh Muhd din d'a daya tamkar

Table of Contents

Chapters

66 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66