Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 17

Chapter 17

Rahima Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

ta taras da gidan nasu a hargitse, itada Uwargidanta basa ko ga maciji, karin abin haushi harda raba Kan 'ya'yansu kowa harkarta take da diyanta. Ran Rahima ya baci,hankalinta yai matukar tashi, bata saurari Maryam don ita ta dorawa lefin abubuwan dake faruwa. Maryam tace "Banyi tsammanin zaki ki fahimta ta ba Rahima, ki duba irin bautar dana yiwa matar Nan da yayanta tun zuwana gidannan tun kafin in haihu na kula da yaranta, Ina bata girmanta, yanzu kuwa na gaji don shiru ba tsoro bane gudun fitina nike yi, yanzun kuwa ban damu ba aje ayi tayi idan tace kule zance cas! Ba abinda zata nuna min, idan tana takama da miji ne nima dashi nike, idan yarane nima ina dasu to sai me? Haka siddan mace ta isheni ta gallabeni tamkar ita ta aje Ni? "Hhmmmm inji Rahima "Maryam don Allah numfasa ki saurareni da kyau, ya za ayi ki taho ki taras da mace da mijinta da yara kice zaki nuna mata iko? Mijinta fa kika aure... "Don na auri mijinta sai me, don ita kadai aka halilto shi ne, mijin mace hudu yake, don me idan ta yayo shararta bata zubewa a kansa sai nawa? To na gaji da rainin wayo, ya isa haka." Rahima tace "Ban ce bata da irin nata laifin ba don bai yiwwa ace koda yaushe mutum guda ne ke da laifi da duk magana ta tashi, dole ace tanada irin nata problem, kawai so nike ki fahimci bai kamata ki biye mata duk ku haukace koma ince ku kafirce gaba daya ba, haba 'yaruwa a matsayinki na musulma ki tsiri gaba da 'yaruwarki musulma, makwabciyarki Kuma?" Ta kada Kai "To ya kike son inyi, ita ta fara, sau nawa Ina gaisheta tana shareni tun ina daurewa nace mu zuba mu gani, ko abinci na aika mata bata ci sai ta maido min ta wanke tukunya ta dora wani ta ci, naga bai dau wani mataki ba bayan ya gani da idonsa, nace tunda haka ne bari nima in maida martani tunda ni ba shegiya bace da ubana, ta hana yaranta shigowa dakina balle suyi wasa da yanuwansu, tun Ina damuwa na dake na fara ramuwar gayya Wanda tafi gayyar zafi inji hausawa." "Kash! Inji Rahima, da baki biye mata ba, me zaisa ki bar shaidan ya samu gurbin gina katangarsa a zuciyarki, don me ba za kiyi aiki da ilmin da Allah ya hore miki ba ki nuna mata abubuwan da take yi tsagwaron jahilici ne?" Ta tabe baki "Kishi da jahilar mace ko masifa, duk yadda kika so ki fahimtar da ita ba zata taba ganewa ba, kullum inda kika dosa daban inda ta dosa daban, kina gabas tana yamma, to yaushe zan bata lokacina a aikin banza." Rahima tace "Da kike kiranta jahila ba gara ita dake ba? Laifinta ragagge ne don dama bata da sanin, ke kuwa kin sani kin take sanin laifi biyu kenan, to wai shi maigidan bai san abubuwan dake faruwa cikin gidansa tsakanin iyalinsa ba?" "Kwarai ya sani Mana, cewa yayi in dominsa muke muje mu kashe kanmu ba ruwansa tunda yai kokarin sulhunta mu Abu ya faskara." Taja tsaki "You see, ya maisheku mahaukata wadanda basu San ciwon kansu ba, tun anan bai isa ku hankalto ba? Shi da kuke kishin dominsa bai damu ba Wai ma in mutuwa za kuyi ku mutu, eh lalle yace muku haka, in Kun kashe kanku ai bashi kuka yiwa asara ba illa iyaye, 'ya'ya da 'yanuwanku, baida asara Kona miyaun barci iyaka ya auri wasu ya zuba a rufe chapter dinku ku bar 'ya'ya da abun kunya." Maryam ta juyo "To naji ustaziyar zamani, zanyi nazari in kwatanta in gani, idan da canji in ci gaba, idan babu riba Zan watsar mu ci gaba da zaman doya da manjan don babu macen da zata takani in kyale." Rahima tace" Allah ya ganar damu baki daya, Kinga da na taho da niyyar kwana amma na fasa don ba zan iya zama gidan da ake gaba ba " Nan da nan ta marairaice "Don Allah yi hakuri na bari, muyi kwanciyarmu.". Ta nufi kofa "Ba zan tabbatar da kin bari ba sai munje har dakinta na gaisheta tukunna, mu dawo in baki labarin dalilin zuwana." Da kyar ta amince suka tafi, suka sallama ta amsa,suka shiga ciki. Tayi mamakin ganin 'yaruwar kishiyarta da suka shafe sati biyu suna gaba da juna, da ita kanta. Rahima ta gaisheta tamkar bata san me ke faruwa ba ta amsa, suka Dan jima suna kame-kamen magana, zuwa can Nafi'u yaron da Maryam ke goyo ya nufi gaban Tv ta ya dauko wata flower vase na glass, uwar tayi saurin tashi ta amsa ta bubbugeshi. Hjy Suwaiba ta kalleta "Meye na dukan wannan Dan yaron kinada hankali kuwa? Ta amsa "Ba kiga barnar da zai yi bane?". Hjy Suwaiba ta dauki vase din ta sake mikawa yaron "Idan ya fasa naki ne? Maryam tayi shiru Rahima tayi murmushi "Nima shi na gani yaro da kayan uwarsa.". Hjy Suwaiba tace "Kila so take in bar mata danta ko daman Walida ce tawa, ta rike kayan barnarta kin ganshi mummuna." Maryam ta kalli Rahima "Kinji ta ko? Wallahi tunda aka haifeshi take tsangwamarsa Wai Walida ta fishi kyau ko Ina kyaun da katon hanci oho._ Hajiya Suwaiba tayi dariya " munji ba komu muma da kayan gyara, naki a sa masa 'yankunne da janbaki mu gani." "Ah ah Hjy gaskiya cun fuskar tayi yawa, ki dai rike taki mu rike namu." A haka suka ci gaba da wasa da dariya har kusan magriba sannan suka koma dakin Maryam suka yi Sallah. Suna idarwa Hjy Suwaiba ta aiko musu da kulolin abinci wai a kawowa Rahima, da gani abincin yafi karfin ita kadai dole suka ci tare da Maryam din ita ta fasa dora tukunya. Rahima ta kalleta tace " Don Allah da kika shiga dakinta, kikai Mata magana gashi har kinci abincinta me ya rage a jikinki? Inda za a bude Miki file dinki yau kiga dimbin ladan da kika samu da ba zaki yards ki kara yin gaba ba koda wasa." "Wallahi Kuma Nima sai naji wani irin dadi a Raina, duk kuncin da nike ji a zuciyata ya yaye na yarda sai kaso abu ya dameka yake damunka din.".. Rahima tace abinda har yanzun mu mata bamu gane ba kenan, mu ke creating ma kanmu problems din da zasu dawo su dame mu, namiji ba ruwansa, sai un har kunyi dace da Mai kula ne zai fahimci halinda kuke cikin, wani ko ya gani ba abinda ya damesa tunda yawancinsu sunfi son haka, su tara Mata cikin gida ayita adawa a kansu, ya fito Yana jin dadi da hura hanci ya rinka ikrarin sabida tsananin son da kuke masa kishi ya hanaku zaman lafiya. Wani shaidanin zaman lafiyar ce bai so, yana ganin kun hada kai sai ya kasa sukuni ya shiga zargi da fargaban shifa sai yadda kuka yi dashi kenan domin da wuya daya ta yarda a ci amanar guda shi kuwa bai son hakan, yafi son ya zama bakin ganga, ya buga nan, ya Fadi gaibu can, yai munafunci a nan sai kunada kyakkyawar kula zaku gane in ba haka

Table of Contents

Chapters

66 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66