Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 54

Chapter 54

Rahima Book 1 Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
Download Book

dinsa 'Blue fruit cikin fridge yai madaidaicin sanyi. Kwanaki biyun da yayi gidan Zuwaira sun bata damar canza tsarin bedroom dinsa ta kawata dakin barcinta da nasa da furanni masu kyau, daga gefen window ma ta aje wasu tukunyar live flower dake fitar da natural kamshi saboda iska da hasken rana dake taimaka musu. Sabon duvet ta baza a saman gadonsa,banda soft blanket din dake gefe koda ana bukatar lullube jiki idan sanyi yai taso, ta feshe gadon da turare Mai suna *seduction* kana ta feshe dakin gaba daya da Natural fresh air (pot pouri), ta kunna Air condition sannan ta koma ga suturar sa da ya saka ya cire kafin barinsa gidan, alreday an wanke su tas an goge, jerasu kawai tayi cikon wardrobe dinsa, da kanta wanke inner wears dinsa ta goge ta feshesu da turare suma ta jera komi a mazauninsa. A gurguje ta leka asibiti ta basu Hjy Fatima hakurin ba zasu ganta da yamma ba ranar, ta koma gida ta ci gaba da hidimarta tsabtacce jikinta, al'adarta ce duk karshen wata bayan ta Kara period ta kanyi shaving pubic hair dinta da na armpit saboda koyi da addininmu da inganta tsabta, to yau ma hakan tayi. Uwale ta rangada mata zanen shuku suka zuba har dokin wuyanta saboda gwargwado tanada yalwar suma ta kame da ribbon,tanada son kumshi sosai, shima Uwalen ta taimaka ta d'afa mata celotape da aka yiwa designs masu kyaun gaske kafa da tafin hannu sannan aka bi da natural lalen da aka kwabashi hade da turarensa tun safe don yai saurin kamawa, a takaice ranar take amaryar zan-zan, ta zama taba ka lashe. Bayan ta ba Abdul abinci yaci ya koshi, sunyi sallah tare tunda baban nasa bai iso balle suje masallaci, hakan take yi duk ranar da yaron bai samu zuwa masallacin ba sai tasa ya rinka binta suyi sallar tare yana gani da koyon yadda ake gabatarwa. Suna idarwa tayi mishi wanka ta saka masa 'yar pyjamas sa ta yara sannan ta shiga tayi wanka ta fito ta kimtsa kanta, moderate kwalliya tayi da wata atampar Holland da aka dinka mata simple gown wanda tayi mata das tayi kyau da kirar jikin nan nata, tayi cas! Ba a batun kamshi a tattare da ita don ita ma'abuciyarsa ce, ya riga ya kama jikinta radam. 'Yar muryar Abdul dake wasa a falo taji yana fadin "Abba oyo-yo." Ta fito daga bedroom dauke da murmushinsa "Barka da isowa." Ta fadi cikin ladabi. Ya mika mata hannun damarsa "Assalamu Alaiki wa rahmatullah wa Barakatuhu." Cikin jin kunya ta mika masa nata hannun kana ta amsa sallamarsa, ya dan matse hannun kadan kana yace "Malamai sun mana koyi da yin hakan bayan yada sallama, yana kara shakuwa tsakanin ma'aurata. So ya gidan?" Ta maida masa sallamar sannan tace "GIda kowa da komi lafiya, ya aka barsu Khalifa?" "They are Okay alhamdulillah." Ya amsa yana wasa da Abdul dake ta zuba surutu.. Sun jima da gama cin abincin amma bai daina santin farfesun kaji da dambun kifin na, ta rinka tsokanarsa tana dariya. Tsaye ta iskoshi cikin bedroom dinsa bayan ta kimtsa falon, ta taka a hankali zuwa bayansa ta kwantar da kanta tace "Menene naji kayi shiru?" Ya juyo ya riko hannayenta yana kallonta, ya girgiza kansa "Kin canza min komi na rayuwata, me zance?" Ta saki ajiyar zuciya "Bana bukatar fitowar wata kalma daga bakinka muddin na faranta ranka, zuciyata cike take da farin ciki." Ya sake girgiza kai "Ba zaki gane bane Rahima, but a bar maganar for now come here... Da kalaman da yayi fada mata, but as long as tana kusa dashi yana kallon yadda tayi kyau ta tsaru tamkar wata 'yar tsana ba zai samu natsuwar wasu surutai ba, ya kama hannunta guda ya rinka kallon desing din lalen da yai ram a tafin hannunta, ya kai hannun bakinsa yai sakar mata kiss, ta lumshe idanunta, bata ankara ba taji ta bisa shimfidarsu, kamshin turaren seduction, da kamshin turaren Haseeb mai suna *Privacy* suka hade da wanda ta shafa *Eternity* suka cakude gaba daya, ya rungumeta tsan-tsan tamkar wani yace zai kwace mishi ita. Kamar a majigi suka rinka iyo cikin kogin so da kaunar juna, sai rada mata yake *Uhibbiki Kaseeran* cikin kunnenta, ta bude idonta da kyar " Me hakan ke nufi? Cikin shauki ya fassara *It means I love you so very much* Rahima, so da kaunarki sun shige min cikin jinina kamar yadda kwayoyin cutar nan da basu da magani kan shiga cikin jinin mutum." "To ni kuma in ce me Ya Haseeb? Saboda yadda nike jinka na rasa yadda zan kwatanta soyayyarka cikin zuciyata sai godiyar Allah nike dare da rana domin kullum adduata ya bani mijn da zan so ya so ni da zuciya daya ashe kaine amsar addu'ar. Nan kishi ya motsa yace "kina nufin baki taba son wani ba harda marigayi?" Ta danyi shiru tukunna kafin ta amsa "Na so Rabiu, irin son 'yanuwa ko kuma ince irin miji da matan da suka tsinci kansu a wannan matsayi kaddara Allah ta gitta amma ban taba jin irin wannan tafasar kunar zuciyar ba sai haduwata da Kai." Ya kara rungumeta "Iam sorry dana bude miki old wound, na kasa daurewa ne.". "Na fahimceki Yaya and iam glad da kayi tambayar coz a karo na farko bayan rasuwarsa nayi maganarsa ba tare da zubda hawaye ba sai deep sad feelings, ko ba komi Uban dana ne, shi ya fara nuna min so da kauna har in mutu ba zan manta dashi ba." Ya nisa "Yes hakane, karki manta nima danuwana ne da muka shaku kwarai, akwai wata irin kauna tsakaninmu da Allah ya dasa Mana, I really missed him, kuma wallahi ban taba tunanin zan auri matar da ya aura ba, but da Allah ya shiryo mana hakan kullum adduata garesa yasa ya huta, Allah ya sanyaya masa, Ina rokon Allah yasa zaki haifa min wani Rabiun bada jimawa ba." Tace "Idan ma ba a samu ba ga Abdul Nan.". "No Abdul -Haseeb dana ne da yaci sunana, yanzun Rabi'u nike so yaci sunan babansa.". Tace "To Allah ya amince ya tabbatar mana da khairan." Saida gari ya waye Rahima tayi maganar kifaye yace "Ya dace ki fahimci dalilin da yasa na baki kyautar kifayen nan Rahima." Tace "Hhmmm ni ban fahimci komi ba Kai dai za kayi min bayani Dakta." "To naji, ya jikin kifi nan tarwada yake?" Cikin rashin fahimtar inda tambayar ta dosa ta amsa "Tarwada ita kullum jikinta tsantsi da damshi ne ko tana cikin ruwa ko akasin hakan." Yace "Yauwa, ya jawota ya zaunar da ita bisa cinyarsa kafin yaci gaba da bayin "To Kinga kamar yadda halittar jikin kifi tarwada take haka Allah ya halicce ki kema exactly, kullum cikin ni'ima, duk namijin da Allah ya nufa da auren irinku to shi fa baida sauran burin wata 'ya mace a duniya, kune irin matan da ake Kira "Sa'ida', ba ruwanku da shaye-shayen magunguna da wasu matan keyi, ko kinsha ko baki sha komi ba mijinki zai matukar gamsu... Kinji reason dina na bada wannan kyauta, kuma daga yau duk gift din da zan baki wajibi ya danganci ruwa.. don nima kina ni'imtani, kin fahimceni, yanzun sai

Table of Contents

Chapters

66 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66